Da Dumi Dumi

Buhari ya bai wa ’yan Arewa kunya a mulkinsa – Ango Abdullahi

Farfesa Ango Abdullahi

Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Farfesa Ango Abdullahi, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza kuma ya kunyata ’yan Arewa a idon ’yan Najeriya. Ya bayyana haka ne lokacin hirarsa da manema labarai a Gombe jim kadan bayan kammala kaddamar da shugabannin Gamayyar Kungiyoyin Arewa (Coalition of Northern Group. Kuma ya ce tsarin karba- karba ba dimokuradiyya ba ne:

 

Me za ka ce kan tsarin karba-karba a siyasar Najeriya ganin mulki zai koma Kudu a shekarar 2023?

Babu inda aka rubuta cewa za a rika yin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa a tsarin mulkin Najeriya, ’yan siyasa ne kawai suka taru suka tsara hakan don biyan wata bukatar kansu. Da ana yin mulki saboda ci gaban kasa ne da jama’a hakan ba zai faru ba, amma da yake don son kai ake neman mulkin za ka iya ganin mutum ya kashe Naira biliyan daya yana neman shugabanci ya kuma san a shekara hudu albashinsa na halal bai wuce Naira miliyan 20 ba. Ashe  kuwa ka ga kasuwar shinku ake shiga.

Ba ka ganin dattaku ne tun da Arewa ta yi a bai wa Kudu ta yi?

ADVERTISEMENT

Karba-karba ba dimokuradiyya in da adalci lokacin da aka yi na farko da an tafi da haka da abin zai yi kyau. Amma a baya aka ce a gwada aka fara da zabar Shugaba Olusegun Obasanjo, Arewa ta zabe shi Kudu suka zabi Olu Falae, ya yi shekara hudu na farko ya gama ya sake cewa a sake zabarsa aka sake ya yi shekara takwas amma sai muka lura babu gaskiya a lamarin sai cin amana ta fuskoki da yawa har ya sake neman tazarce muka ga rainin ya yi yawa, muka yake shi aka kawo Umaru Musa ’Yar’aduwa, ya yi shekara uku ya rasu. Sai wadansu ’yan Arewa saboda son zuciya suka ce tunda Goodluck Jonathan shi ne Mataimakinsa a bar shi ya karasa bayan a tsari na farko duk wanda ya biyo bayan Obasanjo kamata ya yi sai shi ma ya yi takwas. Amma ni ban ga laifin ’yan Kudu ba, ’yan Arewan su ne ke da laifi a hakan ma wadansu munafukai a tsakanin gwamnonin Arewa suka sake cewa Jonathan ya sake tsayawa takara a zaben 2015. Mu kuma muka ga rashin dacewa muka yake shi har aka kada shi a zabe muka zabi Shugaba Buhari shi kuma ya ba mu kunya. Kuma mu ’yan Arewar ne muka jawo wa kanmu duk wata matsala da ta same mu har muka dawo ’yan amshin shata.

Yaya za ka bayyana mulkin Buhari a shekara 5 da ya yi?

Mu muka kori Jonathan muka kawo dan Arewa ya yi takara a APC saboda PDP ta bai wa Jonathan takara. Ganin cewa Buhari dan Arewa ne sai muka yi masa aiki ya ci zabe, bayan an zabe shi sai muka sa ran zai rage wa ’yan Arewa da jihohin Arewa kuncin rayuwa, sai ga shi kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba har yanzu. Mun zabo dan Arewa da nufin a bai wa kowanne bangare kula ba tare da an kwari wani bangare ba, sai ya kasance yanzu dan Arewar aka kwara.

Ganin kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba a wannan gwamnati yaya kake ganin sake zabar dan Arewa a 2023?

Muna fatar samun dan Arewa na kirki a 2023, muna da kuma wanda za mu kawo a zabe shi sai dai idan muka kawo shi Naira ta sa a ki zabarsa a sake zabar wani kuma.

Farfesa tunda karba-karba ba dimokuradiyya ba ce Arewa za ta iya ci gaba da neman mulki ke nan har 2023?

Kwarai kuwa muna da kuri’ar da idan dan Arewa ya fito takara za mu iya zabarsa ya ci zabe kuma tunda ba a mutunta tsarin tun farko ba, Arewa za ta yi ta nema kuma za mu iya.

Idan aka ce ka bai wa Buhari maki nawa za ka ba shi tunda ka ce ya gaza?

Na riga na ba shi maki na rashin tabuka komai shi ya sa a zaben da ya gabata ma na ce kada a sake zabarsa, kuma ina nan kan bakata har yanzu cewa Buhari ya gaza kuma dan Arewa bai shaida komai a mulkinsa ba.

Mece ce mafita ga matsalolin da Najeriya ta samu kanta a ciki?

Mafita ita ce shugabanni su gaya wa kansu gaskiya, domin idan aka ga matsala ba a magance ta ba, kullum kara girma take yi. Kuma kamata ya yi ’yan Arewa su tashi su duba matsalar ilimi da tsaron kasa da duk abin da ya dace ba kawai a tsaya a kan bambance-bambancen siyasa ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya