Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Buhari ya bukaci Majalisa da tabbatar da Tanko a matsayin Alkalin Alkalai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da Mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin mai mukamin Alkalin Alkalan Najeriya (CJN).

Shugaba Buhari, ya bayyana hakan a wasikar da ya aikewa shugaban majalisar dattawan Ahmad Lawan, inda shugaban ya karanta takardar a zauren majalisar yau Alhamis, kuma bukatar hakan ta biyo bayan amincewar Majalisar Kula da Alkalai ta kasa (NJC) da tabbatar wa Ibrahim Tanko Muhammad mukamin Alkalin Alkalan Najeriya (CJN).

ADVERTISEMENT

Ibrahim Tanko na rike da mukamin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya tun ranar 25 ga Janairun 2019. Bayan dakatar da tsohon Alkalin Akalan Najeriya CJN Walter Onnoghen.

ADVERTISEMENT