✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya canja sunan filin wasa na Abuja zuwa M.K.O. Abiola

A shekaranjiya Laraba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya canja sunan filin wasa na Abuja da ake kira National Stadium, zuwa M.K.O. Abiola. Shugaban ya ce…

A shekaranjiya Laraba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya canja sunan filin wasa na Abuja da ake kira National Stadium, zuwa M.K.O. Abiola.

Shugaban ya ce daga yanzu za a rika kiran filin wasan ne da M.K.O. Abiola Stadium  maimakon National Stadium, Abuja.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake karanta jawabinsa a ranar bikin dimokuradiyya (Democracy Day) wacce ta koma ranar 12 ga watan Yuni maimakon 29 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya ce, ya yi haka ne don karrama marigayi Abiola saboda zaluntarsa da aka yi wajen murde zaben shugaban kasa da ake ganin shi ya yi nasara a ranar 12 ga watan Yunin, 1993 kimanin shekaru 26 da suka wuce.  Kuma marigayi Abiola ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin wasanni a kasar nan.

A lokacin da yake raye Abiola ne ya mallaki kulob din Abiola Babes da ya fafata a gasar rukuni-rukuni na Najeriya.

Idan za a tuna a ranar Litinin da ta wuce ne Shugaba Buhari ya sanya hannu a dokar da ta amince a mayar da ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar dimokuradiyya a kasar nan maimakon 29 ga watan Mayu.