✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakala: An dakatar da shugabannin NSITF nan take

Ma’aikatar Kwadago ta ce Shugaba Buhari ya amince da dakatar da Manajan Darektan Asusun Inshorar Kyautata Rayuwa (NSITF), Adebayo Somefun da Manyan Darektocin hukumar nan…

Ma’aikatar Kwadago ta ce Shugaba Buhari ya amince da dakatar da Manajan Darektan Asusun Inshorar Kyautata Rayuwa (NSITF), Adebayo Somefun da Manyan Darektocin hukumar nan take.

Adebayo da Manyan Darektocin da kuma Manyan Manajojin Gudanarwa da Mataimakansu sun tafi hutun dole nan take kuma sai abin da hali ya yi.

Kakakin Ma’aikatar, Charles Akpan, cikin wata sanarwa ya ce, “Dakatarwar ta biyo bayan hujjojin da ke nuna shugabannin NSITF sun karya dokokin kashe kudaden gwamnati baya ga aikata wasu laifuka”.

Wadanda aka dakatar din za su gurfana a gaban kwamitin hadin gwiwa mai bincikar karya dokar kashe kudaden da sauran laifuka a hukumar daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Sanarwar ta umarci dukkanin wadanda aka dakatar da su mika kayan gwamnatin da ke hannunsu ga sauran jami’ai mafiya girman matsayi a sassan da suka bari.

Ta kara da cewa Minista Chris Ngige ya nada jami’an da za su rike mukaman wadanda aka dakatar din daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli, yayin da Shugaban Kwamitin Amintattu, Austin Enajemo Isire zai ja ragamar hukumar.

Manyan Darektocin da aka dakatar sun hada da Jasper Ikedi Azuatalam, Babban Darektan Kudu da Zuba Jari da Misis Olukemi Nelson, Babbar Darektar Ayyuka da kuma Alhaji Tijani Darazo Sulaiman, wanda shi ne Babban Darektan Gudanarwa.

Manyan Manajojin sun hada da Janar Manajan Gudanarwa, Olusegun Olumide Bashorun da kuma Janar Manajan Kudi, Lawan Tahir da kuma Mista Chris Esedebe wanda shi ne Janar Manaja na Hakkoki da Biyan Diyya.

Sauran su ne Mataimakan Manajin Darektan da suka hada da Olodotun Adegbite da Emmanuel Enyinnaya Sike da Misis Olutoyin O. Arokoyo da Mis Dorathy Zajeme Tukura da kuma Misis Victoria Ayantuga.