Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Buhari ya fi kashi 80 na ‘yan Najeriya lafiya- Ministan Kwadado

Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fi kashi 80 na ‘yan Najeriya lafiya, don haka shekaru ba matsala ba ce.

ADVERTISEMENT

Ngige ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Awka, Jihar Anambara, “ni likita ne don haka ina tabbatar muku cewa ya fi mutane da yawa da muke tunanin suna da lafiya. Ya fi kashi 80 na ‘yan Najeriya lafiya.

“Yana zama a taron Majalisar Zartawa na awa 8. Duk da cewa wasu daga cikinmu suna fita su dan sha iska, shi Shugaba Buhari ba ya fita.”  

ADVERTISEMENT