✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gana da tsohon Shugaban Zauren MDD

Wani ikon Allah kuma sai kai da Amina kuka yi aiki tare.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon Shugaban Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA), Farfesa Tijjani Muhammad Bande a Fadar Aso Rock da ke Abuja.

Buhari ya bayyana godiyar Najeriya ga Farfesa Muhammad-Bande bisa yadda ya zama abin alfahari gare ta a matsayinsa na wakilinta a UNGA.

“Ka samu damar hidimtawa inda ka yi abin a yaba maka kuma mun gode sosai.

“Wani ikon Allah kuma sai kai da Amina kuka yi aiki tare.

“A lokacin da na yi jawabi a UNGA na yi matukar alfahari da kasancewar kai da ita a tare da ni”, inji sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar.

Buhari ya yi amfani da damar wajen kira ga jama’ar Najeriya da su kara hakuri da nuna fahimta ga yunkurin kawo cigaban kasa, abin da ya ce kan dauki lokaci.

Shugaban ya bayyana kwarin gwiwa cewa cigaban da ake samu a bangaren ilimi da kwarewa da kere-kere zai taimaka wajen kawo ci gaban kasar da wuri.

A nasa bangaren, Farfesa Muhammad-Bande ya nuna godiya ga shugaban da daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi a matsayin Shugaban UNGA na 74.

Ya yi godiya ga Buhari musamman game da ba shi mukami a gwamnatinsa da kuma mara masa baya a UNGA.

“Ka ba ni aiki tare da ba ni duk abin da nake bukata domin in yi nasara.

“Yarda da ni da ka yi da kuma jagorancin da ka bayar sun taimaka wajen samun nasarar”, inji shi.

A halin yanzu Farfesa Muhammad-Bande zai ci gaba da aiki a matsayin wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.