✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gana da ‘yan Majalisar Wakilai 70 na APC da suka fadi zaben fid da gwani

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan Majalisar Wakilai sama da 70 da suka fadi zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC a Fadar…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan Majalisar Wakilai sama da 70 da suka fadi zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ta ruwaito cewa an gudanar da taron ne a sirri, kuma ganawar ta dauki kusan awa daya da rabi.
Musa Soba mai wakiltar mazabar Soba na Jihar Kaduna ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan ganawar cewa shugaban kasa ne ya kira su domin sauraron kokensu a kan yadda aka gudanar da zaben na fid da gwani, inda ya ce ‘yan Majalisar Wakilai da suka fadi zaben sun fi 70.
Soba ya kara da cewa sun bukaci shugaban kasa da ya sanya baki a abin da suka ce rashin adalci da wasu gwamnoni suka musu da kuma shugaban jam’iyya.
A nasa bangaren, dan majalisa Hussaini Kangiwa wanda shi ma Kamfanin Dillancin Labarai ta ruwaito bayan taron, ya yi gargadin cewa Jam’iyyar APC tana iya rasa Jihar Kebbi idan shugaban kasa bai sa hannu a lamarin ba.