✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba da umarnin hana fita a Abuja da Legas

Gwamnatin Najeriya ta ce daga karfe 11.00 na daren ranar Litinin ba wanda za a bari ya kara fita, in ba dole ba, a Abuja…

Gwamnatin Najeriya ta ce daga karfe 11.00 na daren ranar Litinin ba wanda za a bari ya kara fita, in ba dole ba, a Abuja da Legas sai bayan mako biyu, a wani mataki na hana cutar Coronavirus yaduwa.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ga ‘yan Najeriya da maraicen ranar Lahadi.

“Bisa shawarar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC), ina ba da umarnin dakatar da duk wani kai-kawo a Legas da Abuja har tsawon mako biyu a matakin farko, kama daga karfe 11 na daren Litinin 30 ga watan Maris.

“Wannan umarni zai kuma hada da Jihar Ogun saboda kusancinta da Legas da kuma yawan zirga-zirgar da ake yi a tsakaninsu”, inji Shugaba Buhari, wanda ya kara da cewa, “Dukkan mazauna wadannan yankuna za su zauna a gida; a kuma dakatar da duk wasu tafiye-tafiye daga wasu jihohi, sannan a rufe dukkan ofis-ofis da wuraren harkokin kasuwanci a yankunan”.

Dalilin daukar matakin

Shugaban kasar ya ce daukar wannan mataki ya zama dole ne saboda galibin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus a Legas da Abuja suke, sannan wadanda aka samu a wasu wurare kuma sun kamu ne saboda sun yi mu’amala da wadanda ke yankunan biyu.

“Za mu yi amfani da wannan lokacin domin gano, da bibiya, da kuma killace wadanda suka yi mu’amala da mutanen da aka tabbatar sun kamu, za kuma mu tabbatar an yi jinyar wadanda suka kamu yayin da muke takaita bazuwar cutar zuwa sauran jihohi”, inji Shugaba Buhari.

A makon jiya dai Ministan Yada Labarai da Al’adu Lai mohammed ya ce gwamnati na bibiyar mutane sama da 4,000 wadanda ake tunanin sun yi mu’amala da majinyatan da aka tabbatar sun kamu.

Wadanda matakin bai shafa ba

Wannan mataki dai, a cewar Shugaba Buhari, bai shafi asibitoci, da cibiyoyin kiwon lafiya, da hukumomi da kamfanonin da ayyukansu suka shafi kiwon lafiya ba.

“Baya ga haka, harkokin kasuwanci da suka jibanci sarrafa abinci  da rarraba shi da kuma sayar da shi; da samar da man fetur da sayar da shi; da samar da wutar lantarki da rarraba ta; da kuma kamfanonin tsaro masu zaman kansu, duk an wannan doka ba ta shafe su ba.

“Amma duk da haka su ma za a sa ido a kuma takaita shiga da fitar su”, inji Shugaban Kasar.

Su kuwa ma’aikatan kamfanonin sadarwa, da na gidajen rediyo da talabijin da jaridu, za  a kyale su rika fita ne kawai idan suka tabbatar da cewa ba za su iya aiki daga gida ba, a cewar Shugaba Buhari.

Tallafi ga marasa galihu

Shugaban kasar ya ce sai dai gwamnati za ta duba yiwuwar samar da tallafi ga wadanda wannan lamari zai jefa cikin halin ni-‘yasu.

“Ga mazauna garuruwa da al’ummun da ke kewaye da  Legas da Abuja wadanda tabbas wannan lamari zai shafi rayuwarsu, za mu samar da kayan agaji don saukaka maus radadi a makwanni masu zuwa”.

Su kuwa marasa galihu da ke karbar tallafin kudi duk wata a yankunan, Shugaban kasar ya ce ya bayar da umarni a biya su tallafin na wata biyu ba atre da bata lokaci ba.

Shugaban kasar ya kuma ce babu shakka wannan mataki zai takura wa jama’a, amma idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa a kasashen Italiya da Faransa, da Spaniya, to ba yadda aka iya.

“Sai dai”, a cewar Shugaba Buhari, “lallai ne mu kalli hana wannan cuta yaduwa a matsayin wani wajibci ta fuskar kishin kasa. don haka neke bukatar dukkanmu da wannan lamari ya shafe mu mu ajiye biyan bukatar kauwnanm a gefe don kare kanmu da ma ‘yan uwanmu.

“Za a iya ganin karshen wannan abokin gaba namu ne kawai ta hanyar hada karfi da karfe da kuma yin biyayya ga shawarar masana kimiyya da masana harkar kiwon lafiya”.

Kungiyoyi da kwararru daban-daban dai sun dade suna kira ga hukumomi su ayyana irin wannan dokar ta-baci a fadin Najeriya.

sai dai kuma ko da yake umarnin gwamnatin tarayya a Legas da Abuja da Ogun kawai ya tsaya, gwamnatocin jihohi ma na ta ba da umarnin rufe harkoki a yankunansu.