Daily Trust Aminiya - Najeriya: Buhari ya kaddamar da tambarin cika shekara 60
Subscribe

Najeriya: Buhari ya kaddamar da tambarin cika shekara 60

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da tambarin da za a yi amfani da shi yayin bikin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ’yanci.

Shugaban kasar ya kaddamar da tambarin ne ranar Laraba lokacin da ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa a babban dakin taro na fadar Aso Villa a birnin Abuja.

A ranar 1 ga watan Oktoba na kowacce shekara, Najeriya tana gudanar da shagulgulan murnar zagayowar ranar samun mulkin kai daga Turawan Ingila a shekarar 1960.

Tun a farkon watan Satumba ne Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Sadarwa, Dokta Isa Ali Pantami, ta bukaci ’yan Najeriya da su kawo tsare-tsaren da za a yi amfani da su a yayin bikin.

Ministan, wanda shi ne shugaban karamin kwamitin tsare-tsaren bikin, ya ce Shugaba Buhari ya sahale a yi bikin ta hanyar kiyaye ka’idojin kariya daga coronavirus.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito ministan yana cewa ’yan Najeriya ne za su samar da maudu’i da kuma tsarin gudanar da bikin wanda aka yi wa lakabi da ‘Tarayya a Shekara 60’.

“Rana ce da ke tunatar da kowane dan kasa game da kasar da muke kira tamu – mai kabilu daban-daban tare da mutane masu juriya.”

texem
More Stories