✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya ga mutanen Faskari da Sabuwa

Tsohon Shugaban kasa kuma jagoran Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya da jaje ga al’umomin kananan hukumomin Faskari da Sabuwa wadanda harin…

Tsohon Shugaban kasa kuma jagoran Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya da jaje ga al’umomin kananan hukumomin Faskari da Sabuwa wadanda harin 11 ga Maris ya rutsa da su.
Janar Buhari ya ce wannan al’amari da ke faruwa a wasu sassan kasar nan wata alama ce ta neman kawo rudani a Nijeriya wanda ko kadan hakan ba daidai ba ne.
Ya ce mafi yawan hare-haren ba su da nasaba da addini ko kabilanci domin duk lokacin da aka kai irinsa sai a tarar ya shafi kowace kabila ko addini.
Sai ya bukaci al’umma da su kara sanya ido a duk lokacin da suka ga wata bakuwar fuska a yankunansu, tare da sanar da hukumomin tsaro cikin gaggawa domin a dauki matakin da ya kamata ba tare da bata lokaci ba.
Janar Buhari ya yi addu’a ga mutanen da suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka sanadin harin, inda ya yi addu’ar Allah Ya mayar da mafi alheri ga wadanda suka yi asarar muhallinsu.
Yayin ziyarar Janar Buhari ya ziyarci Marabar Kindo da Maigora da Sabon Layin Galadima da ke kananan hukumomin Faskari da Sabuwa, inda ya ba su tallafin buhunan masara 200 da Naira miliyan daya, inda daga karshe yayi fatan samun dauwamammen zaman lafiya a wannan kasa.