✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kai wa majalisa kasafin 2020 da aka yiwa gyara

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da kasafin kudin 2020 da aka yiwa kwaskwarima ga Majalisar Dokoki ta Kasa don neman amincewarta. Mai taimaka wa shugaban…

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da kasafin kudin 2020 da aka yiwa kwaskwarima ga Majalisar Dokoki ta Kasa don neman amincewarta.

Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a kan harkokin Majalisar Dattawa Sanata Babajide Omoworare ne ya mika kundin ga Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan.

An dai yi kwaskwarima ga kasafin kudin ne bayan da farashin mai ya fadi a kasuwannin duniya sakamakon barkewar annobar coronavirus.

Wata majiya da ba ta so a fadi sunanta a Majalisar Dattawan ta ce Sanata Ahmad Lawan ya umarci Kwamitin Kudi a karkashin jagorancin Sanata Barau I. Jibrin ya fara aiki a kan kundin nan take.

An kuma ruwaito cewa kwamitocin majalisar masu ruwa da tsaki a lamarin za su fara tuntubar ministocin da abin ya shafa ranar Alhamis a kan kundin.