✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kori shugaban hukumar inshorar lafiya NHIS

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori babban sakataren hukumar Inshorar lafiya ta Kasar NHIS Farfesa Usman Yusuf. An nada Farfesa Mohammed Nasir Sambo a matsayin…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori babban sakataren hukumar Inshorar lafiya ta Kasar NHIS Farfesa Usman Yusuf.

An nada Farfesa Mohammed Nasir Sambo a matsayin sabon shugaban Hukumar NHIS a wata sanarwa da Ma’aikatar lafiya ta fitar, inda takardar ke nuna amincewar Shugaba Buhari game korar Farfesa Usman Yusuf, wanda aka tura hutun dole a watan Oktoban bara, bayan majalisar gudanarwar hukumar ta dakatar da shi.

Kamar yadda Daraktar yada labarai a ma’aikatar lafiyar Najeriya, Boade Akinola, ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce korarsa ta zo ne bayan shawarar da kwamitin binciken da aka kafa don gano sanadin rikicin da ya dabaibaye Hukumar NHIS, ya bayar.