✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nemi a gudanar da zaben 2015 rana daya

Tsohon Shugaban kasa kuma jagoran Jam’iyyar APC Janar Muhammau Buhari ya shawarci Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da zabubbukan shekarar 2015 a rana…

Tsohon Shugaban kasa kuma jagoran Jam’iyyar APC Janar Muhammau Buhari ya shawarci Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da zabubbukan shekarar 2015 a rana daya domin magance magudin zabe a ake yi a kasar nan.
Janar Buhari ya bayyana haka ne a Daura ranar Asabar da ta gabata yayin a ya karbi katin zama dan jJam’iyyar APC a mazabarsa Babban-Gida, inda ya ce yin zabubbukan a rana daya zai hana magudin zabe a sace-sacen akwatunan zabe da tsoratar da masu jefa kuri’a.
Ya ce abubuwan da suka faru a lokutan zabubbukan shekara ta 2003 da 2007 da kuma 2011, abubuwa ne marasa dadi a sha’ani irin na dimokuradiyya, wanda muddin ana so a magance sake faruwarsu, to ay i zabubbuka a rana daya a zaben badi.
Janar Buhari ya ce akwai kwarin gwiwar jam’iyyarsu ta APC ce za ta lashe zabe mai zuwa muddin aka shirya zabe na gaskiya da tsoron Allah.
Shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar APC a Jihar Katsina Alhaji Ahmad Musa dangiwa ya ce duk da cewa an fara ba da katin zama dan jam’iyyar a makare, amma an yi kyakkyawan tsari da ya gamsar da ’ya’yan jam’iyyar musamman ganin yadda jama’a suka fito sosai suka yi rajistar.