✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya rattaba hannu a kasafin kudin 2019

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a dokar kasafin kudin 2019 na Naira Tiriliyan 8.92 a matsayin doka. Shugaban ya mika kasafin kudin 2019 na…

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a dokar kasafin kudin 2019 na Naira Tiriliyan 8.92 a matsayin doka.

Shugaban ya mika kasafin kudin 2019 na Naira Tiriliyan 8.83 ga majalisar dattawa, amma majalisar ta kara da kudin zuwa Naira biliyan 10 wanda adadin kasafin kudin yanzu ya kai Naira Tiriliyan 8.92.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya bayyanawa cewa, shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun tabbatar da rattaba hannun da Shugaban Najeriya ya yi a yau.