✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai aike wa Majalisa sabuwar dokar man fetur

Ya riga ya rattaba hannu a dokar da aka shekara 20 ana kai-komo a kai

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan sabuwar Dokar Man Fetur da aka dade ana jira.

Nan da mako mai zawu Shugaban zai aike wa Majalisar Dattawa dokar, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na Reuter ta ruwaito wasu majiyoyi a fadar gwamnati da ba su so a ambaci sunayensu ba.

“Buhari ya riga ya sanya wa dokar hannu a makon jiya kuma ma’aikatansa sun yi nisa wajen neman goyon baya Majalisar Tarayya”, inji rahoton na Reuters.

Rahoton ya ce Majalisun Tarayya sun riga sun nada mutanen da ke aiki a kan sassan dokar wadda dole sai ta samu amincewar Majalisar.

Reuters ta bukaci jin ta bakin masu magana da yawun Shugaban Kasa, amma sun ki cewa komai, yayin da bangaren Majalisa ke cewa sai nan gaba zai yi magana.

An shekara 20 ana aikin gyaran fuska ga dokar da ta shafi bangaren man fetur da iskar gas wadda ke aiki tun a shekarun 1960.

Takaddama kan karbar harajin mai da kuma sharudda da tsarin rabon kudaden shiga a na daga cikin abubuwan da suka yi kawo jawo kwan-gaba-kwan-baya wajen amincewa da dokar.

Bukatar sabunta dokar da yi mata gyaran fuska sun taso ne haikan a shekarar nan sakamakon faduwar farashin danyen mai da kuma karkata zuwa ga amfani da makamashin da ba na mai ba.

Hakan ya kara tsananta gasa a bangaren zuba jari tsakanin manyan kamfanonin mai ta kara kamari.

Ana ganin fahimtar juna tsakanin Majalisun Tarayya da bangaren zartarwa ta taka muhimmiyar rawar da za ta kai ga aiwatar da sabuwar dokar a wannan shekara.