✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sallami mukarraban Osinbajo 35

…Babu rikici tsakanin Buhari da Osinbajo   Dambarwar da ke faruwa a Fadar Shugaban Kasa ta dauki sabon salo, a shekaranjiya Labara inda Shugaban Kasa…

…Babu rikici tsakanin Buhari da Osinbajo

 

Dambarwar da ke faruwa a Fadar Shugaban Kasa ta dauki sabon salo, a shekaranjiya Labara inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami mukarraban Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo 35.

Wannan yana zuwa ne bayan da a farkon wannan mako Shugaban Kasar da ke ziyarar kashin kai a Ingila ya sanya hannu a kan dokar hako mai a can, lamarin da masu fashin baki suke ganin akwai tsama a tsakaninsa da Mataimakinsa.

Sai dai duk da bayyanar wannan matsala Fadar Shugaban Kasa ta wufantar da maganar inda ta ce babu rikici a tsakanin Shugaba Buhari da Mataimakinsa.

Wasu majiyoyi da Aminiya ta zanta da su sun tabbatar da sallamar mukarraban na Osinbajo, wadanda wadansu ke ganin ana yin haka ne domin rage karfinsa kamar yadda aka taba yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Wata majiya a Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar wa Aminiya cewa tuni aka ba wadanda abin ya shafa takardar sallama daga aiki.

Amma Mataimakin Shugaban Kasar da ya ga haka, sai ya amshe takardun sallamar daga mukarrabsan nasa, ya nuna rashin jin dadinsa kan sallamar, inda ya bukaci su ci gaba da aiki har sai Shugaban Kasa ya dawo daga Landan.

Wata majiya ta fada wa Aminiya cewa, “Mataimakin Shugaba Kasa bai ji dadin abin ba. Shi ya sa ya amsee takardun sallamar , inda ya bukaci su jira Shugaba Buhari ya dawo.”

Wata majiya ta ce, “Na yi magana da daya daga cikin wadanda aka sallama, kuma ya tabbatar da cewa an kawo masa takardar sallama daga aiki.”

Shi dai Shugaba Buhari yana birnin Landan ne, inda ake sa ran zai dawo ranar 17 ga Nuwamba.

Babu sabani tsakani Shugaba Buhari da Osinbajo – Fadar Shugaban Kasa

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkokin Majalisar Dattawa Sanata Babajide Omoworare da takwaransa na Majalisar Wakilai Umar El-Yakub sun ce babu wata matsala a tsakanin mutanen biyu.

Omoworare ya ce batun wai Shugaba Buhari ya sanya hannu a wata doka daga Landan wannan ba wani abu ba ne, inda ya ce dokar kasa ta ba shi damar yin haka.

Ka ajiye aiki kawai- Afenifere

Da suke mayar da martani, Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta shawarci Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ajiye aiki.

Kakakin kungiyar, Yinka Odumakin ne ya sanar da haka inda ya ce an mayar da Osinbajo sanaiyar ware kuma an kunyata shi, sannan ya ce babban abin da zai yi ya tsira da mutuncinsa kawai shi ne ya ajiye mukamin.

“Ban san me yake yi a wannan mulki ba? An riga an mayar da shi saniyar ware.”

Dangantaka na kara tsami a Fadar Shugaban Kasa – PDP

Ita kuma Jam’iyyar PDP cewa ta yi akwai alamar cewa dangantaka  na kara tsami a tsakanin Shugaban Kasa da Mataimakinsa bayan cire mukarrabansa 35.

Kakakin Jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ne ya fada haka lokacin da wakilinmu ya tuntube shi.

“Mun ba su shawara su dinke barakar da ke tsakaninsu idan har don mutane suke aiki, amma sun kasa. Me kake tunanin wannan gwamnatin za ta yi bayan ta kasa kinsta gidanta? Mutanen Najeriya sun riga sun cire tsammani,” inji shi.

Abubuwa da ke nuna akwai matsala tsakanin Buhari da Osinbajo

1. Ranar 16 ga Sabumban bana, Shugaba Buhari ya musanya Kwamitin Tattalin Arziki da ke karkashin Osinbajo

2. A ranar 17 ga Satumba  Buhari ya bukaci Osinbajo ya nemi izini kafin ya dauki mataki kan duk wata ma’aikata da ke karkashinsa.

3. A 1 ga Oktoba, Buhari ya mayar da shirin tallafi na N-Power da ciyar ’yan makaranta zuwa Ma’aikatar Jinkai.

4. A ranar 5 ga Nuwamba, Buhari ya zabi sababbin mashawarta kan tattalin arzikin kasa

5. A ranar 6 ga watan Nuwamba, Buhari ya sallami mataimakan Osinbajo guda 35.