Search
Subscribe
Buhari ya sha alwashin hukunta masu hannu a rikicin Kaduna

Buhari ya sha alwashin hukunta masu hannu a rikicin Kaduna

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin hukunta duk wanda aka kama da hannu a rikicin Jihar Kaduna. Yana mai cewa cikin wadanda za a hukunta har da masu ingiza matasa ko daukar nauyin rikice-rikicen a jihar da ma sauran jihohin kasar nan baki daya.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da sarakuna da malaman addini a jihar, a yayin ziyarar jajantawa da ya kawo jahar ta Kaduna.

A cewar shugaban bai kamata Jihar Kaduna da aka sani a matsayin cibiyar Arewa kuma gida ga Firimiyan Arewa ta zama jihar rikici ba. Ya ce idan a shekarun baya masu aikata irin wadannan laifuka suna ganin ba a kama su tare da hukunta su ba, to shi ba zai yarda da hakan ba a lokacinsa.

“Duk wanda jami’an tsaro suka  kama da hannu a wannan rikici ko masu daukar nauyin irin wadannan fitintinu dole a hukunta shi. Gwamnatin tarayya ba zata zura idanu mutane na tayar da fitina dan wani biyan bukatu nasu ba. Mun tura karin jami’an tsaro Jihar Kaduna domin tabbatar da an samu zaman lafiya mai dorewa,” Inji shi.

Buhari ya ce fitina bata taimakon kowa kuma ba zata taba kawo cigaba ba a kasa, face ci baya kawai. Sannan sai ya roki sarakuna da shugabannin addini da su cigaba da wayarwa jama’a kai akan mahimmancin zama lafiya da juna.

Shugaba Buhari ya kuma jajanta wa gwamnati da iyalan Agom Adara Maiwada Madaki da wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane suka halaka a makon jiya.

Shi ma a jawabinsa, Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El’rufai ya nuna cewa gwamnatin jihar ba za ta bari wasu matasa suna tare hanya suna kashe mutane ko matafiya babu gaira babu dalili ba, musamman a lokacin rikici. Ya ce wannan dabi’a ba ta dace ba kuma duk al’ummar wata unguwa da aka samu da irin wannan dabi’a gwamnati za ta dauki tsattsauran mataki a kanta da shugabaninta baki daya.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin