✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya umarci a shigar da masu yi wa kasa hidima shirin inshorar lafiya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Dake Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta tabbatar da shigar da dukkan matasa masu…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Dake Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta tabbatar da shigar da dukkan matasa masu hidimar cikin shirin inshorar lafiya na kasa.

Babban Daraktan hukumar, Birgediya Janar Shuaib Ibrahim ne ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin.

Ya kuma ce NYSC ta kara matsa kaimi wajen hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar matasan a duk inda suke a fadin Najeriya.

Shuaibu ya ce da karin matasa 300,000 da za su shiga cikin shirin a kwanan nan, ko tantama babu shirin na yi wa kasa hidima shine mafi muhimmanci wajen horar da matasa a matsayinsu na jagororin hadin kai da ci gaban kasa.

Ya ce, “Bugu da kari, shirin ya kammala tsare-tsare da hukumar NHIS domin shigar da matasa cikin shirin inshorar lafiya ta kasa kamar yadda shugaba Buhari ya umarta.

“Mun kuma kara kashe kudade da dama wajen kula da lafiyar matasan, ciki har da biyan kudaden magungunansu.

“Ina so in yi amfani da wannan damar wajen mika sakon godiya ga jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki saboda irin hadin gwiwar da suke ba mu,” inji shi.