✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yaba wa ’yan majalisa kan amincewa da kasafin kudin bana

Fadar Shugaban kasa ta yaba wa Majalisar Dokoki ta kasa kan amincewa da kasafin kudin bana a shelaranjiya Laraba. Mashawarcin Shugaban kasa na Musamman Kan…

Fadar Shugaban kasa ta yaba wa Majalisar Dokoki ta kasa kan amincewa da kasafin kudin bana a shelaranjiya Laraba. Mashawarcin Shugaban kasa na Musamman Kan Harkokin Majalisar Dattawa Sanata  Ita Enang, ya shaida wa manema labarai cewa dubawa da amincewa da  abin yabawa ne.
Ya yaba wa kwamitocin kula da kasafin kudi na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan aiki wurjanjan da suka yi domin tabbatar da amincewa da kasafin.
 “Na bibiyi daukacin hanyar da suka bi, kuma na lura da aiki tukuru da sanatocin suka nuna. Ina bayyana cewa mun yaba tare da godiya musamman kan amincewa da kasafin, shugabannin kwamitocin da wakilan kwamitocin da kwamitocin kasafin muna yawan tuntubar juna,” inji shi.
Sanata Enang ya kara yaba wa ’yan majalisar kan amincewa da tsarin kashe kudi na matsakaicin lokaci (MTEF) da takardar Dabarun Kashe Kudi (FSP), inda ya ce su ne sila ta amincewa da kasafin.
Sanata Enang ya kuma yaba wa kafafen watsa labaraikan yadda suka bi diddigin hanyar amincewa da kasafin.
A shekaranjiya Laraba ce  Majalisar Dattawa da takwararta ta wakilai suka amince da kasafin kudin bana, bayan da aka rika dage-dage da cece-ku ce a kansa.
Majalisun biyu bayan amincewa da kasafin sun kuma yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da kasafin kudin wanda shi ne kasafi mafi girma a tarihin Najeriya, ta hanyar da ta dace, musamman idan aka dubi halin da tattalin arzikin kasar nan ya shiga sakamakon faduwar farashin man fetur.
A yayin da yake jawabi Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya ce, “An karanta wannan kudiri sau uku ke nan ana kuma zartar da shi. Don haka yanzu ya rage ga bagaren zartarwa na gwamnati ya yi amfani da shi yadda ya dace.”
A watan Disamba bara ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin a gaban majalisar wanda ya kai Naira tiriliyan shida da biliyan 77 da kuma miliyan 680, kwatankwacin Dala biliyan 30. Sai dai daga baya Shugaba Buhari ya nemi a janye shi bayan wata daya da mika shi, domin ya yi masa wasu gyare-gyare, sakamakon faduwar farashin man fetur.
Sai dai kafin ya nemi janye kasafin an rika samun takaddama a tsakanin banagren majalisar da na zartarwa cewa an sace kasafin tare da sassauya alkaluman da ya kunsa.
Yawan kudin dai bai sauya ba, amma gibin kasafin ya karu da Naira tiriliyan uku daga Naira tirilyan 2 da biliyan 200.
Gidan rediyon BBC ya ce har yanzu babu tabbacin inda za a samo kudaden da za a yi amfani da su wajen cike gibin kasafin lura da yadda kudin da ake samu a baya a bangaren man fetur wanda da shi ne kasar nan take dogara da shi ya ragu, sakamakon faduwar farashinsa a kasuwar duniya.