✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai iya kawo karshen matsalar tsaro – IBB

Tsohon Shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana da yakinin shugaba Buhari zai iya kawo karshen rashin tsaro da ya addabi…

Tsohon Shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana da yakinin shugaba Buhari zai iya kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da ’yan jarida a gidansa da ke Minna.

Tsohon shugaban ya ce hakika yana da yakinin Shugaban Kasa Buhari zai iya magance kalubalen tsaro da ke damun kasar nan, don haka al’ummar kasar nan su kara hakuri.  Ya kara da cewar Buhari mutum ne mai yin Magana daya.  Babangida ya ce lamarin tsaro ya mayar da al’amurra baya  al’amura baya wannan zai kasance ne na dan wani lokaci, domin gwamnati za ta kawo karshen lamarinnan ba da dadewa ba.

Daga nan sai yay i kira ga al’umma su bai wa gwamnati mai cu cikakken hadin kai da goyon baya don ganin ta samu nasara.