✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kai Najeriya ya baro da cin bashi —PDP

PDP ta ce bashin biliya $2.1 da Buhari zai karbo daga Brazil zai kassara Najeriya

Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi alawadai da bashin Dala biliyan 1.2 da Shugaba Buhari ke shirin karbowa daga kasar Brazil.

PDP ta koka bisa irin halin da Najeriya za ta shiga idan aka ci gaba da karbo bashi, tana mai cewa Buhari zai kassara Najeriya da irin tarin bashin da yakewa karbowa.

Jam’iyyar ta sanar da haka ne cikin wani jawabi da ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Kola Ologbondiyan, inda tace “ya kamata majalisa ta taka wa Buhari burki wajen kara ciyo bashi, saboda zai jefa kasar nan cikin mawuyacin hali, ya kuma nakasa harkar noma da bunkasa tattalin arzikin abincinmu.

“Muna jan hankalin ’yan Najeriya da cewa in har aka karbo bashin Naira biliyan 459 daga Brazil, baya ga Naira Tiriliyan 5.20 da ke cikin kasafin 2021, bashin da aka ciyo wa kasar nan zai doshi Tiriliyan 36.2 kuma zai iya jefa tattalin arzikinmu cikin mummunan hali.

“PDP tana kiran majalisa da ta yi wa tsarin karbo bashi gyaran fuska domin kare kasar nan daga fadawa mawuyacin hali.

“Maimakon tulin bashin da gwamnati Buhari ke ciwowa, gara ta mayar da hankali wajen kirkiro hanyoyin samun kudade a cikin gida”, inji PDP.

Daga karshe jam’iyyar ta ja hankalin ’yan Najeriya da su farka su gane irin badakalar da ta ce ake yi musu da sunan ciyo bashi.