✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kai ziyara Birtaniya a yau

A yau Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Birtaniya, fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilin ziyarar ba. Mai magana da yawun shugaban…

A yau Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Birtaniya, fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilin ziyarar ba.

Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a yau, a jiya Laraba ne shugaba Buhari ya kai ziyara Legas don kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta yi.

Ana saran yau Shugaban zai kaddamar da wasu ayyuka a jihar Borno, wanda  Gwamnan jihar Kashim Shettima ya yi da suka hada da: bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma kaddamar da wasu sababbin hanyoyi.