✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai sa hannu a kan sabon kasafin kudin 2020

Shugaba Buhari zai rattaba hannu a kan sabon kasafin kudin 2020 da Majalisar Tarayya ta amince da shi a watan Yuni. Fadar Shugaban Kasa ta…

Shugaba Buhari zai rattaba hannu a kan sabon kasafin kudin 2020 da Majalisar Tarayya ta amince da shi a watan Yuni.

Fadar Shugaban Kasa ta shafinta na Twitter ta ce Shugaba Buhari zai rattaba hannun ne a ranar Juma’a 10 ga watan Yuli, 2020.

A rana 13 ga watan Maris ne Gwamantin Tarayya ta amince da sabon kasafin da aka rage zuwa Naira tiriliyan 10.523 da Ma’aikatar Kudi da tsare-tsaren Kasa ta gabatar wa Majalisar Zartaswarsa ta Kasa.

Sabon kasafin na kuma dauke da sauye-sauyen da aka yi wa kasafin kasa na matsakaicin zango daga 2029.

Da farko Shugaba Buhari a watan Disamban 2019 ya fara amincewa da kasafin 2020 na Naira tiriliyan 10.59 wanda ya sami amincewar Majalisar.

Da farko Majalisar ta amince da kasafin ne da aka yi a kan hasashen farashin gangar danyen mai $57.

Daga baya Gwamantin Tarayya ta rage kasafin saboda faduwar farashin mai sakamakon annobar coronavirus.