✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bukola Saraki ya shiga mahaifarsa a karon farko bayan faduwa zaben 2019

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya shiga mahaifarsa birnin Ilorin a ranar Asabar. Rabon Saraki da shiga Ilorin tun bayan faduwarsa zabe a…

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya shiga mahaifarsa birnin Ilorin a ranar Asabar.

Rabon Saraki da shiga Ilorin tun bayan faduwarsa zabe a 2019, lokacin da ya nemi konawa kujerarsa ta Sanatan Kwara ta Tsakiya.

Ya ziyarci mahaifar tasa ce don halartar taron addu’ar fidda’un cika shekara takwas da rasuwar mahaifinsa Olushola Saraki, da kuma bikin murnar cika shekara takwas da nada sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari.

Tarba daga magoya bayan Bukola Saraki lokacin da ya shiga mahaifarsa a Jihar kwara.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattaan ya samu gagarumar tarba daga dubban magoya bayansa a filin jiragen sama na Ilorin.

Daga nan magoya bayan sun raka shi har Fadar Mai Martaba Sarkin Ilorin.

Bukola Saraki wurin addu’ar mahaifinsa

Bayan nan ya ziyarci gidansu a mahaifarsa, inda babban limamin Ilorin, Alhaji Muhammad Bashir ya jagoranci gabatar da addu’o’i.

An ga ‘yar uwarsa kuma Minista a Ma’aikatar Sufuri, Gbemisola Saraki a wurin addu’ar.

Saraki, ya fadi zaben sake neman kujerar sanata ne ranar 23 ga watan Fabrairu 2019, karkashin inuwar jam’iyyar (PDP), inda ya samu kuri’a 68,994.

Abokin karawarsa na jam’iyyar APC, Ibrahim Oloriegbe ya kayar da shi da kuri’a 123,808.