✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bullar cutar huhun shanu a Bauchi ta tada hankalin gwamnati da makiyaya

Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin da aka fi kiwon shanu a kasar nan, inda kididdigar sashin kula da kiwon dabbobi na Najeriya ta…

Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin da aka fi kiwon shanu a kasar nan, inda kididdigar sashin kula da kiwon dabbobi na Najeriya ta nuna cewa tana da shanu fiye da miliyan daya da tumaki miliyan 3 da dubu 481 da 285 da awaki miliyan 5 da dubu 213 da 423.

Sai dai wadannan dabbobi annobar cutar ciwon huhu da ke kashe dabbobi na barazana gare su a jihar, lamarin da ya damu Fulani makiyaya da kuma gwamnati.

Gwamnatoci na yin allurar rigakafi ga shanu don maganin wannan cuta a kowace shekara.

Binciken da wakilin Aminiya ya yi ya gano cewa an samu fiye da shekara biyar ba a yi wa shanun allurar riga-kafin a jihar ba.

Wani jami’n Ma’aikatar Gona ta Jihar Bauchi, ya ce an yi hujin shanu lokacin mulkin Gwamna Isa Yuguda sau uku, sai kuma a gwamnatin da ta gabata aka yi hujin sau daya. Sannan na farkon  bana hujin da aka yi bai kai ko’ina ba.

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Abubakar Sarkin Shanun Dambam, ya ce shugabannin Fulani daga kananan hukumomi bakwai sun ba shi rahoton cewa shanunsu sun kamu da cutar huhu, kuma tumaki da awaki suna mura hancinsu na ruwa.

Kananan hukumomin da annobar ta shafa su ne Gamawa, da Dambam da Toro da Ningi da Bauchi da kuma Alkaleri.

Ya ce ko sun kai rahoto gwamnati ba ta yin komai a kai. “A gaskiya gwiwar Fulani a mace take kan kai rahoton bullar wata cuta; saboda sau da yawa mukan kai koke-koke amma ba wani mataki da gwamnati take dauka. Wannan yana nuna irin wariyar da gwamnatoci ke nuna mana domin yanzu idan manomi ya yi hasarar kayan Naira dubu 100 a gona sai ka ga an biya shi diyya. Ko a gwamnatin da ta shude lokacin da wannan matsala ta taso na samu Mataimakin Gwamnan na koka masa sai ya ce in je in rubuto. Cikin daren na rubuto na kawo masa ya ce Gwamna ba ya nan sai ya dawo. Har yau shiru amma da manomi ne ya samu wannan matsala da tuni gwamnati ta yi kokari a kai,” inji shi.

Ya ce rakuma ne suke kawo wannan cuta kuma rakuman daga kasashen waje ake taho da su. “Idan sun zo sai shanunmu su dauka ka san shi rakumi kusan kullum kamar cikin mura yake don haka muke kara rokon gwamnati ta taimaka wa Fulani makiyaya,” inji Shugaban.

Da yake tofa albakacin bakinsa, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Jihar Bauchi, Alhaji Muhammadu Husseini, ya ce a Karamar Hukumar Toro, har Shugaban Kungiyar na karamar hukuma ya fara nemo allurar rigakafin don yin huji ga shanu saboda ba su samu tallafi daga gwamnatin ba.

Shugabannin sun ce da wuya su iya gano adadin dabbobin da suka mutu sanadiyyar kamuwa da cututtukan saboda suna wurare daban-daban ne kuma Fulani in saniya ta mutu magana ta kare me za su yi tunda ta mutu.

Sun roki gwamnati ta taimaka ta samo alluran rigakafin cutar shanun kuma a sa ’yan Kungiyar Miyetti Allah ciki don su ne za su nuna ainihin inda Fulanin da ke da matsalar suke,

Kwamishinan Aikin Gona na Jihar Bauchi Alhaji Sama’ila Burga, ya tabbatar da bullar cutar a jihar. Alhaji Burga ya ce sun samu labarin bullar cutar huhun shanu a kananan hukumomi uku wato Bauchi da Alkaleri da kuma Ningi.

Ya ce lokacin da suka samu rahoto sai aka tura jami’ai wurare biyu da ake kiwon shanu inda bayan an dauki samfurin alamomin cutar an kai shi asibitin dabbobi na Bom da ke Jos a Jihar Filato aka yi gwaje-gwaje inda aka samu shanu 28  suna dauke da cutar huhun; a daya gonar kiwon shanun kuwa bayan an yi gwaje-gwaje an samu shanu 18 suna dauke da cutar,” inji shi.

Sai dai ya ce: “Gwamnati na iya kokarinta domin shawo kan cutar baki dayanta. Daga cikin hanyoyin da gwamnati za ta bi shi ne na farko za a yi allurar rigakafi saboda gwamnatocin da suka gabata ba su yi ba; sai da aka shafe shekara biyar kafin a yi na baya-bayan nan tsakanin watan Satumban bara zuwa Janairun bana. Watakila bai karade ko’ina ba, an samu ragowa shi ya jawo sake barkewar cutar amma yanzu gwamnati za ta yi allurar rigakafin ne baki daya kuma za a ci gaba da yi. Ana yi kowace shekara don tabbatar da koshin lafiyar dabbobinmu,” inji shi.

“Daga cikin matakan da muke dauka muna neman goyon Gwamnatin Tarayya a kai, shi ne za mu kafa wasu shingaye da kafin a wuce wadannan shingaye sai a tsare a duba lafiyar dabbobin idan an samu mai dauke da ciwo ba za a bari ta wuce ba sai an yi mata magani. Don akwai hanyar shanu tun daga Mali har zuwa Misau da Darazo har zuwa Bauchi, kuma hanyoyin suna nan. Ta haka ne za mu rika tantance lafiyar dabbobin da ke shigowa da wadanda suke fita,” inji Kwamishinan.

Ya ce gwamnati za ta yi wani gangamin wayar da kan Fulani game da alamomin kamuwa da cutar da bukatar da ake da ita na su rika kai rahoto duk lokacin da aka ga bullar wata cuta ta dabbobi don ta hanyar kai rahoto ne kawai a ofisoshin gwamnati a kananan hukumomi da cibiyoyin makiyaya za su samu bayanai a dauki mataki tun abin bai zama annoba ba.

Ya ce wadannan cututtuka da dabbobi ke dauke da su suna iya yada wa dan Adam kamar su tarin-fuka da sauran cututtuka.

Alhaji Burga ya ce babbar matsalar Fulani makiyaya ita ce rashin kai rahoton bullar cuta. Sai dai ya ce an yi wani tsari da a kowane wata a Ma’aikatar Gona za a rika karbar rahoto kuma ana daukar matakai a kai.

“Idan muna samun bayanai daga gare su, za mu dauki matakin da zai warkar da cutar kuma ya hana ta bazuwa nan take,” inji shi.