✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burin kungiyarmu shi ne  tallafa wa nakasassu da marayu – Lilian Akwuchi

Lilian Akwuchi wata ’yar aikin yi wa kasa hidama ce (NYSC) da ta yi suna wajen tallafa wa nakasassu da marayu a yankin Saminaka da…

Lilian Akwuchi wata ’yar aikin yi wa kasa hidama ce (NYSC) da ta yi suna wajen tallafa wa nakasassu da marayu a yankin Saminaka da ke Jihar Kaduna ta hanyar kungiyar da ta kafa, mai suna  Akwuchi  Risk and Bulnerable Foundation. A tattaunawar da ta yi da wakilinmu, ta bayyana yadda ta kafa kungiyar da irin ayyukan da take gudanarwa:

 

Da farko za mu so ki gabatar mana da kanki?

To sunana Lilian Akwuchi. Na fito ne daga garin Wukari a Jihar Taraba. Kuma a yanzu ina zaune a garin Saminaka,  da ke Jihar Kaduna.

Wane lokaci kika kafa wannan kungiya, ta tallafa wa naKasassu da marayu, kuma me ya karfafa maki gwiwar kafa kungiyar?

Na kafa wannan kungiya ce a shekarar 2014. Kuma ayyukan kungiyar su ne tallafa wa nakasassu da marayu da matan da mazansu suka rasu. Babban abin da ya karfafa mini gwiwar kafa kungiyar, shi ne saboda ni mai son  tallafa wa  nakasassu da marayu ne. Kuma na fara kafa kungiyar ce tun lokacin da nake karatu a Jami’ar Jos. A nan na fara aiki da wannan kungiya, inda na fara da nakasassun da suke jami’ar na tallafa musu da kayayyakin masarufi da abinci. Daga nan na shiga Bassa na je wata makaranta ta kurame na tallafa musu da kayayyakin abinci.

Yaya aka yi kika zo garin Saminaka?

Na zo garin Saminaka ne a matsayin ’yar yi wa kasa hidima (NYSC). Da farko Hukumar NYSC ta tura ni Kalaba ne a Jihar Kuros Riba. Sai na bukaci a dawo da ni Jihar Kaduna. Na shaida musu cewa ina son a kai ni yankin karkara ne. Shi ne aka turo ni Saminaka kuma  na ga yanayin yankin yana bukatar ayyukan wannan kungiya. Shi ne na sanya ayyukan  kungiyar a cikin aikin yi wa kasa hidima da nake yi.

Babban aikin da na fara yi a garin Saminaka, shi ne tallafa wa almajirai masu karatun allo ta hanyar tallafa masu tare da wayar masu da kai kan muhimmancin tsabta. A karon farko na samu wani malami ya tara mini almajiransa 200, na ilimintar da su kan muhimmancin tsabta kuma na raba masu takalman silifas 200. Kuma na tallafa wa kungiyoyin nakasassu da suka hada da guragu da makafi da kekunan guragu 15. Bayan haka na shirya gangamin wayar da kan matasa kan illolin shan miyagun kwayoyi a makarantun sakandare  da unguwannin da ke cikin garin Saminaka. Kuma ina da burin ci gaba da gudanar da wannan aiki a wannan yanki na Saminaka. 

Wadanne hanyoyi kike bi wajen samun kudin gudanar da ayyukan kungiyar?

Ni ne nake samar da kudin da nake kashewa wajen gudanar da ayyukan wannan kungiya domin ni ’yar kasuwa ce. Kamar yadda na fada maka tun farko ni ’yar Jihar Taraba ce, don haka ina kasuwancin gasasshen kifi da manja. Ina tafiya har kasar Kamaru don gudanar da harkokin kasuwanci. Don haka ni nake daukar nauyin kaina wajen gudanar da ayyukan kungiyar. Babu tallafin gwamnati ko na wata kungiya, ko na wadansu mutane wajen gudanar da ayyukan wannan kungiya. 

Mene ne burinki kan wannan kungiya?

Babban burina shi ne in ga cewa na ci gaba da tallafa wa nakasassu da marayu a  dukkan kasar nan, ta hanyar wannan kungiya. Domin a kullum idan na kwanta ina tunani ne kan halin da nakasassu da gajiyayyu da marayu suke ciki a kasar nan. Duk lokacin da na je wani gari na ga halin da nakasassu da gajiyayyu da marayu suke ciki,  nakan zauna in yi tunani kan halin da suke ciki. Don haka burina shi ne in ga na taimaka wa nakasassu da gajiyayyu da marayu a kasar nan.

Wane sako kike da shi ga  al’umma game da muhimmancin tallafa wa nakasassu da marayu? 

Babu shakka tallafa wa gajiyayyu da marayu da nakasassu yana da matukar muhimmanci. Don haka ina kira ga al’umma musamman masu hali, su rika tallafa wa nakasassu da marayu da gajiyayyu. A kasar nan muna da masu kudin da za su ciyar da al’ummar Najeriya baki daya. Idan ka tafi kasashen Turawa da Amurka za ka ga kowane mai hali yana da kungiyar da yake tallafa wa al’umma. Don haka ina rokon masu hali su rika taimaka wa jama’a musamman marasa karfi.

Kuma ina kira ga Hukumar NYSC kan su rika karfafa wa masu yi wa kasa hidima da suke son tallafa wa jama’a  gwiwa. Kamar ni Hukumar NYSC ba ta karfafa mini gwiwa ba. Ya kamata a ce ta karfafa mini gwiwa, kan wannan aiki da nake yi ta hanyar karrama ni, amma ba ta haka ba.

Kina da kira ga gwamnati?

Kirana ga gwamnatocin kasar nan shi ne su rika shiga yankunan karkara suna taimaka wa mutane. Domin gaskiya mutanen karkara suna cikin wahala. Babbar matsalarmu a Najeriya ita ce ba a kula da mutanen da suke zaune a yankunan karkara, sai lokacin zabe. Idan zabe ya wuce daga nan mutanen da suke zaune a karkara ba sa kara ganin kowa.

Mutanen da suke zaune a karkarar kasar nan da damansu ba su da hanyar mota, babu ruwan sha, babu makaranta, babu wutar lantarki babu asibiti. Don haka ina kira ga gwamnatoci  a rika shiga yankunan karkara ana taimaka wa jama’a.