✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burin masu zanen su tayar da fitina – Akibishop Kaigama

Akibishop na darikar Katolika na Jos kuma Shugaban Majalisar Bishop-Bishop din Katolika ta Nijeriya Akibishop Ignatius Kaigama, ya ce mutanen da suka yi zanen batanci…

Akibishop na darikar Katolika na Jos kuma Shugaban Majalisar Bishop-Bishop din Katolika ta Nijeriya Akibishop Ignatius Kaigama, ya ce mutanen da suka yi zanen batanci ga Manzo Allah a mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa mutane ne masu son tada fitina, don haka ya yi kira ga Musulmi da Kirista su guji yarda wadannan mutane suna hada su fada da tashin hankali.

Akibishop Kaigama ya shaida wa wakilinmu a Jos cewa, irin wadannan mutane burinsu shi ne su taba nan su taba can, don su tayar da fitina. Irin wadannan mutane da suke rubuce-rubuce ko zane-zanen batanci ga Musulunci, wani lokaci suna irinsa ga Yesu Almasihu domin tada fitina a tsakanin al’umma. “Addinin Kirista bai yarda da irin wannan al’amari ba, domin addinin Kirista bai yarda a bata addinin wani ba. Kuma addini Kirista bai yarda a yi amfani da addini a zubar da jini ba,” inji shi. Don haka ya yi kira ga irin wadannan mutane su daina aikata irin wannan rubutun batanci da ke tayar da hankalin jama’a.
Akibishop Kaigama, ya ce bai kamata wasu su yi ramako a kan wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. Ya ce idan har mutum ya yarda da Allah idan irin wannan al’amari ya faru a bar wa Allah Ya yi hukunci. “Amma a dauki bindiga ko wuka a yanka mutum ko a bindige shi bai dace ba. Saboda haka mu san yadda za mu zauna da juna lafiya. Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, irin wadannan mutane suna zanen batanci kan Yesu Almasihu ko Fafaroma don a tayar mana da hankali, amma ba mu yi komai ba abin ya wuce. Saboda haka idan irin wannan abin ya faru, mu kwantar da hankalinmu. Kashe-kashen da ake yi da sunan Musulunci ba su dace ba, domin na bata wa Musulunci suna a duniya,” inji shi.
Akibishop Kaigama, ya bukaci a guji fada da zubar da jinin al’umma saboda zabe, ya ce babu wanda yake samun riba sai asara.