Burin neman matsayi bai kai dan takara ga nasara a Najeriya- Kashim Shetima

Kashim Shettima

Tsohon Gwamnan jihar Borno kuma Sanata a yanzu mai wakiltar Borno ta Arewa, Kashim Shetima ya gargadi ‘yan siyasa da su yi taka-tsantsan wajen neman mukamin siyasa ta ko a mutu ko a yi rai.

Sanata Shetima, ya bayyana bukatar ce, a yayin taron tattaunawa ta shekara-shekara da kamfanin jaridun Media Trust masu jaridar Aminiya, ya shirya a yau Alhamis a Abuja, wato ‘Trust Annual Dialogue’, inda taken taron wanda shi ne karo na 17 ya maida hankali a kan shekara 20 da dawowar dimokoradiyya a Najeriya.

Ya ce, idan a ka duba tarihin tsayawa takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nemi matsayin shugabanci sau 3 ba tare da nasara ba, sai a na 4 ne ya samu nasara bayan an tilasta masa sake tsayawa takara.

“Haka nan wanda ya gabace shi shugaba Goodluck Jonathan burinsa shi ne ya tsaya takarar shugaban karamar hukuma, sai gashi a karshe ya samu, tare da nasara a na mataimakin gwamna, ya kuma yi gwamna, ya yi mataimakin shugaban kasa, sannan ya yi shugaban kasar ba ki daya.

A lokacin da ya nuna burin sai ya zarce, sai ya sha kasa. Shi kansa marigayi shugaban qasa Umaru ‘Yar Aduwa, burinsa shi ne ya koma koyarwa a jami’a bayan gwamna a jihar Katsina, amma sai gashi ya zama shi ne shugaban kasa a zaben da ya biyo bayan hakan.

ADVERTISEMENT

Haka nan ya ce, ya kamata ‘yan takara su san da cewa, “A cikin adadin wadanda za su tsaya takara, mutum daya ne kadi a karshe zai yi nasara.

Share