✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in ga al’umma ta ci gaba – Hajiya Hadiza A. Abubakar

Hadiza Abdul Abubakar, gogaggiyar ’yar Jarida ce da ta jima tana gwagwarmaya har ta kai matakin Edita kuma mataimakiyar Manajar shirye-shirye a kafar watsa labarai…

Hadiza Abdul Abubakar, gogaggiyar ’yar Jarida ce da ta jima tana gwagwarmaya har ta kai matakin Edita kuma mataimakiyar Manajar shirye-shirye a kafar watsa labarai ta Newage Network, ta kuma yi aiki da gidan Talabijin mai zaman kansa na farko a Arewacin kasar nan DITB (Desmims Independent Telebision) kuma kwararriya a bangaren kimiyyar siyasa. A hirar ta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da kuma wasu bangarori. A yi karatu lafiya:

 

Tarihin rayuwata:

Sunana Hadiza Abdul Abubakar.   Ni Bafulatana ce, iyaye na ’yan asalin Karamar Hukumar Keffi ne a Jihar Nasarawa amma a garin Kaduna aka haife ni.   A can na girma.   Mu hudu mahaifin mu ya haifa, uku maza, ni ce mace a cikin su.   Har na yi kuruciya na kai munzalin shiga makaranta aka sa ni a firamare ta Command Children School dake Dantuku Road, Kaduna bayan na gama sai na tafi karamar sakandare ta FGGC Bakori wato Federal Gobernment Girls Collage Bakori a Jihar Katsina.   Ina gamawa sai na  koma Kaduna na karasa babbar sakandare  a Essence International School daga nan sai na tafi  CAS Kano inda na yi karatun share fagen shiga jami’a  (IJMB) daga nan sai na samu shiga jami’a kai tsaye wato (direct entry admission) a Jami’ar Bayero ta Kano inda na samu digiri na farko a bangaren Kimiyyar Siyasa wato (Political Science). Ina gamawa bayan na yi hidimar kasa a Jihar Yobe sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) na yi digiri na biyu wato Masters a bangaren abin da ya shafi harkokin kasa da kasa (International Affairs/Diplomacy, MIAD).  Sannan na sake koma Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) na yi wani digiri na biyu (Masters) a bangaren harkokin ci gaba (Debelopment Studies).

 

Aiki:

Na fara aiki ne a lokacin da na gama hidimar kasa (NYSC) da gidan Talabijin mai zaman kansa na (Desmims Independent Telebision) DITB da ke Kaduna wanda shi ne gidan talabijin na farko mai zaman kansa a arewacin Najeriya inda a can na fara aikin jarida a matsayin mai karanta labarai kuma mai dauko rahoto, har ila yau kuma editar labarai sannan mai hada shirye shirye,  mai kuma gabatar da shirye-shiryen.  A gaskiya ina alfahari da yadda na koyi aiki a wajen a karkashin kulawar mamallakin tashar Marigayi Khalifa Baba Ahmed Allah Ya jikansa.

Na tuna shirina na farko da oga na  Malam Khalifa Baba Ahmed ya ba ni in gabatar mai taken (issues and situations) yanayi da matsaloli, shiri neda ake gabatar da shi mako-mako wanda ya kunshi siyasa da matsalolin tattalin arzikin kasa a Najeriya.  Bakon da na yi hira da shi a lokacin shi ne Marigayi Malam Umaru Dikko tsohon Ministan harkokin sufuri a Jamhuriya ta biyu (2nd Republic).

Mun tattauna a kan babban taron kasa a lokacin da na fara tuntubar Margayi Malam Umaru Dikko domin zantawa da shi a kan wannan shiri har ga lokacin tattaunawa da shi na fahimci mutun ne me saukin kai, bayan wani lokaci sai na bar DITB na koma aiki da gidan Rediyon Tarayya na Kaduna FRCN a tashar su da ke Kaduna a karkashin shugabancin babban daraktan su Barista Yusuf Nuhu inda na fara a matsayin mai dauko rahotanni inda manya irin su Malam Suleiman Kaura tsohon Kwanturolan tashar a wancan lokacin da Malam Nasiru Isma’il da Joseph Edegbo wanda dukkan su yanzu sun yi ritiya daga nan na zama edita wacce take tace labarai  inda nan ma manyan abokan aiki na kuma editoci irin su Malam Bashir Ahmed mai kula da sashin tace labarai (Controller Editorial) da kuma Hajiya Hauwa Abdullahi suka ba ni kwarin gwiwa a wurin gudanar da aiki na bayan na share wasu shekaru sai na bar FRCN a lokacin ina matakin albashi na GL10 a shekarar 2008 na koma kafar watsa labarai ta Newage network masu gabatar da shirye-shiryen su a tashar NTA da AIT daga majalisar tarayya na Inside the Senate da kuma House Ticket, ina kuma gabatar da shiriye-shirye duk mako inda a nan har na kai matakin mataimakiyar manajar shirye-shirye, bayan shirye shiryen da nake gabatarwa ina rubuta labarai sannan kuma ni Edita ce ina kuma shirya documentaries, ina nan wata rana sai oga na Malam Ibrahim Buba, ya wakilta ni ina kula da fannin lafiya na ma’aikatar lafiya matakin farko ta tarayya National Primary Health Care Debelopment Agency NPHCDA, kafin nan kuma ina shiryawa ma’aikatar lafiya ta tarayya wani shiri da ake kira Hands on Deck, a turance a lokacin ma’aikatar tana karkashin Farfesa Babatunde Osotimehin, wannan aikin da nake yi a bangaren lafiya na NPHCDA ya kunshi aiki da hukumomi daban-daban da bangaren tattara jama’a da sashin sadarwa da nufin fadakar da al’umma illar cutar shan inna (Polio), wannan bangaren kuma ya kunshi yawan tafiye-tafiye zuwa wurare daban-daban don ganin kokarin da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da sashin kula da lafiya na al’umma da Malaman addini da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki suke yi a lokacin allurar rigakafin shan inna ta Immunizations plus days (IPDs) don ganin an yaki wannan cutar ta shan inna a Najeriya baki daya.

Aiki a wannan bangare na NPHCDA ya sa na samu damar halartar tarurruka da dama na kwararru kamar na kwamitin sake yin dubi na kwararru kan harkar polio Edpert Rebiew Committee ERC da kwamitin masu ruwa da tsaki na cikin gida da na kasashen waje da masu doka a bangaren kula da kiwon lafiya, hakan kuma ya ba ni dama na ba da tawa gudumawar sosai a harkar yau da kullum a lokacin da na bar aikin jarida na koma bangaren harkokin ci gaba wato debelopment sector inda nake taimakawa da ba da shawara a kan harkokin kafofin watsa labarai.

Kalubale:

Na gode Allah domin ba yadda za a yi mutum ya yi aiki bai fuskanci kalubale ba. Kodayake kalubalen shi ne ya kara mini kwarin guiwa na ci gaba da gudanar da aiki na. Sannan kalubale ya zame mini kamar taki ne wajen gudanar da al’amurra  na rayuwa.

Nasara:

Alhamdu lillahi aikin jarida ne ya hada ni da mutane kala-kala har na koma bangaren hukumar lafiya matakin farko duka a aikin jarida wannan aiki ya ba ni dama wajen taimakawa na yada wasu muhimman al’amura don shawo kansu.

Burina a rayuwa:

Burina a rayuwa shi ne ganin yadda na kara dagewa wajen ba da tawa gudumawar ga ci gaban al’umma da taimakwa  wajen ba su damar fadin albarkacin bakin su ta dalilin aiki a  bangaren ci gaban al’umma (debelopment sector).

Tufafi:

A matsayina ta ’yar arewa suturar da tafi burgeni ya danganta daga kalan ta sannan na kan sanya kananan kaya da kuma kayan mu na arewa wanda ya kan sa na ji na samu natsuwa idan na sanya su.

Hutu:

Hutu ya danganta da irin lokacin da ka zaba wa kanka amma dai mafi yawan lokaci ina yin hutu ne tare da iyalina.

Kasashen da na je.

Na je kasashe da dama amma duk da haka ina da  sha’awar zuwa wasu manyan kasashe na duniya da ban je ba irin su Japan da Thailand da kuma Indiya.

Yawan iyali:

Alhamdu lilahi ina da aure da ’ya’ya biyu.

Shawara ga iyaye:

Nagode wa Allah kasancewa ni kadai ce  mace a gidanmu. Mahaifi na ya ba ni fifiko fiye da sauran ’ya’ya. Iyaye na sun tabbatar da na je makaranta ganin cewa karatun shi ne hanyar da rayuwa ta za ta inganta Fifita ni da iyaye na suka yi mini bai sa na yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ganin na cimma burin nan na rayuwa Saboda haka ilimi abun nema ne domin yana da muhimmanci kuma shi ne gishirin rayuwa da yake habaka tattalin arzikin kasa ya kuma inganta rayuwa, ya ba ka damar shiga siyasa. Sannan shi ilimi ba a ce na zamani kadai ba, har da na addini domin ko Allah ba za ka bauta masa da kyau ba muddin ba ka da ilimi. Kamar iyayen da suke fifita maza wajen ba su ilimi a kan ’ya mace, kuskure ne domin ita mace idan aka ilmantar da ita an ilmantar da al’umma. Don haka ina kira ga iyaye da su mayar da hankali wajen ganin sun bai wa ’ya mace dama ta samu ilimi. Haka ita ma gwamnati ina mai shawartar ta da ta maida ilimin ’ya Mace ya zama wajibi saboda yadda wasu iyaye ke hana su yin karatu suna dora musu tallace-tallace da yakan lalata musu tarbiya.