✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in ga ana yi wa al’umma adalci –Fatima Suleiman Takuma

  Fatima Suleiman Takuma tana daya daga cikin Alkalai a Babbar Kotun Jihar Neja.  Ta kasance tsohuwar Shugabar kungiyar Alkalai Mata Ta kasa da kasa…

 

Fatima Suleiman Takuma tana daya daga cikin Alkalai a Babbar Kotun Jihar Neja.  Ta kasance tsohuwar Shugabar kungiyar Alkalai Mata Ta kasa da kasa (International Federation Of Women Lawyers (FIDA).  ’Yar asalin Jihar Neja, ta fito ne daga wani gari da ake kira Takuma.  Mahaifinta tsohon dan jarida ne amma daga baya ya zama gogaggen dan siyasa.  Ya rike mukamin Sakataren Jam’iyyar NPN  (National Party of Nigeria) na kasa.  Ta fara aiki ne tun  daga matakin akawu kafin ta kai wannan matsayi na babbar alkali. A tattaunawarta da Aminiya ta tabo batutuwa da dama da suka shafi rayuwarta da ma wasu bangarori kamar haka:

 

Tarihin rayuwa:

Sunana Fatima Suleiman Takuma. Na halarci makarantu da dama.  Na fara karatu ne a garin Kaduna a matakin karatun renon yara (Nursery) daga nan na wuce matakin firamare.  A gaskiya yanzu ba zan iya tuna sunayen makarantun ba.  Daga nan na koma Gusau inda na ci gaba da karatu a matakin firamare har zuwa aji 4.  Daga nan na koma Minna inda aka mayar da ni wata firamare mai suna Waziri Primary School inda na kammala a shekarar 1979.  Mun zauna a garuruwa masu yawa saboda yake aka rika yi wa mahaifina canjin wurin aiki.  Daga nan na tafi sakandaren ’yan mata ta Gwamnatin Tarayya (Federal Gobernment Girls College), Akure.  Na shafe shekara 1 ne kacal inda aka mayar da ni Kwalejin ’yan mata ta gwamnati da ke Minna (Gobernment Girls Secondary School) Minna, nan ma ban dade ba aka mayar da ni Kwalejin ’yan mata ta gwamnati da ke Kwantagora (Gobernment Girls Secondary School).

Daga nan na bar makarantar saboda an mayar da Kwalejin ta bangaren karatun Kimiyya zalla ni kuma a lokacin ba na sha’awar yin karatun Kimiyya.  Don haka na yanke shawarar komawa Kwalejin da zan karanci abin da nake bukata. Daga nan na canza sheka zuwa wata Kwalejin inda na kammala karatu a shekarar 1983.  Daga nan na samu nasarar shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi Karatun Diploma a bangaren Shari’a a shekarar 1985. Daga nan na tafi Jami’ar Maiduguri inda na karanta digiri na farko a fannin Lauya (LLB).  Ina cikin karatun ne sai na ajiye saboda a wancan lokaci ne na yi aure kuma hidima ta yi mini yawa, don ba zan iya ci gaba da zirga-zirgar zuwa Jami’ar da ke da nisa da ni ba, kuma ina ci gaba da gudanar da harkokin gida.  Na ajiye karatun ne a kashin kaina.  Daga nan na koma Jami’ar Abuja kuma zan iya tunawa mu ne daliban farko a Jami’ar.  A shekarar 1990 ne na fara karatu a Jami’ar inda na kammala a shekarar 1995.  Daga nan na wuce Kwalejin Zama Cikakken Lauya (Law School) inda na kammala a shekarar 1996.

 

Yadda na fara aikin gwamnati:

Na fara aiki ne da Kotun Majistare da ke Jihar Neja bayan na kammala karatun diploma.  Na nemi mukamin rajistara ne (mai tattara bayanan kara) amma sai aka ba ni mukamin akawu.  An tambaye ni ko zan iya yi na ce me zai hana?  saboda sun fahimci an ba ni mukamin da ban nema ba. Bayan kimanin watanni shida ne aka yi mini karin girma zuwa mataimakin rajistara a wannan kotu da nake aiki.  Daga baya aka yi mini karin girma zuwa mukamin rajistara. Na fara aiki ne a shekarar 1987 da shaidar karatu ta diploma don haka bayan shekaru 3 watau a 1990 sai na koma karo ilimi inda na samu digiri a fannin shari’a (LLB).  Daga nan na samu karin girma inda aka ba ni mukamin Mataimakiyar Babbar Alkali, amma a wancan lokaci nakan zauna ne tare da alkali don na ga yadda ake shari’a don na samu gogewa..  Daga nan likkafa ta ci gaba inda cikin hukuncin Allah a yau na zama Babbar Alkali ta Babbar Kotun da ke Jihar Neja.

Daga cikin nasarorin da na samu na taba rike mukamin Shugabar kungiyar Lauyoyi Mata ta kasa da kasa a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017.  Gaskiya na ji dadin rike wannan mukami.  Don babban burina shi ne in ga ina taimakon al’umma a bangaren shari’a musamman gajiyayyu.  Daga cikin shari’un da na taba yi wanda ba zan taba mantawa da ita a rayuwa ba ita ce na wata yarinya da wadansu batagari suka yi wa fyade a garin Kwantagora.  Bayan an yi mata fyade sai aka bar ta a yashe, inda aka dauka ma ta rasu.  Nan take na hada tawaga muka nufin asibitin da aka kwantar da ita.  Nan take na nemi bayanin daga wajen Likitan da ke duba ta inda ya bayyana mini cewa suna da karancin kayayyakin aikin da za su yi mata cikakken bincike.  Daga nan na canza mata asibiti, inda na kai ta asibitin IBB.  A can ne aka gano cewa batagarin sun dura mata maganin da ake ba doki ne da hakan ya sa ta fadi sumammaye har na tsawon lokaci.  Wadanda suka aikata mata hakan ashe ’ya’yan masu hannu da shni ne. Sun yi kokarin ganin an kwantar da batun amma na yi tsayin-daka ta hanyar yatata batun a kafofin watsa labarai da shigar da kara a kotu da kuma daukaka kara har sai da aka hukunta su. 

Daga nan na ci gaba da kai mata ziyara a asibiti har sai da ta samu lafiya.  Bayan nan sai na ga cewa idan ta ce za ta koma gidansu, hankalinta zai ci gaba da tashi saboda halin da ta tsinci kanta a ciki, nan sai na yanke shawarar na ajiyeta a gidana don cigaba da kula da ita har na tsawon watanni shida.  Daga nan na sallameta kuma har yanzu ina ci gaba da tuntubarta don sanin halin da take ciki.  Don haka babban burina in ga ana kwato wa marasa galihu hakki.

 

Yadda na yi kuruciya:

A gaskiya a lokacin da nake karama ba na jin magana (dariya).  A wancan lokaci ina karatun sakandare anna na ki yarda na zauna a cikin makaranta.  Na gwammace in an tashi daga makaranta na koma gida washegari sai na koma duk da nisan da ke tsakanin makarantarmu da gida.  A lokacin sai da wani aminin Babana, Sakataren Dindindin (Permanent Secretary) ya rika dauka ta zuwa manyan shaguna yana yi mini sayayya don na rika zama a makaranta amma duk da haka sai da na ci gaba da komwa gida.  Na rika fadawa mahaifina cewa ba na son zama a makaranta da hakan ta sa mahaifina ya shiga damuwa.  Idan ya tambaye ni dalili, sai na ce masa babu wani dalili.  Daga nan ya rika rarrashina ta hanyar yi mini wayau da hakan ta sa na koma makaranta. Mu biyar ne a wajen mahaifinmu, kuma ni ce ta uku, nakan bi ’yan uwana maza zuwa filin kwallo.  A haka na samu sha’awa game da wasan kwallon kafa.

 

kalubalen da na fuskanta a rayuwa:

Ban fuskanci kalubale da yawa a rayuwa ba, ganin cewa komai ina bin sa ne a hankali ba tare da yin garaje ba.  Kuma ina kokarin ganin na ba kowa hakkinsa musamman a lokacin da nake yin alkalanci a kotu.  Ba na shakkar kowa, abin da ke gabana shi ne in ba mai gaskiya, gaskiya.  Ba na yarda a bi ta wajen iyalina don in take gaskiya.  Abin da nake bukata daga wajen iyalina shi ne addu’a da fatan alheri. Haka kuma ba a rasa kalubale a gida, don ko a tsakanin harshe da hakori ma a kan saba ballantana a tsakanin ’yan adam.  Amma idan an yi hakuri da juna komai sai ya wuce.

 

Sha’awata ga bangaren shari’a:

Na fara sha’awar aikin shari’a ne tun ina karatu a matakin firamare.  A lokacin akwai wadansu makwabtanmu mata da miji da kullum sai an ji yana dukanta.  Idan na nemi mu je don mu cece ta sai a fada mini ai ba a shiga tsakanin miji da mata.  Sai wasu su rika cewa da akwai lauya ne a kusa da ya shiga don ya sasanta su.  Daga nan na fahimci karatun Lauya zai sa na iya shiga don kare wa irin wannan mata da duk wanda ake zalunta hakki.  Hakan ta sa na rungumi karatun Lauya kuma yana daga cikin dalilin da ya sa na zama Shugabar kungiyar Mata Lauyoyi ta kasa da kasa.

 

Abubuwan da na koya a rayuwa:

Kada ka taba yarda da kowa, ko da abokanka ne.  Hatta ’ya’yana ba kasafai nake yarda da su 100 bisa 100 ba a wasu lokuta (Dariya).  Za ka zauna tare da abokanka ko kawaye ka fada musu sirrinka amma da zarar ka juya baya su ne na farko da za su yi kokarin tona maka asiri.  Hakan ta sa na dauki dabi’ar zama ni kadai a kowane lokaci inda nake yawan yin karatun Alkur’ani don yana samar mini da natsuwa a zuciyata ba tare da shiga wata damuwa ba. 

Burina:

Bayan na cika burin zama Lauya kuma yanzu na zama Babbar Alkali ta Jihar Neja, yanzu burina shi ne in kasance Babbar Alkali ta Kotun daukaka kara da ke kasar nan.  Hakan zai sa na ci gaba da kare hakkin marasa galihu.

 

Kyautar da aka  taba ba ni wacce ba zan taba mantawa da ita ba:

Marigayi tsohon mijina ya taba yi mini kyautar wani agogo mai dauke da zinare da azurfa.  Yanzu haka ina ajiye da wannan agogo kimanin  shekaru 30 kenan.  Duk da agogon ya daina aiki, amma na ki rabuwa da shi saboda tarihin da ke tattare da shi.

 

Yadda na hadu da mijina:

Mun hadu ne a lokacin da yake rako wani abokinsa zuwa zance wurin ’yar uwata.  Daga karshe abokinsa bai samu nasarar auren ’yar uwar tawa ba, amma mu kuma sai Allah Ya hada auren mu.

 

Kyawawan halayen maigidana:

Gaskiya maigidana yana da halaye masu kyau.  Duk da dai a tsakanin harshe da hakori akan saba, amma a gaskiya bai taba bata mini rai ba.  Hasalima yana mutunta ni, ya kula da ni tun kafin mu fara haihuwa har muka samu karuwar ’ya’ya.   Ya ba mu hakki daidai gwargwado.  Shekararmu 23 da aure kafin Allah Ya yi masa rasuwa amma bai taba kirana da sunana ba, sai dai ya kira ni da “masoyiya”.

 

Abin da nake yi kafin na kwanta barci da kuma idan na tashi da safe:

Duba kafar sadarwar WatsApp saboda na ga sakonnin da nake samu.  Sai dai a wasu lokutan nakan yi tunanin na daina hakan, don tamkar ina takurawa rayuwa ta ce.

 

Kayayyakin da na fii sha’awa:

Agogon hannu da takalma da kuma jakunkuna.

 

Tufafin da na tsana:

Masu shara-shara da ke nuna tairaici.

 

Abincin da na fi so:

Na fi sha’awar abincin kabilar Inyamurai irin su miyar Oha ko ta Onugbu ko ta Nsala ko ta Edi Kan Kong da sauransu.

 

Nasihar mahaifiyata:

Kullum takan ce mini in rika yin hakuri a rayuwa.

 

Shawara ga masu tasowa:

Su rika yin hakuri a rayuwa.  Su rika bin komai sannu a hankali.  Su rika neman shawarwari a duk lokacin da wani abu ya shige musu duhu.  Su rika yin biyayya ga na-gaba.  Su rika sanya tsoron Allah da yin gaskiya a rayuwa.  Su dage wajen yin karatu tukuru.  Idan suka rike wadannan abubuwa ko shakka babu za su samu nasara a rayuwa.