✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in ga mata sun samu ilimi – Hajiya Hauwa Sani

Tarihinki: Sunana Hajiya Hauwa Sani dan Gyatin.   An haife ni a garin Kafin Hausa cikin yankin masarautar Hadeja a Jihar Jigawa.   Na girma a wajen…

Tarihinki:

Sunana Hajiya Hauwa Sani dan Gyatin.   An haife ni a garin Kafin Hausa cikin yankin masarautar Hadeja a Jihar Jigawa.   Na girma a wajen kakata a Gaya da ke Jihar Kano.   Na yi makarantar firamare  a Gaya daga nan na wuce  sakandare inda na kammala sakandare a 1989 kuma iyayena sun yi mini aure a 1990.

Daga nan na fara aikin koyarwa a kauyen dangyatin da ke karamar Hukumar Miga a lokacin maigidana yana aikin banki a can Buniyadi da ke Jihar yobe shi ne na koma can wata makaranta da ake kira  Central Primary ta Buniyadi na ci gaba da aikin koyarwa.

Bayan mijina ya bar aiki saboda an yi masa sauyin wajen aiki zuwa Yola ta Jihar Adamawa sai muka dawo gida na kama sana’ar saka kafin na koma aikin koyarwar a makarantar da na bari ta dangyatin kuma na ci gaba da karatu daga nesa  (Distance Learning) domin mallakar takardar shaidar malanta (NCE) a Jahun. Da na gama ne a tsakanin shekarar 2004  zuwa 2006 sai aka ba ni matsayin (Kodineta) mai kula da makarantun mata zalla. 

Ni ce nake fadakar da yara mata ta hanyar yadda za su kula da kansu a bangaren rayuwa ta yau da kullum a matsayinsu na mata wadanda za su iya zama iyaye a nan gaba. Daga nan ne aka nada ni  shugabar Kwalejin ’yan mata ta Miga wato Principal a 2013.

Yanzu haka ina karatun digiri na biyu wato Masters a Jami ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse (Federal Unibersity Dutse) a Jihar Jigawa ina yin nazari a kan harshen Turanci kuma na kammala karatun digirina na farko a ita wannan Jami a a 2016.

kalubale:

Ni ban samu wani kalubale ba illa dai a lokacin na bar mijina a kauyanmu dangyatin ni kuma na koma gidan dan uwansa saboda karatu kuma ga tunanin jarabawa wannan ya sa ni cikin damuwa matuka kuma ana ta yi mini barazanar cewa karatun Harshen Ingilishi abu ne mai wahalar gaske amma dai har na gama ban fuskanci wata matsala ba kamar yadda ake ta nuna mini.

Duk da yake ban shiga karatun da wasa ba na samu karatun da sauki. Na samu sakamako mai kyau a cikin karatuna kuma na yi sa’a mijina ya karfafa mini gwiwa.   Kuma daga cikin irin gudunmawar da na bayar na yi aiki da Hukumar Esspin wajen fadakar da mata muhimmancin ilimin ’ya’ya mata, na sha gwagwarmaya matuka wajen bai wa ’yan uwana mata ilimi a wannan bangare.

Sakamakon irin kalubalen da na fuskanta da irin bayanan da nake samu na cewar ana neman mata masu digiri wadanda za su rika fadakar da mata a karamar Hukumar Miga, wannan ya sa na dage wajen karo ilimi har na samu shaidar karatu na digiri.

Burina: 

Burina na ga yara mata sun dage wajan neman ilimin zamani wanda sakamakon haka ne ya sa na bude makarantun Islamiyya guda 10, biyar na yara, biyar kuma na matan aure domin in bai wa yara mata ilimi, kuma dukkansu a yankunan karkara na bude su.  A kauyukan da na bude irin wadannan makarantu akwai Gora da dangyatun da Zango da Rukumawa da Ganuwa da Koya da kuma ’Yanduna da kauyen Zareku da sauransu.

Abin da na fi so a rika tunawa da ni a kansa:

Idan matan aure suka kai ga kammala karatunsu na samu abin alfahari wanda za a rika tunawa da ni ko na mutu, sabod ina tausayawa matan karkara ganin yadda matan suke zaune kara zube babu ilimi, wannan abu na ci mini tuwo a kwarya.

Yabo ga Gwamnati:

A gaskiya ina yaba wa gwamnatin Jihar Jigawa da take bai wa ’ya’ya mata tallafin karatu na Naira dubu ashirin-ashirin kowaccensu. Wannan tallafin yana taimakawa iyaye wajen sanya mata su dage wajen neman ilimi domin irin waxannan kuxi ba qaramin tasiri suke da shi ba wajan inganta rayuwar mata a yankunan karkara.

Abin da ya fi tsaya mini a rai:

Akwai wata yarinya da ta tava faxa min cewa abokin mahaifinta ya tava yin lalata da ita.   Wannan al’amari ya tsaya mini a raina.  

Wata kuma ta tava faxa mini cewa wani mai kanti ya yi qoqarin vata mata rayuwa.   Irin waxannan abubuwa na ban takaici suna da yawa a karkara, idan na tuna abin yana ba ni takaici matuqa.

Abin da ya fi vata mini rai:

A halin yanzu babu abin da ya fi vata mini rai kamar tallar da ’yan mata suke yi na cin kasuwannin qauye inda ba sa komawa gida sai da tsakar dare wani lokacin ma iyayensu har sai sun yi barcci.

Qasahen da na ziyarta:

Ban da Saudiyya ban je wata qasa ba amma na gamsu da tsarin qasar Saudiyya, domin mutane ne masu gaskiya kuma suna gudanar da komai cikin tsari.

Batun iyali:

 Ina tare da maigidana Alhaji Sabo Xangyatin kuma Allah Ya albarkacemu da ’ya’ya 10, amma xaya daga ciki ta rasu.  Yanzu haka ina da ’ya’ya 9, maza 3 mata 6.

Abin da ba na so:

Ban son qarya.  Ban son zalunci domin ko a makarantata ban son in ga ana zaluntar yara kuma a duk lokacin da na ga haka nakan xauki mataki.