Da Dumi Dumi

Burina in ga talaka ya samu ilimi – Hajiya Maryam Garba

Hajiya Maryam Garba Wamakko ’yar asalin Jihar Sakkwato ce daga karamar Hukumar Wamakko , ta fito daga wani gari da ake kira Birnin Kimball gidan Safna, a can ne ake sarautar garin, a yanzu babbar Malama ce a Kwalejin Horar da Malamai ta Shehu Shagari, (Shehu Shagari College of Education) da ke Sakkwato.   Mai son ci gaban talakawa ce, musamman a bangaren samun ingantaccen ilimi. A tattaunawarta da Aminiya  ta tabo tarihin rayuwarta kamar haka:

 

Tarihinta:

Sunana Maryam Garba Wamakko wadda aka fi sani da Maryam Wamakko. An haife ni ne a garin Sakkwato cikin karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu a wata unguwa da ake kira Kalhu.   Na yi karatun allo a  makarantar Malam na Yabo wanda matarsa ta karantar da ni da ake kira Yaya, Allah Ya jikanta da rahama. Daga nan na shiga makarantar firamare a Secretariat wacce a yanzu ta koma Attahiru Bafarawa da ke kan titin Zuru da ke birnin Sakkwato daga shekarar 1980 zuwa1986.   Bayan nan na je sakandaren mata ta gwamnati ta Kimiya da ke garin Tambuwal a tsakanin 1987 zuwa1990 sai na koma makarantar mata ta gwamnati GGC daga 1990-1992, daga nan na samu nasarar shiga Jami’ar Usman danfodiyo ta Sakkwato na yi karatun share fagen shiga jami’ar na shekara biyu.   Da na kammala sai na shiga ajin digiri duk a jami’ar a 1995-1999 inda na kammala digirin cikin nasara a shekarar 2000 na je bautar kasa a Jihar Kwara na kare a 2001 a Jihar Zamfara, na yi digiri na biyu a 2008-2012.

ADVERTISEMENT

 

 Fara aikin gwamnatinta:

A 2001 na fara aiki da Hukumar Bayar da Ilmin Firamare a yankin Wamakko mahaifata ta asali a wani gari da ake kira Bakin Kusu daga nan aka yi min canjin wajen aiki zuwa firamaren Muhammad, bayan nan aka mayar da ni Bakin Kusu a matsayin shugabar makaranta bayan nan ne maigidana Alhaji Buhari Yusuf Tambuwal, Allah Ya  jikasaya nema min aiki da Hukumar Kula da Malamai ta jiha na koma wurinsu da aiki matsayin malama mai daraja ta daya dake koyar da Ilmin sanin yanayin kasa (geography) a sakandaren Sani Dingyadi  a haka ne kwatsam aka mayar da ni Kwalejin Horar da Malamai ta Shehu Shagari a 2003 tun a wancan lokacin har yanzu can nake karantarwa tun ina mataimakiyar Malama har na kai babbar Malama.

 

Mukaman da ta taba rikewa :

Na rike shugabar fannin kimiya na kungiyar malamai mata a Kwalejin ilmi ta Shehu Shagari daga 2003-2011, Mamba a kwamitin raba wurin kwanan dalibai da gudanar da jarabawa, mataimakiyar darakta a MIS, jami’a a kula da tarbiyar dalibai, mataimakiyar babban sakatare kuma mataimakiyar shugaban  kungiyar malamai na fanin sanin yanayin kasa (Geography) ta kasa reshen Sakkwato, mukaddashiyar darekta na MIS a 2011-2012, mamba a kwamitin tsaftace muhali na wajen kwanan dalibai duk a makarantar.

 

kuruciyarta:

A gaskiya lokacin ina karama na tashi da nutsuwa da basira da girmama manya, ba ni da abokin fada, a jinmu ni ke yin ta daya, gani da son zuwa makaranta ba na yawon banza kamar yadda wasu yara ke yi kan haka ya sanya mahaifiyata ke alfahari da ni.   Na tsaya na yi karatu na zama abin kwatance da alfahari ga halaye nagari.

 

kalubalen da ta fuskanta:

kalubalen da na fuskanta a rayuwata shi ne wurin neman ilmi domin ni na zamanto yarinya mai son karatu amma mahaifina ya rasu tun ina aji daya na firamare.   Ni kadaice a wurin mahaifana  da uwayena suka rike kuma suka ki daukar nauyin karatuna a haka har na samu aikin goge-goge a ma’aikatar ilmin Larabci a 1993, ana biyan Nairaa 600 a wancan lokaci daga nan ne na yanke shawarar komawa makaranta na yi digiri da kudin da nake samu.  Ni na dauki dawainiyar karatuna. Kwatsam sai Sakataren wurin a lokacin dan uwana ne na jini ya ce ko dai na bar aiki ko kuma na bar makaranta, in zabi daya.   Na roke shi da ya taimaka min ya san mahaifina ya rasu kuma mamata ba ta da karfi ka bar ni da aikina na yi makaranta amma ya ce bai yarda ba. Na ce masa na zabi makaranta, nan take ya gaya min kada na sake komawa ma’aikatar an kore ni, haka na tafi na gayawa mamata ta ce na yi hakuri Allah Zai kawo min wata hanya.   A makon ne Malam Sani Ambursa ya kaini wajen da ake bayar da tallafin karatu ga mata ’yan asalin Jihar Sakkwato na samu na cigaba.  A makaratar ce Allah Ya hada ni da mijina a 1995 ya dauki nauyin karatuna gaba daya sai abin ya zama tarihi, kan haka nake da burin dan talaka ya samu ilmi kamar dan kowa a al’umma.

 

Darussan da ta koya:

Kar ka yarda da kowa a duniya sai mahaifiyarka, ko danka ka rika ba shi yarda dari bisa  dari.   A wannan lokaci akwai tsoro ga rayuwar mutane domin zaka samu kanka cikin mutane da kake ganin amintattunka ne daga baya su koma suna bata maka lamari ga jama’a don kawai rashin adalcin dan Adam. Daman duk wanda ya sanni ya sanni da kau da kai da hakuri da yafe duk abin da aka yi mini hakan ya zama babban darasi gare ni da ba don haka to da na shiga wani mummunan hali.

 

Burinta:

Bayan na samu digiri na daya da na biyu, in samu na uku, in zama Farfesa don kara wa dan talaka karfi da kwarin gwiwa cewa kowa na iya zama wani abu in ya jajirce. Sannan in taimaki talaka wajen neman ilimi.

 

Kyautar da aka yi mata da ba za ta manta ba:

Margayi mijina Alhaji Buhari Tambuwal na ba shi labarin ’yar da mahaifiyata ta rika ta biya wa mahaifiyarta Hajji sai ya ce Allah ya sauwaka kowa ya sanshi da wannan kalmar ba za to ba tsammani kwana daya da ba shi labarin sai ya shigo gida ya kirani na zo ya ce mini bude gyalenki abu kamar wasa na kara gyalen ya rika zuba kudi lokacin Naira 20 ce babbar kudi  sai da ya cika min gyalen da kudin,  na ce masa kudin mene ne sai ya ce na je na biya wa mahaifiyata Makka Wallahi wannan kyautar har na koma ga Allah ba zan manta da ita ba.  Allah ya gafarta masa. 

 

Wallafe -Wallafe da kasidu: 

Ina da Wallafe -Wallafe har guda bakwai da kasidu 12.

 

Abincin da take so:

Tuwon shinkafa da miyar kuka.

 

Karramawar da aka yi mata: 

A shekarar 1998 kungiyar dalibai ta Ilmin yanayi dake Usman Danfodiyo sun ba ni ‘macen shekara da mamba mafi kwazo a kwamitin shirye -shirye.   A 2011 an karrama ni da kyautar ma’aji mafi kwazo da gaskiya a kungiyar malamai mata ta Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari. 

 

Mukaman da ta rike a kungiyoyi masu zaman kansu:

Sakatariya a kungiyar ci gaban matan aure da ko’odinata a kungiyar sana’a ta matan arewa da uwa mai ba da mama da Sakatariya a kungiyar muryar  matan jiha da ko’odinata ta yanki na kungiyar matasa a harkar noma. Da sauransu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya