✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in gina gidan marayu – Hajiya Jummai Ali Fago

Tarihinta: Sunana Hajiya Jummai Ali Kazaure.   An haife ni ne a Unguwar Fago da ke garin Kazaure a ranar 17 ga watan Afrilun 1966.   An…

Tarihinta:

Sunana Hajiya Jummai Ali Kazaure.   An haife ni ne a Unguwar Fago da ke garin Kazaure a ranar 17 ga watan Afrilun 1966.   An yi mini aure ne ashekarar 1985 a lokacin ina da shekara 19 da mijina Alhaji Sule b.I.O.  Yanzu haka muna da yara 3 da jikoki takwas.  Na yi karatun firamare a L.E.A. Primary School Fago da ke garin Kazaure. 

Sannan na yi karatun sakandare a Kwalejin ’Yan Mata da ke Kabomo a Jihar Katsina kuma na yi karatuna na NCE Kwalejin horon malamai ta Gumel da ke Jihar  Jigawa inda  karanta biology da chemistry daga nan na ta fi Jami ar Bayero da ke Kano na karanta Bsc. Education.  Kafin na je Jami’ar Bayero na fara aiki ne da ma’aikatar ilimi ta Jihar Kano a lokacin ina yin malamanta ne a Kwalejin ’Yan Mata ta garin Kazaure da ke Jigawa. 

A shekarar 1989 ina koyarwa ne na kammala karatun digiri a Jami ar Bayero.   Da na kammala karatun digirina sai aka tura ni Kwalejin ’yan mata ta Kaugama a matsayin malama.  Ana wannan hali ne sai na tafi karatun digiri na biyu watau (Masters) a Jami’ar Bayero inda na sake karanta fannin mulki da tsare tsare a bangaren ilimi.   Bayan na dawo na zauna a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwaram wacce a halin yanzu ita ce makarantar hadaka watau Unity School ta ’Yan mata da ke Gwaram a matsayin mataimakiyar Shugaba (bice Principal).  Daga nan aka sake mayar da ni Kwalejin ’Yan Mata da ke Kaugama kuma aka kara mini girma na kai matakin Darakta amma duk da haka ina koyarwa ne a cikin aji.  Daga nan aka same mayar da ni Kwalejin ’yan mata ta babura a matsayin Shugaba (Principal) a shekarar 2010 kuma har yanzu a can nake yin aiki.  A haka na samu damar komawa Jami’ar Bayero inda na yi karatun digiri na uku (Phd.). Daga nan ne aka canza mini wajen aiki inda aka mayar da ni Kwalejin Horar da Malamai ta Gumel a matsayin Babbar Malama.  A karshen wannan wata ne zan ajiye aiki a matsayin Shugabar Kwalejin ’Yan Mata ta babura don na koma Kwalejin Horar da Malamai ta Gumel don na ci gaba da aiki.

Tallafin da take yi wa mata:

A kodayaushe ina kara wa mata ’yan uwana kwarin gwiwa wajen neman ilimi, domin mace mai ilimi ta fi jahila mara ilimi daraja kuma ta fi sanin yakamata a harkokin rayuwarta.  Ilimi shi ne ginshikin rayuwar al’umma musamman mata

Na sha tallafa wa mata da kayan karatu da shawarwari nagari domin in kara wa mata ‘yan uwana karfin gwiwa a kan su dage wajen neman ilimin zamani da na addini.  Hakan ta sa da yawa daga cikinsu a yau sun samu shaidar karatun digiri da ta malanta ta biyu (Grade II).

Biyayyar matan da suka samu ilimi ga mazajensu: 

A gaskiya in dai maganar rashin tarbiyya ne babu kamar mata marasa ilimin zamani da na addini domin ni na gani da idona inda wata mata saboda mijinta ya yi mata fada a kan wani abu da bai taka kara ya karya ba ta rika zagin mijinta kamar tana yi wa dan cikinta fada.

 Amma saboda rashin adalci na wasu mutanen in suka tashi magana ba su da aiki kullum sai bata sunan mata ma’aikata ko wadanda ke da ilimi suna bata su da wadansu kalamai da halaye marasa kyau.

 Sau da yawa mata marasa ilimi suna da karancin tarbiyyakuma ba sa girmama mazajansu. Wallahi mace mai aiki kuma mai ilimi ta fi girmama mijinta don duk abin da mijinta zai yi mata ko zai ba ta ba ta rainawa, hasalima tana gaba-gaba wajen taimakonsa da iyali baki daya don ta san muhimmancin yin hakan. 

Burinta a rayuwa:

Ina da burin gina gidan marayu.  Da Allah Zai mini arziki, ba ni da burin da ya wuce in rika taimaka wa marayu da gajiyayyu da daukacin talakawa.  Talakawa na shan wahala musamman mutanen karkara don a lokacin azumi za ka tarar mace ta zuba ruwa a cikin kwarya don ya yi sanyi idan an sha ruwa ta yi amfani da shi saboda ba ta da halin sayen kankara ko randa saboda tsabar talauci.  Amma abin bakin ciki sai ka tarar wani mai kudin duk shekara sai ya je Makka da Umra amma ga talakawansa suna cikin halin kuncin rayuwa.

Da ni na samu damar hakan, to ba zan rika zuwa Makka da Umrah a kowace shekara ba, sai na rika amfani da kudin wajen tallafawa gajiyayyu.  Na ziyarci kauyuka da yawa a lokacin azumi inda na tarar da yawan magidanta ba sa iya dora abinci, sai dai su sha kunu ba ko kosai idan an sha ruwa sannan da shi suke yin sahur da asuba, saboda tsabar talauci.

Abin da ya fi ba ta sha’awa:

Abin da ya fi ba ni sha’awa shi ne karatun na’ura mai kwakwalwa watau kwamfuta.

To menene yafi baki tsoro arayuwa?

Ni abindayafi bani tsoro bakamar karatun kwamfuta alokacin bansan menene kwamfutaba saboda ina tunanin karatunta yanada wahala domin lokacin dazanyi karatun digirina da akace dole sainayi karatun kwamfuta naj imatukar tsoro sosai

Mene ne yake burgeki?

Ina sha’awar na ji an ce mace tana yin karatu da Turanci da Hausa.  A gaskiya yin haka na burge ni kuma yana ba ni sha’awa.

kasashen da ta ziyarta:

Na je Saudiyya sannan na ziyarci kusan dukkan Jihohin Najeriya a lokacin da nake Shugabar Kwaleji a wajen taron shugabannin makarantun sakandare saboda ina cikin kungiyar Malamai.  Zan iya cewa kusa babu jihar da ban taba ziyara a Najeriya ba.

Abincin da ta fi bukata:

Na fi sha’awar Laban irin ta kasashen Larabawa da kuma wainar fulawa.

Tufafin da ta fi sha’awa:

A wajen yin kwalliya na fi sha’awar amfani da atamfa.  Hakan ce ta sa na fi yin amfani da atamfa a kodayaushe.

Shawara ga matan aure:

Su ji tsoron Allah, su rike mazajensu cikin amana da daraja.  Su daina amfani da jita-jita a kan yanke wani hukunci da ya shafi zaman aure.  Hakan ke sanya ake yawan samun mutuwat aure musamman a kasar Hausa.