✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in ilmantar da mata da kananan yara – Murjanatu Ibrahim Duwan

Malama Murjanatu Ibrahim Duwan malama ce da ta yi gwagwarmaya a wajen neman ilmi tare kuma da bayar da shi. Mace ce mai kamar maza…

Malama Murjanatu Ibrahim Duwan malama ce da ta yi gwagwarmaya a wajen neman ilmi tare kuma da bayar da shi. Mace ce mai kamar maza a fannin neman ilmi, duk kuwa da cewa ta yi aure ne tun tana da shekara 11.  Sannan bayan ta fara haihuwa ne ta koma makaranta don yin karatu gadan-gadan.  Aminiya ta samu zantawa da ita inda ta bayyana tarihinta da nasarori da kuma kalubalen da ta fuskanta a rayuwa kamar haka:

 

Aminiya: Ko za mu ji takaitaccen tarihinki?

Malama Murjanatu: A’uzu billahi mina lshaidanir rajim, Bismillahir-rahmanir-rahim. Alhamdulillahi. Sunana Murjanatu Ibrahim Duwan,wannan sunan maigida ne. Haka kuma sunana Murjanatu Ibrahim Kaita,shi kuma sunan mahaifina kenan. An haife ni a garin Kuraye da ke cikin karamar Hukumar Charanci a yanzu a 1963. Bisa ga al’ada ta wancan lokacin ana fara kai yaro makarantar addini ne kafin ta boko,to ni ma haka aka yi mini. Na kuma yi firamare a tsawon shekara 6 a tsakanin garin Maidabino da ke karamar Hukumar danmusa a yanzu da kuma garin Jikamshi. Wato nayi shekara 4 a can Maidabino sannan na gama a Jikamshi a shekarar 1974. Na kuma fara samun karatun addini, wato tun daga babbaku har zuwa tattashiya a hannun wani malami mai suna Malam Usman dan Ali a garin Maidabino, kuma a wajensa na cigaba da karatun addini har na tsawon wannan shekara 4 da na yi a can. Wato dai ina jin ina da kimanin shekara 8 zuwa 9 kenan bisa doron kasa kafin mu koma garin Jikamshi. To a Jikamshi saboda na fara girma sai karatuna ya koma a cikin gida wajen mahaifina. A wurin mahaifina na sauke kur’ani tare da koyon wasu abubuwan ibada, ma’ana, irin su wanka, alwala, salla da sauransu. Ban fara karatun littafi ba sai kusan a shekara ta 1983,wato shiga ta Islamiyya ta farko kenan a rayuwata.

Aminiya: To bayan kammala firamare sai aka nufi ina?

Malama Murjanatu: To bayan na gama firamare da kudurin ni da mahaifiyata muna fatan a ce na yi gaba, domin har jarabawa ta tafiya sakandare na yi na kuma ci har na samu makarantar Soba ta Zariya,to bisa wani hukunci na Allah sai zuwan bai samu ba. Ganin na girma, saboda na taso da jiki, kuma an san iyayenmu a lokacin ba su son su ga yarinya ta girma a gabansu, sai mahaifina ya yi mani aure ina ’yar shekara 11.   Na kuma fara haihuwa ina da shekaru 13 a duniya. Wannan dalili na aure ya sa batun karatun duka sassan biyu ya tsaya sai abin da aka samu aka cigaba da amfani da shi. Zaman aure na ci gaba har zuwa waccan shekara ta 1983 ban cigaba da karatu ba. Na kuma shiga waccan Islamiya wadda kuma ita ce ta farko a garin Katsina ana kiranta Abubakar Gumi. An kuma bude ta a nan cikin harabar ma’aikatar jin dadi da walwala da ke kofar Durbi a Unguwar filin Samji. Sheikh Yakubu Musa shi ne shugaban makarantar a lokacin. To na yi karatu na tsawon shekara daya da wani abu a cikinta. To amma saboda korafi da aka rika samu a wancan lokacin na ganin rashin dacewar maza na koyar da mata sai shi Malam Yakubu ya ce,za a tsinci wasu daga cikinmu masu kokari a tura su karo ilmi don koya wa matan amma in mazajensu sun yarda. Ban samu matsala da mijina ba,domin ya bar ni na kuma tafi can makarantar ATC a cikin shekara ta 1984 wadda ita ce a matsayin sakandare. Na kuma yi jarabawata ta shiga makarantar a ranar da na gama wankan ’ya ta ta uku.

Aminiya:  Me za ki iya tunawa a lokacin da kike dakin miji kafin samum waccan dama ta shiga Islamiya?

Malama Murjanatu:  To zama ne aka yi na matar aure a gidan mijinta. Sai dai ka san ba za a rasa samun yin wani abu na kuruciya ba, domin ina son karatu saboda haka sai na rika karatun littattafai haka nan, amma cikin sa’a har da na addinin na rika karantawa. Sai ma daga baya na gane wata rahama da Allah ne Ya nufe ni da ita don saboda a tsakanin 1980 zuwa 1982, lokacin an fiddo Tafsirin Marigayi Malam Abubakar Gumi na Hausa Hizib 4, to wannan littafi na daya daga cikin littafan da na ci gaba da karantawa har  ta kai tun daga Suratul Mulki har zuwa Nas na san fassararsu. A daya gefe kuma, baya ga hidimar gida sai kuma na shagaltu a kan yin kitso da dinki. Ba ni fa da keken dunkin amma nakan yanka da hannuna in kuma dinka da hannu kuma in ka ga ni ba ka cewa da hannu aka yi dinkin. Amma babu batun yin wata sana’a a cikin gida, wadancan abubuwa biyu da nake yi duk na raha ne. A batun zuwa ATC kuwa, ina jin mutum daya kawai zan iya tunawa cikin wadanda aka zabe mu zuwa can, watau Malama Karimatu ko kuma Karima Bala kamar yadda muke kiranta, Balan sunan mijinta ne. To babban kudurina a wannan lokacin shi ne,tunanin da aka saka mana na cewa mata s su yi karatu domin su karbi mazan, sannan kuma ga wancan ciwon na ban tafi karin karatu ba to sai suka kara mini karfi na in je in nemi ilmin. Amma kafin wancan tunani na Malam Yakubu, ni babban kudurina sh ine in ga na yi boko har na zama wani abu  acikinsa, amma wancan tunani na Malam sai ya canza mani nawa. Har ila yau, a can ATC maimakon in yi shekara 4 sai muka yi 6 domin ta kanmu aka fara yin shekara 6

Aminiya: Ke nan in na ce, babban kudurinki shi ne karantar da mata ban yi kuskure ba?

Malama Murjanatu: Tabbas ba ka yi laifi ba, domin babban kudurina shi ne in ga na karantar da mata da kananan yara. Kuma da farko na tafi ATC ba da nufin in bar Islamiyata ba amma sai na tarar abin ya wuce tunanina. Duk da kalubalen da na fara samu da farko amma na jure aka ci gaba da karatun da kuma hidimar gida. Inda kuma na kara gode wa Allah da ya hada ni da wata Malama wadda ta yi fice a batun Da’awah kuma ta yi tafiye-tafiye kasashen waje don neman ilmi watau Malama Lami Sabi’u Jibiya, ai kuwa ganin gamu a cikin aji daya tare da ita, ai shike nan sai na like mata. Kuma sau da yawa nakan gayawa mata cewa, sirri na karatun addinin musulunci ya kasance mutun ya san baki da wasali, watau ya iya karanta su tare da rubutawa.

Aminiya: Bayan gama ATC islamiyar kika dawo don koyarwa ko aiki aka nema?

Malama Murjanatu: To farko dai ina so ka tuna cewa karatu fa ba shi tafiya sai tare da kudi. Shi dai maigida ya bayar da duk damar da ake bukata, saboda haka, kayan dakina na rika kwasa ina sayarwa a boye. To na fara samun wani dan abu na daga karatun sanadiyar wata islamiya ta matasa da aka bude a unguwarmu na fara koyarwa. Daga nan kuma sai aka neme ni a can cikin Saulawa gidan Kadarko, shi kuma ina koyar da tsofaffi da mata. Na kusa shekara 17 ina koyarwa a nan. Kuma wani abinda zai baka mamaki shine,maza arba’in ke cikin ajinmu a ATC amma mu mata mu 3 ne kacal kuma cikin ikon Allah har na daya na sha dauka. Kuma a karshe dai na dauko babban sakamako.  

Aminiya:  Wadanne nasarori kika samu?

Malama Murjanatu:  Zamowa cikakkaiyar dalibar harshen Larabci da darussan addinin Musulunci.  Fahimtar Larbaci kamar yadda na fahimci harshen Hausa. Fahimtar tafsirin Alkur’ani Mai girma.  Sannan wata nasarar ita ce yadda na fara koyarwa a Makarantar Islamiyya tun daga shekarar 1985 kawo yanzu.  Sannan wata nasarar ita ce yadda na kafa makarabtar koyon darussan Larabci da na addinin Musulunci (Community College of Arabic and Islamic Studies) wacce aka fi sani da Makarantar Koyon Larabci.

Aminiya:  Wadanne kalubale kika fuskanta?

Malama Murjanatu: kalubalen da na fuskanta bai wuce yadda na yi karatu bayan na yi aure ba, saboda duk karatun da na yi, na yi shi ne bayan na yi aure. 

Aminiya:  Batun iyali fa?

Malama Murjanatu:  Yanzu haka ina tare da magidana Alhaji Ibrahim Duwan, sannan Allah Ya albarkace mu da ’ya’ya 11, amma daya daga ciki ya rasu, saboda hakan yanzu muna tare da 10.  Sannan ina da jikoki 27. 

Aminiya:  Mene ne burinki a rayuwa?

Malama Murjanatu: In ga wannan makaranta ta habaka kuma an bude rassanta a ciki da wajen Jihar Katsina.  Sannan burina in ga na ilimantar da mata da kananan yara don a samu al’umma tagari.