✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in inganta rayuwar marasa galihu – Hajiya Laraba Ahmed Kawu

Hajiya Laraba Ahmed Kawu, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ta share shekara 31 tana aiki, ta fara aiki ne a matsayin jami’ar labarai a Ma’aikatar…

Hajiya Laraba Ahmed Kawu, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ta share shekara 31 tana aiki, ta fara aiki ne a matsayin jami’ar labarai a Ma’aikatar Watsa Labarai a tsohuwar Jihar Bauchi, har ta kai Mataimakiyar Darakta a ma’aikatar.Bayan ta yi canjin wurin aiki sai ta zama Daraktar Mulki da Kudi a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA).Yanzu kuma Babbar Sakatariya ce a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe.

 

Tarihin rayuwata:

Sunana Hajiya Laraba Ahmed Kawu. Ni haifaffiyar garin Gombe ce.

Bafulatana ce gaba da baya kakannina uku ma dukansu Fulani ne. An haife ni a ranar 7 ga Nuwamban 1962.  A can  na yi kuruciyata har na kai lokacin shiga makaranta iyayena suka sa ni a makarantar firamare ta Jankai wadda yanzu ta koma makarantar firamare ta Jalo Waziri daga 1969 zuwa 1975.   Bayan nan sai na tafi Sakandaren  Gwamnati ta Billiri a Jihar Gombe a 1975 zuwa 1978, inda na yi aji uku. Daga nan na sake tafiya Sakandaren ’Yan mata ta Doma da ke garin Gombe a 1978 zuwa 1980. Bayan na kammala sakandare, sai na rubuta jarrabawar WAEC na samu tafiya Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato, a 1980 zuwa 1985 inda na samu digiri na farko a bangaren tarihi. Na sake tafiya Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi na yi babbar diploma (PGD) a  sha’anin mulki.

 

Aiki:

Na fara aiki ne a matsayin Jami’ar Watsa Labarai ta II a Ma’aikatar Watsa Labarai na tsohuwar Jihar Bauchi a 1987. Na yi aiki a ma’aikatar har tsawon shekara uku. A 1990 sai na yi canjin wajen aiki na koma Ma’aikatar Kananan Hukumomi a matsayin Sufeta mai kula da kananan hukumomi daga 1990 zuwa watan Yuli shekarar 2011, lokacin na samun karin girma na zama Mataimakiyar Darakta. A 2011 sai na koma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA), inda na zama Daraktar Kula da Sha’anin Mulki da Kudi (DAF).  Ina Hukumar SEMA a matsayin DAF sai na  zama Babbar Sakatariya, inda yanzu nake aiki a Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Jihar Gombe.

 

Kalubale:

Kalubale akwai shi, domin duk macen da take aiki a tsakanin maza tana tare da kalubale saboda yadda za ta rika cudanya da maza dole ne mace ta yi duk mai yiwuwa don ta ga ta kare kanta musammam ma mai aure. Domin dole sai wani ya furta miki maganar  da ba ta da dadin ji. Sannan al’ada irin tamu ta Hausawa da Fulani akwai matsala ta ganin cewa tunda maza aka fi sani da fita wajen aiki ke mace duk yadda za ki yi kokari na ganin kin yi kwazo sai wani ya nemi ya kwashe miki kafafu, ya nuna ya fi ki kwazo.

Uwa-uba kuma hada aikin gida da na ofis ba karamar matsala ba ce domin ba za ki so a ce aikinki na gida ya tsaya ba, haka na ofis, ga kuma tarbiyyar ’ya’ya, ka ga ashe dole sai mace ta yi taka-tsantsan don ganin kowane bangare ta ba shi kulawar da ya dace.

 

Nasarori:

Nasara alhamdulillahi, an samu nasara domin albarkacin wannan aiki da nake yi ya rufa mini asiri inda na samu na iya tarbiyyar ’ya’yana sannan na dauki nauyin wadansu ’yan uwa har na aurar da kannena 7 a dalilin wannan aiki. Na san jama’a musamman a aikina na ba da agaji a Hukumar SEMA inda duk inda aka samu wata annoba ina daga cikin masu shiga gida-gida muna daukar bayanan abin da ya faru sannan gwamnati ta ba da tallafi ta hannunmu, mu kuma mu raba wa jama’a.

Kungiyoyin da nake ciki:

Ina da kungiya ta mata mai suna Taufik Women Group muna koya wa mata sana’o’i.   Ina kuma da kungiya mai zaman kanta ta Ahmed Kawu Hearth For Children Initiatibe inda muke taimaka wa yara musamman almajirai wajen koya musu sana’o’i da kula da su ta wajen ganin mun kare lafiyarsu.

Kasashen da na ziyarta:

Na ziyarci kasashe da dama, daga ciki akwai Saudiyya da kuma Ruwanda.

Yawan iyali:

Alhamdulillahi Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya uku, maza biyu da mace daya, sannan ina da jikoki bakwai kuma dukansu sun yi karatu. Babban ya gama karatunsa na jami’a inda ya samu digiri na farko da na biyu yanzu kuma yana digiri na uku, ita kuwa ta biyu ita ma ta kammala karatunta na jami’a karamin kuma wato na uku yanzu haka yana karatu ne a sakandare.

Burina a rayuwa:

Burina a rayuwa shi ne idan na yi ritaya zan ci gaba da ayyukan da na faro a wannan kungiyar don kyautata rayuwar yara musamman almajiran makarantun Tsangaya da marayu ko wadanda iyayensu ba su da karfi don dogaro da kai da sauran al’amuran rayuwa, musamman makarantarsu da saya musu magani da kuma yadda za su rika tsaBtace jikinsu. Kuma muna iya yi musu aure idan suka girma sai ga shi kafin in yi ritaya Allah Ya ba ni iko na kafa tawa kungiyar ta Ahmed Kawu Hearth For Children Initiatibe wacce take kula da yaran. Muna hada kai da mutanen unguwa wajen ganin mun dauki nauyin taimaka wa wadannan almajirai muna saya musu ruwa don su rika yin wanki da wanka da kuma gudanar da al’amurran rayuwarsu na yau da kullum.

Musamman muna yin haka ne a duk ranar Alhamis da kuma ranar Juma’a don almajiran su rika kasancewa cikin tsabta.

Shawarata ga iyaye:

A matsayina na mace ina kira ga iyaye musamman mata su sa ’ya’yansu mata a makarantar boko don su samu ilimin zamani da zai taimake su wajen sanin ’yancinsu da kuma iya tarbiyyartar da ’ya’yansu yadda ya dace. Rashin ilimi ga ’ya mace akwai ciwo domin ko zaman gidan miji ba za ta iya shi yadda maigidanta zai ji dadin zama da ita ba, kuma idan ba za ta yi aikin gwamnati ba bayan ta yi karatun, ai ilimin zai taimake ta wajen tafiyar da sana’o’i irin na cikin gida cikin sauki.  Sannan ina kira ga iyaye su guji dora wa ’ya’yansu mata talla, don yin haka ke jefa yaran cikin gurbacewar tarbiyya da za a koma ana yin da-na-sani.