✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in kafa babban kamfanin takalma nan da shekara 5 – Khadija Ahmed Malumfashi

Khadija Ahmed Malumfashi matashiyar ’yan kasuwa ce da ta kafa masana’antar takalma. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara da kuma burinta nan…

Khadija Ahmed Malumfashi matashiyar ’yan kasuwa ce da ta kafa masana’antar takalma. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara da kuma burinta nan gaba:

 

Tarihina:

Sunana  Khadija Ahmed Malumfashi, an haife ni a garin Katsina amma na girma a Abuja ina zama da iyayena kusan shekara ashirin da uku yanzu.   An haife ni ranar 7 ga Augusta, 1995.

 

Ilimi:

Na yi firamare da sakandare a Abuja, sannan na yi karatun diploma a garin Bida inda na karanta fannin sadarwa, bayan shekara uku na sake komawa wata makarantar a Abuja inda na yi babbar diploma a fannin aikin sadarwa, daga baya na so in canja zuwa karanta fannin kasuwanci sai aka ce sai na yi wata tara, ni kuma sai na fasa na ci gaba da karanta fannin sadarwar saboda ba na so in bata lokaci ina so in gama da wuri.

 

Burina ina karama:

Lokacin da nake karama ina son  zama lauya, amma da na ji wani labari a kan lauyoyi dangane da yadda za su kasance in suka mutu saboda aikin lauya yana cike da kalubale, saboda yarinta sai na tsorata. Shi ne dalilin da ya sa na canja buri daga son zama lauya zuwa zama ’yar jarida mai watsa labarai a talabijin ko rediyo, a bangare daya kuma ina so in zama mai kudi kuma sananniya a cikin mutane, sai na yi tunanin cewa kasuwanci zai fi ba ni damar cimma wannan burin nawa, to sai na fara sayar da kayan amfanin yau da kullun kamar su omo yayin da a gida kuma iyayena suka goyi bayana a kan haka.

Bayan na kammala diploma, sai na yi tunanin fadada kasuwancina, ta yadda zan samu damar cimma burina, sannan ne na yi tunanin fara harkar takalma. Kuma takalman ina so su zama daban da sauran, domin ina so ya zama akwai sunana a jiki kamar yadda manyan kamfanoni suke yi. Shi ne sai na yi wa wani kawuna magana, saboda yana harkar takalman. Da na yi masa bayanin abin da nake so sai ya kara min karfin gwiwa cewa hakan mai yiyuwa ne sosai, Sai na fada wa mahaifiyata ita ma ta goyi bayan hakan. Ta ce za ta kai ni wurin kawun nawa domin ya koya min harkar sosai, Babana ya kawo kudi Naira dubu 50 ya ba ni lokacin da za mu je Kaduna wurin kawun nawa. To haka dai na fara harkar takalman. Da muka je, na dage ni fa sai an yi min takalma da sunana a jiki, saboda ina so ya zama designers shoes, sai suka tambaye ni wane suna za a sa? Na ce KAD.

Kalubalen rayuwa

Gaskiya ban samu wani kalubalen rayuwa ba, saboda na taso cikin gata da hutu, don haka na gode wa Allah, don a gaskiya ni yar gata ce, komai nake so in yi za a yi mini don Babana yana ji da ni,

 

Nasarorina:

Alhamdulillahi da wuya in nemi abu ban samu ba, kuma idan ban samu ba na san hakan ya fi mini alheri saboda ko a makaranta da na fara ban taba samun matsala ba. Da na fara kasuwanci komai na tafiya daidai, ban taba zaton zan kamo yanzu ba. Tunda na fara kasuwanci nan alhamdulillah, yana tafiya fiye da yadda nake zato, don haka ma na ji ya kamata in kara bude wani fanni na alabe (wallet) da bel na daurawa da takalma masu tsayi na mata da kuma agogon hannu. Saboda ina ganin harkar ta fara kankama bai kamata in tsaya wa abu daya ba.

Jama’a da dama suna amfana da kasuwancina kuma da dama sun koya daga gare ni. Hakan ya zama abin alfahari gare ni. Kuma duk wanda ya zo ba ma bari ya tafi sai ya iya sosai. Don haka abin alfahari ne a ce ka taimaki mutum ya koyi irin wannan  sana’a, wato ya zama ta dalina ya samu abin yi maimakon zaman banza ba aikin yi.Don haka ina matukar jin dadi da alfahari na kasancewa ta matashiyar ’yar kasuwa da ta fito daga Arewacin Najeriya

 

Dalilina na kafa masana’antar yin takalma

Ina so kasuwancina ya habaka ya zama na zama hamshaiyar ’yar kasuwa tun daga nan gida har zuwa kasashen waje in Allah Ya ba ni nasara. Shi ya sanya na gina masana’antar takalma inda nake sa ran zan rika turawa zuwa wasu kasashen da ke kusa da mu kamar Ghana da Togo da Nijar. Idan na ga na fara turawa zuwa na kusa sai in yi wajen su Masar da Moroko da Kenya da Tanzaniya da sauransu. Na san abu ne mai wuya amma na yarda da cewa Allah Ke yin komai,

Shi ya sa nake so in fara samun babban waje a garin Abuja wanda zan yi babban gini amma haka idan zan yi sai na nemo wadanda za mu hada jari da su ko kuma su saka jari a kamfanin mu hada mu yi saboda ina so in gina babban kamfani nan da zuwa shekara biyar masu zuwa ina sa ran zan gama ginin insha Allah.

 

Abin da nake son a tuna ni da shi:

Ina son a tuna da ni a matsayin mai neman na kanta kuma wacce take da kwazo tukuru.

 

Abu uku da na saka a gaba:

Ina son in zama wadda duniya za ta sani, ina so in zama mai kudin ’yan Arewa a mata, saboda idan ka duba a masu kudin Najeria babu wata ’yar Arewa. Don haka ina so in zama daya daga ciki Insha Allah. Kuma zan yi haka ne idan na samu na gina kamfanina mai girma sosai a nan Abuja

 

Shawarata ga mata:

Ina ba mata masu sha’awar shiga harkar kasuwanci shawara su dage su yi hakan. Su yi shiri mai kyau sannan su hada da addu’a insha Allahu za su kai ga gaci.

 

Shawarar mahaifiyata da ba zan mance ba

Ki rike mutuncinki, ki ji tsoron Allah, kuma kada ki yi ha’inci a duk abin da kike yi. Ki yi karatu, iya yadda za ki iya.

 

Mata na iya hada karatu da aure

Ban taba aure ba, balle in sani, amma gaskiya a ganina za su iya, a duniyar nan komai bai da wuya sai dai idan ba ka sa kanka ba. Domin ina ganin idan har tsofaffi za su iya komawa makaranta su yi karatu, to kuwa hakan ba zai yi wa matar aure wahala ba.

 

Iyalina:

Ba ni da iyali sai dai mahaifana da sauran ’yan uwana

 

Tufafin da na fi so

Jallabiya da atamfa. Saboda ita jallabiya, idan kasa za ta rufe maka duk jikinka, atamfa ma haka.

 

Mawakan da na fi so:

Ba ni da wani takamaiman mawaki da na fi so saboda ni ba damuwa na yi da waka ba.

Abincin da na fi so:

Dambu ko na shinkafa ko na masara

 

Yadda nake hutu:

 

Ina yin hutuna ne ta hanyar yin barci da kuma in zauna haka kawai.

 

Gudunmawar da nake bayarwa:

Gaskiya ba zan iya fada ba, saboda ko Allah ma Ya ce idan za ka yi kyauta da hannun dama kada ka bari hannun hagu ya sani, idan na yi abu na yi don Allah ba sai wani ya sa ni ba.