Da Dumi Dumi

Burina in kafa makarantar koyar da ilimi da sana’a ga mata marasa galihu – Farfesa Bilkisu Aminu Shinkafi

Farfesa Bilkisu Aminu Shinkafi wacce ake kira Balaraba, ita ce Farfesa mace ta farko a Jihar Zamfara.  Aminiya ta tattauna da ita kan tarihin rayuwarta da gwagwarmayarta da burinta na rayuwa da sauran abubuwan da suka shafe ta.

 

Tarihinta:

Balkisu Aminu Shinkafi ’ya ga Malam Aminu Usman da Hajiya Asma’u Muhammad wadda ita kam har yanzu da rayuwarta. An haife ni ne a Jihar Kaduna a UnguwarTudun Wada a ranar 24 ga watan Fabrairu 1971.  Na yi firamare a unguwar Tudun Wada Kaduna sannan na yi karamar sakandare  a WATC Gusau.   Na gama a shekarar 1985.   Mu muka fara bude makarantar bisa tsarin karatu na 6.3.3.4.   Bayan na ci jarrabawar Kimiya ne aka mayar da ni Kwalejin ’yan mata mata ta Sakkwato (GGC), a lokacin Sakkwato da Zamfara suna hade, mun kare a 1988 daga nan na samu damar shiga Jami’ar Sakkwato (Usman danfodiyo Unibersity) aka ba ni fannin karatun Zoology (Nazarin dabbobin daji) na gama a 1992. Daga nan na koma gida Zariya na fara aiki a Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Nuhu Bamalli a 1996 sai kuma na samu aikin malanta da Jami’ar danfodiyo (graduate assistant) ina makarantar har zuwa shekarar 2015 sai na koma Jami’ar Tarayya ta Gusau. A can na yi digirina na biyu da na uku  na zama babbar Malama (Senior lecturer) kuma na zama reader, amma Jami’ar Zamfara ce ta ba ni Farfesa kuma ni ce shugabar Tsangayar Kimiyya har zuwa yau. A cikin wannan tafiyar na yi aure da Abdullahi Muhammad Shinkafi mun haifi yara biyar maza biyu mata uku.

ADVERTISEMENT

 

kalubale:

Ni ban fuskanci wani kalubale na karatu ba na rayuwa ba  duk da Allah bai hada ni da wata doguwar jarabawa ta abu ya fi karfinka ka shiga halin ha’u’la’i amma dai a cikin harkar ilmi na tashi gidan da ake karatu mahaifina malami ne a koyaushe yana son ya ga ‘ya’yansa sun yi ilmi, ni ce ta biyu a gidanmu ko kudin karshe ne a wurin babanmu zai tura ni makarata da su.   Na yi aure na fada hannun mijina mai son karatu, gaskiya su ne suka hana ni shiga kalubale, yawanci ana fuskantar cikas na abokiyar zama, ko shi ban hadu da shi ba ina zaman lafiya da abokiyar zamana na gode wa Allah ban hadu da wani abu da ya shiga gabana ya gagare ni ba.

 

Burinta na rayuwa ya cika:

Alhamduliliah gaskiya burina ya cika sai dai buri ba ya karewa, Allah Ya hada ni da miji nagari da abokiyar zama ta gari ‘yan uwana ba wanda nake kuka da shi.   A cikin mata miliyan kaza a ce kai kadai ke rike da wani mukami kuma ba don iyawarka da karfinka da isarka ba don ganin damar Allah to burina ya cika.   Ba kishi, ba yunwa, ba talauci amma in an ce abin da kake hasashe ya tabbata ta wannan ba buri ba ne ina da shi.

 

Burinki na kuruciya:

Shi ma na same shi in Allah Ya ja kwanana na kara, ina da abin da nake son na cimma kafin na mutu na bar wani abin da bayan raina da shekara 100 ana nuna shi da cewa na Bilkisu ne al’umma ta karu da ni, wato na yi wani abu da ya shafi rayuwarsu suke amfana da shi, yanzu na fara amma ban yi nisa cikinsa ba.

 

Abin da take son a rika tunata da shi:

Kamar yadda na fada a ce alummata ta amfana da ni, na zaburar da ita su yi la’akari da kansu su nemi ilmi don su daukaka jama’arsu, su tarbiyantar da ’yayansu a samu haka ta sanadin aikina, gidan ma’aurata ya gyaru maza su sani kan shawarwari na ne ga mata hakan ya gyaru, ina son kafin Allah Ya dauke ni na kafa tare da gina wata makaranta ta koyar da masana’antu ga mata marasa galihu su samu ilmi da sana’a, ina fatan da hannuna zan kafata ba bayan raina za a yi ba.

 

Tarbiyyar mata matasa a yau:

Gaskiya ban gamsu ba, duk mai idon gani ya san akwai kalubale da yawa a tarbiyyar, wannan ya taso ne tun daga aure su waye ke aure su samu ‘ya’ya.   Mai gidana yake cewa ku daina ganin laifin yaran zamani ku ga laifin uwayen zamani mu ne muka bata tarbiyyar don mu ne ke barin ‘ya’yan suna yin abin da suke yi yanzu.   Lalacewar ta faro ne tun daga iyaye a wurin aure da ake yi da son rai ba a samu abokin tafiya mai akida mai kyau ba, auren kwadayi ya fi yawa.   In ana son cin nasara sai an hada auren kirki na taimakon juna, a sani ba zama ne na kece raini ba, barin wannan asali ya sanya ‘ya’yan zamani suka shigo cikin kalubale, harkar yanar gizo ta shhiga cikinmu ta yi mana illa a tarbiyya, duk wayon iyaye ana yi masu wayo amma in ka tashi tsaye Allah Zai taimake ka, son rai da ciyar da ’ya’ya haramun yana cikin abin da ke kawo kalubale bayan zuwansu duniya.

 

Game da zuwan ’ya’ya mata makaranta:

An samu kari daga inda aka fito amma zuwansu makaranta daban, amfani da ilmin daban.  Kadan ne amma kowa a jajirce yake ga wahalar samunsa ana ganewa yanzu ga ilmi da sauki amma kudin sun ki biyan kudin sabulu. Abin da muka sani wanda ya gama sakandare yana iya rubuta takarda da turanci to yau dan jami’a ko kyakkyawar gaisuwa baya iyawa, ilmi a yi gaba a yi baya ne, ya karu a yawa amma an debe masa albarka.  Mata da yawa sun shiga babu tarbiyya, ilmi da tarbiyya ‘yan tagwaye ne, babu ilmi matukar ba tarbiyya, ko dabi’a ce ta dan adam ta canja ya haifar da ragwanci ya hana su samu ilmi ya yi tasiri a rayuwarsu musamman mata, neman satifiket  don a samu kudi na ke ce raini yana kara kashe ilmi.   Sai ka ga mutum da satifiket amma ba ilmin, wannan masifa ce gare mu mu malaman jami’a, don haka dole uwaye su canja alakarsu ana son a yi ilmi ne a gyara zaman al’umma yadda za a yi zama mata da miji ya za a yi tarbiyya tsakanin mutane.   Ko karamin abu na koya wa yaro nagode.   An daina wanda hakan ya cire tasirin da yaro yake da shi na girmama na gaba da shi.   Koyar da yaro tahazibi an daina kan haka yaro mai girmama kowa sai mai kudi.   A yanzu an samu cigaban mai hakar rijiya.

 

Abin da take yi lokacin da ta samu hutu:

Ina da durowa mai cike da dimbin littafai da nake yin nazari a lokacin hutawa.   Ina da wasu littafai da ban gama ba. Wayata ma wurin bincike na ce ina zama da yara mu yi hira ta shiriyar da su da shiga wurin girki da yin abubuwa tsakanin mutum da Allah su ne abin da muke yi.

 

Mata masu son su zama yadda kike wane mataki za su bi?

Wani abin in ka ga Allah Ya yi wa mutum shi ganin damar Allah ne, ban san yadda aka yi na zo wannan matsayi ba, amma kila da zato na babban abin da zai taimakawa mutum ya zo wannan matsayi iyaye su dage su bai wa ‘ya’yansu tarbiyya da ilmi, a daina cire yara daga makaranta ana yi masu aure kuskure ne hakan kuma shi ke mayar da ilmi baya.  Ko a cire yarinya makaranta ba ta gama karatu ba a yi mata aure.  Idan mace tana son ta yi karatu fa sai ta auri mai ilmi.   Ba zai yiwu wanda bai da ilmi ya bari ki yi digiri na biyu ba.   Ina ba mata shawara kwarya ta bi kwarya. Su auna maza da za su bar su su yi ilmi don mai abu ne ya san girmansa, kuma mata ku yi kyakkyawan zama na aure don wani na son matarsa ta yi karatu amma dabi’arta ke daga masa hankali komi ilminsa sai ya fasa.   Wata kuwa rashin girmama mijin zai sa ya yi tunanin in ko ta karo karatu fiye da hakan kenan za ta yi wanda tarbiyyar gidansu ce ta dauko ba ilmi ba ne.   Mata kuma su sani jan aiki ne hada aure da karatu ga uwa.   daliba a lokaci daya sai an jajirce, sannan a roki maza su ba mata goyon baya su yi karatu don in ba kwanciyar hankali da kyar mata su yi karatu. Ni ban san iyakar gudunmuwar da mijina ya ba ni ta karatu ba.   Sai da tallafin miji mace ke ilmi har ta iya taka matakin da nake kai.

 

kasashen da ta ziyarta:

Indiya da Saudi Arebiya da Dubai da Nijar.  Daga cikin kasashen da nake son zuwa shi ne Holand.

 

Abin da ya yi maki tsaye a rai:

Kome ne ne ya yi mini tsaye zai wuce a matsayina na musulma, amma rasuwar mahaifina ta tsaya mini a rai duk kwana biyu sai na yi maganarsa.   Na samu ilmi gare shi a komi na rayuwata sai an gan shi a ciki kan abin da ya fada mini mutuwarsa ta dauki hankalina don ta kai tsaye ce sai zama na Farfesa na yi farin ciki duk da na san komai mai zuwa da wucewa ne kuma akwai mai tafiyar da su.

 

Kungiyoyin da take ciki:

Ina cikin kungiyoyin addini na mata  irin su MSS da FOMWAN da MSO da Da’awa IMWAN.   A Jami’a kuwa ina cikin kungiyoyin Kimiyya da ilmin kiwon kifi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya