✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in  kawar da jahilci a tsakanin jama’a – Dokta Fatsuma Dada Mohammed

Dokta Fatsuma Dada Muhammad, ita ce Mataimakiyar Magatakardar Jami’a Jihar Yobe, tsohuwar malamar makaranta ce da ta kware a bangaren koyarwa, inda saboda kwazonta ta…

Dokta Fatsuma Dada Muhammad, ita ce Mataimakiyar Magatakardar Jami’a Jihar Yobe, tsohuwar malamar makaranta ce da ta kware a bangaren koyarwa, inda saboda kwazonta ta kai matsayin da take a yanzu. A zantawar da ta yi da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da ayyukanta da ma wasu bangarori da suka shafe ta:

Tarihin rayuwata

Sunana Dokta Fatsuma Dada Mohammed, Ni ’yar asalin garin Potiskum ne a Jihar Yobe kuma ’yar kabilar Bolewa, a nan aka haife ni na girma aka sani  a Makarantar Firamare ta Kara (Kara Primary School), Potiskum da na kammala na shiga Kwalejin’ Yan mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke garin Owerri na samu takardar shaidar WAEC. Ina gamawa na shiga Jami’ar  Bayero ta Kano  na yi digiri na farko kan ilimi (B.A Edu.), a1984.  Sai na tafi hidimar kasa a Jihar Binuwai na gama a 1985, daga bisani na sake komawa Jami’ar Maiduguri, na yi digiri na biyu kan ilimi (M. Ed.) a bangaren mulki da tsare-tsare (Administration and Planning) a 1992, na yi digiri na uku (Phd) a bangaren mulki da tsare-tsare a Jami’ar Bakht Al Ruda a kasar Sudan.

Aiki

Bayan kammala NYSC an dauke ni aikin koyarwa aka tura ni Sakandaren Al’umma da ke garin Biu a Jihar Borno (Community Secondary School), Biu, don a lokacin ba a kirkiro da Jihar Yobe ba, daga nan na zagaya makarantun sakandare da dama a matsayin malamar harshen Ingilishi.  Da aka kirkiro  Jihar Yobe sai aka tura ni na zama Shugabar Makarantar Sakandaren ’Yan mata (GGSS) Nguru a 1992, na zagaya makarantu da yawa a matsayin shugabar makaranta, kamar GGSS Ngelzarma da GGSTC Potiskum inda na yi shekara 14 ina matsayin shugabar makarantar sakandare har zuwa shekarar 2006.

Daga nan likkafa ta yi gaba aka mayar da ni hedkwatar Ma’aikatar Ilimi da ke Damaturu a matsayin Mataimakiyar Darakta mai kula da Harkokin Makarantu, daga nan aka kirkiro da Jami’ar Jihar Yobe, wacce da farko ake kiranta Bukar Abba Ibrahim Unibersity kafin a canja mata suna, aka dauke ni aiki a wajen a matsayin Babbar Mataimakiyar Magatakarda wato Principal Assistant Registrar a shekarar 2008 aka kara min girma zuwa Mataimakiyar Magatakarda wato Deputy Registrar inda na zama ni ce Mataimakiyar Magatakarda ta farko a jami’ar.

Kalubale

Da yake yawancin aikin da na yi a matsayin Shugabar Makarantar ’Yan mata zalla ne kuma na kwana da muke tare da yaran na sa’oi 24 a kullum, kiwon yara ba abu ne mai sauki ba. Kuma a wannan matsayi ba wai ilimi kawai muke ba su ba, har da tarbiyyarsu muke kula da ita da tsabtarsu da ci da shansu ga kuma tafiyar da harkokin malamai da sauransu. To aiki ne mai cike da kalubale sosai don kullum ana kan aiki ne kawai amma duk da haka gaskiya alhamdulillahi na gama lafiya.

Nasara

A duk tsawon shekarun da na yi ina aiki a makarantu ba a taba yi min wani bore ba kuma ba wata mutuwar yara ko wani hadari. Na samu hadin kan dalibai da ma’aikatana har ma ina da takardar yabo guda uku daga Ma’aikatar Ilimi, kuma har yanzu akwai kauna da zumunci mai yawa daga tsofaffin dalibai da ma’aikatana har yau ina cin moriyar mu’amalarmu.

Burina a rayuwa

Burina a rayuwa shi ne in yada ilimi in kuma ba da gudunmawa wajen  kawar da jahilci don ilimi shi ne ya bambanta mutum da dabba kuma gishiri ne na zaman duniya.

Hutu

Duk hutuna ba ya wuce cikin Jihar Yobe tsakanin Damaturu da Potiskum ba na zuwa ko’ina don yin hutu.

Yawan iyali

Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya shida kuma a yanzu biyar suna raye, hudu maza, daya mace, kuma ina tare da mahaifnsu, sannan Ina kuma da ’ya’yan ’yan uwa wato wadanda kamar ni na haife su.

Kasashen da na je

Na je Saudiyya aikin Hajji kuma na je Indiya na halarci wani taro na kasashen duniya, na je Jamhuriyar Benin ta hanyar aiki kuma na je Sudan karatun digiri na uku.

Kungiyoyi

Ni ce Shugabar Kungiyar Ci gaban Mata ta President Natibe Women Adbancement, inda muke tallafa wa mata da marayu. Kuma ina Jami’ar Gudanarwa a Shirin Initiatibe for the Needy, Orphans Less Pribilege and Widows (INOL) kuma mai tsara bincike (Research Coordinator) ta Kungiyar NCWS. Kuma ni mamba ce a Open Gobernment Partnership (OGP), ta Yobe da sauransu. Wadannan duka kungiyoyi ne masu zaman kansu ko kungiyoyin sa kai don ci gaban al’umma da kuma ayyukan jinkai.

Tufafi

Na fi amfani da atamfofi namu na kasar Hausa don laushi da saukin sarrafawa domin ka san kasarmu akwai zafi.

Abinci

Na fi son tuwo da miyar kuka, ko agushi ko ogbono.

Shawara

Gaskiya mata su yi kokarin samun ilimi na zamani da na addini. Ilimi shi yake sa komai na rayuwa ya zo da sauki jahilci cuta ce babba don haka nake bai wa iyaye shawara su mayar da hankali  kan karatun ’ya’ya mata kada a fifita kararun namiji a kan mace. Sannan iyaye su sani talla da ake dora wa ’ya’ya mata ba ta dace ba, domin talla jami’a ce ta lalacewar yara mata.