✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Burina in kera jirgin sama’

  Tun yana karami matashi Isma’ila Surajo da ya fada cikin mawuyacin halin sai ya ya amfani da kwali a matsayin takalmi domin ya kare…

 

n Sirajo a na’urar yin shuka da ya qirqiroTun yana karami matashi Isma’ila Surajo da ya fada cikin mawuyacin halin sai ya ya amfani da kwali a matsayin takalmi domin ya kare kafaufuwansa a yayin da yake tafiya a hanyarsa ta zuwa gona.

Haka kuma bukatar kare fuskarsa daga rana ta tilasta shi yin hular raga, daga nan kuma sai ya yi karanan motoci da jiragen kasa da injunan nika, duk da kwalin.
Aminiya ta gano cewa, tun da ya shiga makarantar sakandare Surajo ya fara amfani da kwanon rufi wajen kera kananan motoci, kamar motar kashe gobara da kuma motocin noma.
‘’Duk abin da na gani na kan so in yi irinsa, mun tafi wata gasa sai na ga wadansu sun yi babur suna hawa, sai ni kuma na ce zan yi injin shuka wanda mutum zai hau ya yi aiki, saboda ina gani a kasarmu ba mu da injin shuka, manomanmu kuma suna wahala. Sai na dauki karfe da kwanon rufi na fara yin karami inji wanda karamin yaro zai iya shiga. Sai kuma na yi babba, inda na yi amfani da tayoyin baro da karfen gado da giyabus din babur.’’ Inji Surajo.
Surajo, wanda ya tashi a wurin kakansa na wurin uwa, ya kuma yi karamin jirgin ruwa ta hanyar amfani da kwanon rufi da injin rediyo, wanda ya sanya yake motsawa gaba ko baya idan aka sanya masa batira, ya ce idan ya samu cikakken horo da kayan aiki zai yi wanda ya fi shi.
Haka kuma Surajo ya yi injin janareta da ke aiki da batir da ruwa, ya kuma nuna yadda ake amfani da janaretan a kuma yi cajin wayar hannu da ita, kuma ya yi fanka mai tsayuwa. Sai dai ya ce wutar da janeratat ke samarwa ba ta da karfin da za ta iya jan mutum.
A cewarsa, yana kuma da hanyoyin da za a magance matsalar magudin zabe a kasar nan. Na’urar da za a yi amfani da ita da ya kirkiro ta yi kama da na’urar kwamfuta ta kan cinya, wanda ya kira ‘’ tsarin zabe ta hanyar na’urar lantarki’’. Ya nuna wa wakilinmu yadda ake yin zabe ta hanyar amfani da wani abu da ya yi kama na’urar lissafi.
Da yake kauyensu Rubochi da ke yankin karamar hukumar Kwali a Abuja yana kewaye da kamfanonin gine-gine ne, Surajo ya kuma yi gireda mai kwasar kasa da ke amfani da batira.
Surajo dai ya ce yana so ya zama injiniya ne domin harkar kere-kere ta bunkasa a kasar nan, ‘’muna bukatar bunkasar harkar kere-kere,’’ inji shi.
Wannan yaron dai ya ce yana son ya ci gaba da karatunsa na babban sakandare a kwalejin koyon sana’a ne domin ya samu damar yin babban injin noman da mutane za su iya shiga su yi aiki da shi. ‘’’A lokacin da muka je kasar Birazil muka baje kolin kere-kerenmu, a cikin mu 22 da muka tafi daga Najeriya nawa ne ya fi burgewa.’’
Malam Isa shi ne kakan Surajo, ya bayyana farin cikinsa game da bajintar da jikan nasa yake nunawa, inda ya ce a kowane lokaci yana taimaka masa da kudi domin ya sayo kayan aikin da yake bukata.