✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in koya wa mata da marayu sarrafa sarka da jaka – Zainab Zubairu

Malama Zainab Zubairu wata matashiyar matar aure ce da ke sana’ar yin kayayyakin ado na mata da suka hada da sarkoki da jakunkuna da takalma…

Malama Zainab Zubairu wata matashiyar matar aure ce da ke sana’ar yin kayayyakin ado na mata da suka hada da sarkoki da jakunkuna da takalma da sauransu da ke zaune a cikin garin Kafanchan a Jihar Kadunaa. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana irin alherin da ke cikin sana’ar da kuma burinta na son taimaka wa marayu da mata.

 

Ki fara da gabatar mana da kanki.

Suna na Zainab Zubairu, shekaruna talatin ni matar aure ce da ke zaune a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a yankin Kudancin Jihar Kaduna.

Ki gabatar da sana’arki?

Ina sana’ar yin kayayyakin kwalliyar mata da suka hada da jakunkunan mata manya da kanana sai takalman mata da sarkoki da ‘yan kunne iri-iri da kuma yin ado a dinkunan mata da salo dabam-dabam.

Tun wane lokaci fara wannan sana’ar?

Shekarata tara zuwa goma ke nan ina wannan sana’ar amma sai daga baya ne jama’a su ka fara fahimta saboda karancin jari.

Yadda aka yi na koya kuma watarana ne na je rakiyar wata ‘yar uwata a wata makaranta ta Federal Technical College da ke Malali a Kaduna, sai na ga yadda ake koyawa mutane shi ne abin ya ban sha’awa na zauna ina ta kallo daga nesa, to bayan sun gama sai suka daga wata sarka suka tambaye su wa zai yi irinsa sai na daga hannu na ce ni zan yi sai suna ta mamaki ga wata bakuwa daga zuwanta ranar farko ta ce ita za ta yi shike nan kuwa sai suka bani kayan aiki nan take kuwa na dukufa hadawa abin har ya basu mamaki suka nemi da in dawo washegari amma ban samu komawa ba na dawo Kafanchan. To bayan dawowata da yake abin ya shiga raina sai na fara gwadawa a haka nake ta samun basira daga aikin rana daya kawai. Da haka na fara har zuwa yanzu.

Ko yaya ki ke ji a matsayin ki na matar aure da ta riki irin wannan sana’ar?

Gaskiya ina jin dadin wannan sana’ar domin sana’a ce da kina zaune a cikin gida za ki rika yinsa mutane na zuwa suna yin sari. Masu bukukuwa da masu kwalliyar daki da teloli da masu sayarwa da kuma masu sayen daidai don amfanin kansu. Idan mace ta natsu a gida za ta ci gajiyarsu wannan sana’ar domin gaskiya akwai rufin asiri a cikinsa.

Yaya kike wajen sayar da kayayyakin da ki ke yi?

To ina sayar da dai-dai kuma ina sayarwa masu sari kamar yadda na fada maka. Akwai sarka da ‘yan kunnensa da nake sayarwa a kan naira dubu daya zuwa dubu 2 ko da dari 5, ya danganta da irin yanayin aikin da aka yi masa. Takalma kuma akwai daga dubu 1 da dari 5 zuwa da dari takwas. Akwai babban jaka na mata da nake sayarwa naira dubu biyar da kuma kanana da nake sayarwa naira dubu daya da dari biyar haka duka a farshin daidai na fada maka.

Ya kan dauke ki kamar tsawon wanne lokaci domin hada kayayyakin?

To ya danganta da irin lokacin da zan zauna musu ne. Misali na kan yi kwana uku zuwa hudu in hada babbar jaka, karami kuwa a yini guda na gama hadawa. Kamar takalma kuma a rana daya zan iya yin dozin daya wato guda goma sha biyu (sawu shida ke nan) shi kuma sarka ya danganta da irin wahalarsa ne don iri-iri ne akwai wanda ya kan dauke ni kwana daya akwai kuna wadanda zan iya hada ko da guda goma ne a rana guda. Na kan je na saro ‘ya’yan ne na zo na zauna na fitar da duk irin zayyanar da nake so.

Ya zuwa yanzu kamar mutum nawa ki ka koyawa wannan sana’ar?

Akalla za su kai mutum goma zuwa sha biyar saboda mutane ba su fahimta ba sai daga baya inda wasu ke turo matansu ko ‘ya’yansu.

Wanne kira kike da shi ga ‘yan uwanki mata kan tashi tsaye wajen kama sana’a?

Kira na ga ‘yan uwa mata shi ne su tashi su kama sana’a ko wace iri ce na halas don rufawa kansu asiri domin sana’ar hannu yana da dadi da kuma amfani. Kuma shi sana’a ka da kice sai kin rasa wani abu ne tukuna za ki nemi sana’a, ko da ace mijinki na da hali kuma ya dauke miki komai da komai ki dai kama sana’a saboda karin rufin asiri kan ki da na ‘ya’yanki.

Wanne irin alheri ki ka samu a sanadiyyar wannan sana’ar?

Gaskiya na samu alherai masu yawa don daga ciki ba zan manta da wani lokaci da aka kira mu zuwa Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi don koyawa mata da ‘yan mata irin wadannan sana’o’in wacce wata kungiya mai zaman kanta ta dauki nauyin gudanarwa kuma gaskiya mun samu alheri sosai. Bayan nan sun sake gayyatata Kaduna inda muka sake koyarwa da wasu matan.

Ko menene burinki a wannan sana’ar?

Burina shi ne in ga harkokin nan sun bunkasa ta yadda zai zama wani babban kamfani. Kuma har ila yau ina da burin bude wajen koyar da wannan sana’ar ta yadda mata manya da kanana musamman marayu da marasa galihu. Don haka ina kira ga gwamnatoci da kungiyoyi da kuma ‘yan kasuwa da su sanya min hannu domin fadada wannan harkar don zai taimaka wajen koyawa mata sana’a wanda zai rage rashin aikin yi a tsakanin mayan aure da zawarawa da kuma ‘yan mata. Kamar marayu mata ma burina shine in koyar da su kyauta.

A karshe wane kira kike da shi ga gwamnati?

Kirana ga gwamnati shi ne ta sanya min hannu ta hanyar ba da tallafi da kuma bude min wajen koyar da wannan sana’ar da kuma jari sannan kuma ta rika taimakawa wajen fitar da irin kayayyakin da nake yi zuwa wasu wurare don fadada kasuwancina.