Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Burina in taimaki mata da matasa – Hajiya Fatima Umar Kakenna

Hajiya Fatima Umar Kakenna
Hajiya Fatima Umar Kakenna

Hajiya Fatima Umar Kakenna, ’yar gwagwarmaya ce da ta taka rawar gani a Karamar Hukumar Geidam a Jihar Yobe.   Ta rike mukamai daban-daban. Ta taba zama zababbiyar Kansila a karamar hukumar Geidam, kuma yanzu haka ita ce Babbar Manaja ta Kamfanin sufurin  motocin gwamnatin na Jihar Yobe (Yobe Line). A hirar ta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwar ta da kuma wasu bangarori da dama kamar haka:

Tarihinta:

ADVERTISEMENT

Sunana Hajiya Fatima Umar Kakenna.  Ni ’yar asalin Karamar Hukumar Geidam ne da ke Jihar Yobe.  An haife ni ne a ranar 20 ga watan Afirilu 1969.   A can na girma har aka sa ni a firamare ta Kafela a tsakanin 1977  zuwa 1983.   Bayan na gama sai na samu tafiya

sakandaren ’yan mata ta gwamnati,  Women Teachers Collage WTC Gaidam a 1983 zuwa 1985.   Bayan na yi aji uku na karamar sakandare sai na tafi Gobernment Girls Secondary School Nguru (GGSS) Nguru daga 1985 zuwa 1988.  Ina kammalawa sai na wuce Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ramat Polytechnic da ke garin Maiduguri a tsakanin shekarun 1988 zuwa 1989 inda na yi satifiket a bangaren kula da harkar Otel wato Hotel

ADVERTISEMENT

Management.   Daga nan sai na sake komawa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Damaturu a tsakanin 2000 zuwa 2002 na yi difloma  a bangaren mulki da kasuwanci wato Business Administration.   Har ila yau a 2003 zuwa 2005 na sake komawa na yi Babbar Difloma (HND).   Sannan a 2008 zuwa 2009 na yi PGD duk a wannan fanni.   Yanzu haka ina aji hudu a Jami’ar Maiduguri a wannan fanni na Business  Administration.

 

Aiki:

Na fara aiki ne a 1990 a Karamar Hukumar Gaidam a bangaren mulki a matsayin mai kula da dafa abinci wato Caterer, sannan a shekarar ce na zama Sakatariya ta Better For Rural Women In Agric.  A 1992 na zama Shugabar Mata masu harkar Noma na Karamar Hukumar Geidam wato Chairperson Women in Agric.   Na sake zama Sakatariya ta Youth Caucus  duk a wannan shekara (1992). A 1993 sai na zama Shugabar wani kwamiti na shiyya a Geidam,  Chairperson Geidam District Committee.  A a wannan shekarar aka mayar da ni wani sashe na shiyyar Arewa Maso Gabas da ake kira North East Arizon Debelopment Program.   A 1998 na zama shugabar shirin tallafawa iyalai wato Chairperson Family Support Program.    A 2002 na zama memba ta maat masu koyon sana’o’i wato Women entrepreneur.  A 2003 aka zabe ni Sakatariyar kudi ta mata ’yan siyasa na Jihar Yobe (Financial Secretary Women In Politics).   Sannan a ranar 4 ga watan Afirilun 2006 na zama Kansila a Karamar Hukumar Geidam. A 2007 aka sake ba ni shugabar mata ta SAY YES  ta Jihar Yobe. Sannan a 2009 aka ba ni wani mukamin memba a yankin Yobe ta Arewa a sashin kula da Ilimi wato Member Yobe North Constituency on Eduction.   Bayan nan a 2011 aka sauke mu daga shugabancin kungiyar SAY YES ta jihar Yobe aka mayar da ita Women SAY YES For Brah-Brah inda aka sake ba ni shugabanci.  Ina rike da wannan  shugabanci har 2015.   A 2018 aka canja mata suna zuwa All Women Campaign Organization, sannan a 2009 aka ba ni mukamin Babbar Janaral Manaja a kamfanin sufurin motocin jihar Yobe wato Yobe Line.

Kwasa-kwasai:

Na je kwas sau biyu a Ilorin ta Jihar Kwara kan yadda za a taimakawa mata a bangaren aikin gona.

 

Lambobin yabo:

Na samu lambar yabo ta Women Debelopment in Africa a 2004.  Sannan a lokaci na da nake Janaral Manaja na Yobe Line na sama wa Yobe Line lambar Yabo ta Kamfanin Sufurin da ya fi yin fice a shiyar Arewa Maso

Gabas (Best Transport Company Award in North East 2010)

 

Kalubale:

A shekarar 1990 da na fara aiki na fuskanci matsala kasancewa ta mace ’yar siyasa kuma budurwa da ba ta da aure a lokacin.   Maza sun sa ni a gaba kuma a lokacin  albashina Naira dari uku ne.

Allah Ya taimake ni aka tura ni North East Arizon Debelopment Program sai albashina ya koma dubu goma. Daga irin wannan kalubale da na fuskanta sai ya zame mini ci gaba da samun daukaka har yanzu na zama   Janar Manaja (GM) ta Yobe Line.

 

Nasarori:

Gaskiya na samu nasarori domin daga lokacin da na tafi North East Arizon Debelopment Program ina wajen aka ba ni mataimakiyar jami’ar ci gaban yanki wato Assistant Area Debelopment 6 da kuma Kodinetan wannan shiri. A lokacin ne muke bi gida- gida muna raba wa mata tallafi, da yake shiri ne na turawa (UN Women) da haka ne na samu ci gaban da har ta kai aka nemi na shiga harkokin siyasa, inda har na zama Kansila ta dalilin haka.

 

Burina:

Ba ni da burin da ya wuce na zama gogaggiyar ’yar   siyasa sosai domin in taimaki al’ummata wato mata da matasa, saboda yanzu duniyar matasa muke ciki, komai sai da matasa ake yi.   Ta dalilin siyas  ne kuma zan taimakawa mata su samu ilimin zamani da zai taimake su zaman rayuwa.  Sannan ina da burin yin siyasa har karshen rayuwata.

 

Hutu:

A lokacin hutu na ba na zuwa ko’ina, tun ban yi aure ba saboda babana almajiri ne, bai barin mu kara zube.   Ina hutu ne a gidan mu gaban iyayena.   Har na yi aure tare da iyalai na nake hutu, ba na zuwa ko’ina.

 

Tufafi:

Zani da Riga nake daurawa da Lufaya wanda za su rufe mini jiki kasancewa ta

 

Musulma ’yar Malamai kuma ’yar Arewa cikakkiya wacce kowa ya ganni zai ce ya ga mai kamala da sutura ta kirki a jikin ta.

 

Kungiya/kasashe:

Ba na kowacce irin kungiya amma ina sha’awar nan gaba in kafa kungiya ta mai zaman kanta wacce zan rika taimakawa mata ta hanyar koya musu sana’a’o’i da yadda za su rika dogaro da kansu musamman  gwauraye da marasa galihu irin matan ’yan gudun hijirar nan da sauran su.

Kasashe kam na je Saudiyya da Ethopia da Cyprus  da Turkiyya da Dubai da Misira da Sudan da Kotono da Ghana da kuma Nijar.

 

Yawan Iyali:

Alhamdulillahi, Allah Ya albarka ce ni da ’ya’ya biyu duk maza.   Daya yana karatun  Jami’a a Cyprus karamin yana aji uku na karamar Sakandare a Jihar Yobe.

 

Shawara ga iyaye:

Kira na ga iyaye su rika barin ’ya’yansu musamman mata suna yin karatu, walau na zamani da kuma na addini, don hakan zai taimaka musu a rayuwa.

Bayan ilimin addini da aka san kowanne dan musulmi yana yi kada a ce sai da namiji ne kawai za a bari ya yi karatu, su ma matan karatun su yana da matukar alfanu saboda su ne ke rike da kaso mafi yawa na gida wajen ba da kula ga yara.   Misali yanzu haka akwai ’ya’yana ma’ana ’ya’yan mijina wadanda ba ni ce asalin  mahaifiyarsu ba, amma a gabana suka girma. Na kula da su, sun yi karatu yanzu wasunsu ba sa kasar nan suna aiki ne a kasashen duniya daban daban. Da ba su yi karatun ai da ba za su samu irin wannan daukaka ba. Sannan ni kaina a matsayina na mace da ban yi karatu ba, ta yaya zan zama Janar Manaja a kamfanin Yobe Line?