Search
Subscribe
Burina in zama Malamar Jami’a – Sarah Dadih Mbula

Burina in zama Malamar Jami’a – Sarah Dadih Mbula

Madam Sarah Dadih Mbula, Jami’ar Hukumar Kare Hadurra ce ta Kasa, Federal Road Safety Corps (FRSC) da ke da mukamin (Route Commander) a babban ofishin hukumar a Jihar Gombe. A zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihinta da wasu al’amura da suka shafi rayuwarta.

 

Tarihin rayuwata

Sunana Sarah Dadih Mbula, ni Basaya ce daga Karamar Hukumar Bogoro da ke Jihar Bauchi an haife ni a Karamar Hukumar Ningi, na tashi a Tafawa Balewa a ranar 8 ga watan Disamba shekara ta 1980, na girma aka sani a Makarantar Firamare ta Bakari Dukku dake cikin garin Bauchi daga shekarar 1986 zuwa 1991 na gama na samu tafiya Makarantar Sakandare Kimiyya ta ’Yan Mata dake Gindiri a Jo’s daga 1991 zuwa 1997 sai na rubuta IJMB a (ATAP) Abubakar Tatari Ali Polytechnic dake Bauchi a 1997 zuwa 1998 daga nan sai na tafi Jami’ar Jos a shekarar 2000 zuwa 2004 na yi digiri dina na farko a bangaren Tarihi wato History sai aka tura ni Talatar Mafara a jihar Zamfara inda na yi hidimar kasa a can wato NYSC, bayan na gama sai na sake tafiya Jami’ar Bayero ta Kano BUK na yi digiri na biyu a wannan bangare na History na gama a 2013.

Aiki

Na fara aikin gwamnatin da hukumar kiyaye hatsura ta kasa FRSC a shekarar 2007 har zuwa yanzu Inda na yi aiki a Kano da Gombe ina da mukamin route commander ina rike acting admin wato mai kula da sashin mulki na rikon kwarya a Helkwatarmu ta Gombe.

 

Kalubale

Kalubalen aikin Kayan sarki ba’a karawa mutum girma ba tare da ya yi jarrabawa ya ci ba, sannan kalubalen shi ne a aikin kaki ba Mace kowa Namiji ne amma na yi sa’a aikin bai hana ni kula da iyali na ba.

 

Nasara

Na samu nasara domin karin girma na yana zuwa akai-akai ina kuma samun dama na taimakawa jama’a ta dalilin wannan aikin wajen da ya kamata na taimaka. Sannan na hadu da manyan mutane wadanda da ba dan albarkacin kaki din ba da ban isa na shiga inda suke ba saboda ina zuwa taruka daban-daban na karawa juna sani.

 

Burina

Burina shi ne in samu dama in koma Jami’a in yi digiri dina na uku wato PhD. in zama Dokta saboda ina sha’awar koyarwa a Jami’a, sannan in hada da gidan gona dan yanzu ma ina dan taba Noma dai dai gwargwado.

 

Tufafi

Na fi son Atamfa in dinka doguwar riga da gyale inda duk wanda ya ganni ya san na fito cikakkiyar yar Arewa.

 

Abincin da ta fi sha’awa

Na fi son Tuwon Masara da miyar Kuka, wani lokaci kuma Tuwon Shinkafa da miyar Kuka irin ta gargajiya.

 

Hutu

Ya danganta da yadda mutum ya samu hutun amma ba na zuwa kowace kasa ko gari dan yin hutu a garin mu na Bauchi nake hutu na cikin ’yan uwana da iyali na.

 

Kungiyoyi

Kasancewa ta kwararriyar a bangaren ilmin tarihi amma bana kungiya kowacce iri.

 

Yawan Iyali

Ina da aure da ‘Ya’ya ukku, Maza biyu Mace daya kuma dukkan su suna Makaranta.

 

Kasar da nafi sha’awa a duniya

Amurka da Kasar Dubai.

 

Wakar da ta fi so

Nafi son wakar Fanan fasi wakar Coci ce idan ina jin ta tana kara min natsuwa.

 

Wayar da ta fi so

Na fi son waya Infinid

 

Shawara ga Mata

Ina mai baiwa Mata shawarar cewa karatun ‘Ya’ya Mata yana da muhimmanci domin yanzu an fara gane muhimmancin karatun na Mata. A da ne ba a gane ba ake fifita Namiji akan Mata dan idan Mace ta samu ilmi za ta tarbiyartar da ‘ya’yan ta fiye da wacce ba ta yi karatu ba. Sannan zaman gidan miji ma zai sha ban-ban da wacce ba ta yi karatu ba, dan haka shawara ta anan shi ne iyaye su gane ci gaban da ilmantar da ‘Ya’ya Mata yake kawowa domin Mata su ne kan gida wajen tafiyar da harkokin gida sun fi Maza tausayawa iyaye, ko wajen tsabta idan Mace ta yi ilmi za ta san ya za ta tsabtace gidanta daga wasu cututtuka da ake saurin kamuwa da su daga rashin tsabta.

Kamar yadda wasu iyaye kan tura ‘ya’yansu Mata gonaki suna kwadago lokacin Damina Maza kuma ana tura su Makaranta hakan ba dai dai ba ne domin wasu ma talla suke dorawa ‘ya’yan nasu ba karatu ba tarbiya da hakan kan jefa rayuwar su ga hatsari na abun kunya da fatan Iyaye za su gane su yi tunani wajen yin amfani da wasu shawarwarin dan daidai ta tsakanin Maza da Mata wajen karatu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin