✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in zama muryar Arewa a duniyar waka – Mawakin Aku Mai Bakin Magana

A kwanakin baya lokacin da aka rika sace ’yan Arewa ana sayarwa a Kudu, mutane sun rika magana a kan yadda wadansu daga cikin manyan…

A kwanakin baya lokacin da aka rika sace ’yan Arewa ana sayarwa a Kudu, mutane sun rika magana a kan yadda wadansu daga cikin manyan Arewa suka yi shiru. Kwatsam sai ga wata waka mai taken Aku Mai Bakin Magana da Fresh Emir ya yi yana nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake sace yaran ana kaiwa Kudu, ya nuna takaici kan yadda manyan Arewa suka yi shiru kan batun. Aminiya ta zanta da matashin mawakin, inda ya bayyana dalilinsa na fara waka da sauransu:

Wane ne Fresh Emir?

Sunana Adam Abdullahi Emir wanda aka fi sani da Fresh Emir ko  Aku Mai Bakin Magana. Ni haifaffen Unguwar Gwauron Dutse ne da ke cikin birnin Kano. A nan na taso, na yi rayuwata har zuwa girmana.

Na yi makarantar firamare ta Gwauron Dutse  na yi sakandare a Makarantar Abdu Na-Liti. Sannan yanzu ina shirye-shiryen ci gaba da karatu da yardar Allah.

Yaya aka yi ka fara waka?

Gaskiya ba zan ce ga takamaiman yadda aka yi na fara waka ba, saboda na taso tun ina dan karamin yaro da ra’ayin waka a cikin raina. Kuma har na girma wannan ra’ayi na tare da ni. Don haka a takaice zan iya cewa waka kaddarata ce domin da abin aka haife ni, na taso kawai na tsinci kaina ina waka

Mene ne burinka a duniyar waka?

Babban burina shi ne in zama muryar Arewa a fannin waka. Idan na ce muryar Arewa, ina nufin in zama wani jigo da muryata za ta rika tasiri a Arewacin Najeriya da duk inda harshen Hausa yake a duniya. Sannan ina son in samu kudi ta yadda zan yi amfani da su wajen gina gobena da kuma taimaka wa marasa karfi.

Yaya kake ganin bangaren wakokin Hip-Hop a Arewa?

Gaskiya wakokin Hip-Hop na baya. Dalili shi ne har yanzu Hausa Hip-Hop ba ta samu karbuwa ba a Arewa, kuma hakan ya samo asali ne bisa kyamar da ake nuna mana da rashin samun tallafi daga masu kudi da ’yan siyasa kamar yadda abokan sana’armu masu wakoki suke samu.

Da na yi tunanin Hausa Hip-Hop din ce ba a so a Arewa, sai daga baya na gane cewa masu kudinmu da ’yan siyasarmu ne ba sa son ci gabanmu ganin yadda ake gayyato mawakan Kudu a bukukuwa da sauran tarurruka, sannan a ba su makudan kudi, kuma abin mamaki idan sun zo Hip-Hop din da muke yi ana rainawa ita su ma suke yi.

Saboda haka ina kira ga masu kudinmu da ’yan siyasa da mu ma su rika ba mu dama kamar yadda suke ba ’yan Kudu domin mu nuna bajintarmu da fasaharmu.

Me ya sa ka fara jerin wakokin Aku Mai Bakin Magana?

Na fara jerin wakokin Aku Mai Bakin Magana ne saboda ina ganin hakan zai zama min wata hanya da zan yi amfani da ita domin wayarwa da fadakar da mutane cikin sauri da sauki, lura da yadda yawancin mawakan Hausa suka fi mayar da hankalinsu kan wakokin soyayya kawai. Wannan ne ya sa na bullo da wannan salo domin nuna wa duniya cewa ba nishadi da soyayya ake yi wa waka ba.

Ita waka hanya ce ta tura sakonni masu karfi cikin al’umma ta yadda cikin kankanen lokaci za ka tura sakon da dubban mutane za su amfana cikin sauki, musamman a wannan zamani da kafafen sadarwa na zamani suke da karfi.

Kana wakokin fim?

Gaskiya ba na yin wakar fim. Ko wakokin biki a da ba na yi, amma saboda yadda nake yawan samun gayyata yanzu zuwa bukukuwa, dole an canja min tunani. Yanzu haka na tsunduma bangaren wakokin biki.

Idan aka ba ni wakar fim din ma zan yi duk da cewa a al’adar fina-finamu na Hausa, ba sa amfani da wakar Hip-Hop a fim. Amma wani lokaci aka bukata zan yi.

Wace waka ce ta fara jawo maka farin jini

Daya daga cikin jerin wakokin Aku Mai Bakin Magana kashi na uku, wanda na yi a kan illar tura kananan yara bara. Ita ce wakar da ta jawo min farin jini musamman a shafukan sada zumunta, domin a kanta manyan jarumai da mawaka da daraktoci da masu nishadin ban-dariya masu dimbin mabiya suka fara dorawa a shafukansu na sadarwa kamar su Adam A. Zango da Ali Nuhu da Ali Jita da Nazir Sarkin Waka da Ado Gwanja  da Hamisu Breaker da General BMB da Kamal S. Alkali da Ayatullahi Tage da Ali Artwork da sauransu. Don gaskiya a kanta ne jerin wakokin da nake yi na Aku Mai Bakin Magana suka karade ko’ina, don yanzu kusan duk inda na shiga ana gane fuskata sosai.

Wace waka ka fi so a cikin wakokinka?

Wakar da na fi so ita ce mai suna “A yi Mu gani” saboda waka ce da take bayani a kan kada ka raina wani yau saboda ba ka san me zai zama gobe ba.

An haife ka a Kano, amma a wakokinka kana magana kamar ba Bahaushe ba, me ya sa?

Ina haka ne saboda da yanayi. Kasancewar kowane mawaki yana da salonsa, to ni na dauki wannan a matsayin salona. Sannan duk abin da aka ce Bahaushe ne ke yi, bai fiye burge mu ba. Shi ya sa na ce bari in canja kamar ba Bahaushe ba, kuma na samu nasara domin yanzu haka daya daga cikin abin da yake burge mutane shi ne suna ganin ga wani kabila ya zo yana isar da sako da Hausa duk da cewa Hausarsa ba ta fita yadda ta dace.

Wane ne ubangidanka a waka?

Ubangidana a waka shi ne Darakta Mus’ab, kuma shi ne manajana, saboda shi ne wanda har gobe idan na rubuta waka sai na fara ba shi ya duba, ya yi gyare-gyare ko shawarwari kafin in buga.

Me ke ba a sha’awa idan ka yi waka?

Abin da ke ba ni sha’awa idan na yi waka suna da yawa, amma abin da ya fi burge ni shi ne yadda al’umma suke yaba abin da nake yi. Wani lokaci nakan samu yabo daga wajen manyan mutanen da nake ganin kamar ba su san ma ina yi ba. Wannan abin yana ba ni sha’awa matuka

Mene ne sakonka ga mawaka ’yan uwanka?

Sakona ga mawakanmu kuma shi ne mu rika tsabtace kalamanmu a wakokinmu, mu rika yin wakar da za mu iya jin ta tare da iyayenmu da ’yan uwanmu da abokan arziki ba tare da shakka ba.

Sannan ina shawartar mawakanmu na Hip-Hop mu rage yin waka a kan makiya.

Harkar Hip-Hop ba abar rainawa ba ce kamar yadda wadansu ke dauka, domin harka ce da ake yin ta da ilimi, kuma jahili ba zai iya yi ba lura da yadda yawancin masu wakar za ka ga dalibai ne. Mutum ba zai tabbatar da haka ba sai ya yi yunkurin gwadawa sannan zai fahimci abin da nake nufi.

Sannan idan muka kalli harkar wakoki a duniya baki daya, salon Hip-Hop na daya daga cikin manyan salo da duniyar waka ke tafiya da shi a yanzu. Don haka kamar yadda na fada, ya kamata mu mawakan Hip-Hop a rika ba mu damai kamar yadda ake ba sauran mawaka ’yan uwanmu.

Kana da kundin wakoki?

A’a ba ni da albam, sai dai nan gaba da yardar Allah. Kuma za a iya samun wakokina na bidiyo a shafina na YouTube mai suna Fresh Emir, kuma za a iya samun na murya kai-tsaye a manhajar Google idan aka nema.

Mene ne kiranka ga mutane kan kallon da suke yi wa wakokin Hip-Hop?

Kirana ga mutane shi ne su daina kallonmu a matsayin shashashun mutane ko mahaukata kamar yadda yawancin mutane ke yi mana.