✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in zamo babban kocin kwallon kafa a duniya – Rabi’u Tata

Rabi’u Tata shi ne mai horar da ’yan wasan kwallon kafa na kungiyar Jigawa Golden Stars. A tattaunawarsa da Aminiya tsohon Kyaftin din Jigawa Golden…

Rabi’u Tata shi ne mai horar da ’yan wasan kwallon kafa na kungiyar Jigawa Golden Stars. A tattaunawarsa da Aminiya tsohon Kyaftin din Jigawa Golden Stars ya bayyana yadda a yanzu a matsayinsa na kocin kungiyar ya samu nasarar daukaka darajarta daga ajin ’yan dagaji rukuni na hudu har ya kai ta ga matakin Firimiya ta kasa:

Yaya kake ji kan yadda ka samu nasarar haurowa da Jigawa Golden Stars zuwa gasar Frimiya ta kasa?

Zan fara da godiya ga Allah, wanda da taimakonSa ne muka samu wannan nasara. Sannan  ina cike da farin ciki, saboda na kafa wani tarihi wanda babu wani mai horar da ’yan wasa dan asalin Jihar Kano ya taba ajiyewa. Ka ga na dauko wannan kungiyar ce tun daga ajin ’yan dagaji na jiha rukuni na hudu na kawo ta  gasar Firmiya ta kasa wadda ita ce karshen matakin na rukunin kwallon kafa a Najeriya. To ka ga wannan ba karamin abin alfahari ba ne a wurina.

Ko kun sayi sababbin ’yan wasa ganin sabon matakin da za ku fara bugawa?

Eh, ai kamar yadda ka sani dama haka na faruwa walau ka hau ko kuwa ka fado. To zuwa yanzu dai mun ajiye wajen mutum 10 kuma mun samu nasarar daukar sababbin ’yan wasa 15 zuwa 17. Kuma muna sa ran za su taimaka mana mu samu nasarar kaiwa ga gaci da yardar Allah.

Kungiyarku ta halarci gasar Kofin Super 4 ta Kasa har ta kasance ta uku a karshen gasar ta bana me wannan yake nufi gare ka?

Halartar wannan gasa da aka gabatar a garin Enugu gare mu wata nasara ce. Sannan kamar yadda na fada maka a  baya mun sayi sababbin ’yan wasa kuma wannan gasa ta zame mana wata dama da muka yi amfani da ita wajen gwajinsu. Mun fara gane wadanda za su iya yi mana amfani da wadanda watakila sai mun yi wasu ayyuka a kansu.

Sannan game da nasarar da muka samu ta kasancewa ta uku a wannan gasa, abin alfahari ne, domin misali in ka kalli kungiyar Warri Wolbes wacce ta zo ta hudu za ka ga tsohuwar kungiya ce da ta dade a rukunin kwararru na Firimiya kuma tana da manyan ’yan wasa masu karbar kudade masu tsoka amma sai ga shi ni da nake da sababbin ’yan wasa wadanda ba su gama sanin junansu ba da kuma yaran ’yan wasa wadanda a yanzu wadansunsu suka fara bugawa a babban mataki kuma ba wasu manyan kudade suke karba ba, sai ga shi mun doke su da ci 2-1. To ka ga babu abin da zan ce sai dai godiya.

Yanzu wane shiri kake yi don tunkarar gasar Firimiya ta Kasa?

A gaskiya muna nan muna ta kokari, amma dai da farko abin da muke nema shi ne addu’a. sannan muna bukatar gwamnati ta ci gaba da tallafa mana kamar yadda ta saba. Kuma muna ta shirye-shiryen wasannin sada zumunci don yin atisaye.

Kana ganin za ku iya taka wata rawar a-zo-a-gani a gasar Firimiyar da ake daf da farawa?

Lura da irin ’yan wasan da muke da su a yanzu, ina sa ran in Allah Ya so za mu taka rawar gani a wannan kakar wasa ta bana.

Mene ne burinka a wannan sana’a ta horar da ’yan wasa da ka fara?

To ni burina a wannan harka shi ne nan gaba da yardar Allah in zama daya daga cikin manyan masu horar da ’yan wasa na Najeriya daga nan kuma in zamo daya daga cikin manyan masu horar da ’yan wasa na duniya.

Wane kira kake da shi ga gwamnatin Jihar Jigawa?

Kasancewar duk wani abu da za mu yi yana bukatar kudi, ya zama wajibi in yi kira ga gwamnatin Jihar Jigawa ta ci gaba da tallafa wa wannan kungiya don mu samu mu kai gaci.

Wane kira kake da shi ga magoya bayan Kungiyar Jigawa Golden Stars?

Ina kiransu da su ci gaba da yi mana addu’a da kuma kara ba mu shawarwari kamar yadda suka yi a baya. Domin yanzu mun hau kan wani mataki wanda ya fi na baya. Kuma ina tabbatar musu cewa duk shawarar da suka ba mu mai muhimmanci za mu yi aiki da ita.

Ga ’yan wasanka fa?

Ina kira su dage su ci gaba da karbar horo da aiki tukuru, domin kuwa akwai aiki mai dama a gabanmu. Don haka ina kara nanata musu cewa sai sun zage damtse sannan za mu cimma burinmu.