Da Dumi Dumi

Burina ya cika tunda na zama Lauya – Hajiya Jamila Faruk

Hajiya Jamila Umar Faruk kwararriyar lauya ce da ta yi fice a Jihar Jigawa.  Ta yi ayyuka masu yawa a ma’aikatun gwamnatin jihar tun daga Ma’aikatar Shari’a  zuwa wasu ma’aikatun gwamnati da  inda take yanzu wato kamfanin zuba jari mallakar gwamnatin Jihar Jigawa (Jigawa Inbest).  Wakilinmu ya zanta da Lauya Jamila inda ta bambance masa tsakanin Jigawa Inbestment and Property da kuma kamfanin Jigawa Inbest saboda yadda jama’a ba sa iya bambance su. Ta kuma yi karin haske a kan masu sha’awar zuba jari da sayen hannun jari. Da kuma yadda suke taimaka wa kananan kamfanoni su samu kafuwa a kokarin gwamnatin jihar na sama wa matasa aikin yi da dogaro da kansu tare da samar wa gwamnatin jihar kudaden shiga ta hanyar noma da fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje ta hanyar tallafa wa manoman jihar su bunkasa harkar nomansu:

 

Takaitaccen tarihina Sunana Jamila Umar Faruk. An haife ni a Kaduna, a can na yi karatun firamare da sakandare a makarantar Essence International School. Bayan na kammala sakandare a 1995 ne na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda na yi karatun digirina a can daga 1996 zuwa 2002 na kammala karatun lauya wato LBB. Daga bisani na je makarantar aikin lauya don zama cikakkiyar lauya wato Law School da ke Bwari, Abuja a 2002.

Bayan na gama ne na sake yin karatun Debelopment Studies a Jami’ar Tarayya da ke Jihar Jigawa (FUD) a 2017. Na yi aure a shekarar 2003,  ina da ’ya’ya 5 maza 3, mata 2. A takaice yanzu ina da shekara 40 a duniya.

ADVERTISEMENT

Yaushe kika fara aikin gwamnati?

Na fara yin aikin gwamnati a Ma’aikatar Shari’a ta  Jihar Jigawa, a sashen taimaka wa marasa galihu wato Community Law Centre, daga nan na koma Justice Secter Reform ita ma wata cibiya ce da ake taimaka wa masu shari’a. Haka kuma na yi aiki a Ma’aikatar Shari’a, a bangaren yin dokoki na Jihar Jigawa domin yin dokokin ma’aikatun gwamnatin jihar.

Daga nan ne na koma cibiyar wayar da kan jama’a kan zuba jari a Jihar Jigawa wato Jigawa Inbest  yanzu haka da ita nake aiki da nufin bayar da gudunmawata a wannan bangaren domin jihar ta samu baki masu kafa kamfanoni da zuba jari a kamfanonin Jihar Jigawa.

 

Burina lokacin da nake yarinya

Burina a wancan lokacin shi ne in zama lauya, a lokacin ina matakin firamare saboda ina son in zama kamar Hajiya Nana Abdullahi. Saboda ita lauya ce kuma da na gama karatuna na je Jami’ar ABU shi ne na samu kaina a cikin aikin lauya.  A takaice dai ina iya cewa burina ya cika.

 

Kalubale da na fuskanta a matsayina ta mace ganin yadda maza suka fi yawa a aikin lauya

Kalubalen da na fuskanta shi ne na cudanya da maza kasancewata mace mai tarbiyya kuma na fito daga gida mai daraja, saboda ni ’yar manya ce kuma saboda aikina aiki ne da dole zan yi mu’amala da mutane iri-iri. Saboda darajar iyayena na samu sauki sosai wajen abokan aikina, ana daga mini kafa, ban samu wata matsala ba. Sau da yawa mata ba sa iya tsayawa a kan aikin saboda wahalarsa.

 

Gudunmawar da na bai wa mata a aikina na lauya

Gudunmawar da na bai wa mata ba za ta misaltu ba, musamman wajen korafe-korafe a kan yara da mata ta fuskar shari’a. Idan  an zalunce su nakan yi kokari wajen kwato musu hakkokinsu.

Sakamakon haka ya sa nake bai wa mata shawara duk lokacin da zama ya hada ni da su, su dage wajen neman ilimin addini da na zamani kuma a yanzu haka nakan yi bakin kokarina wajen ilimantar da mata musamman ’yan kasuwa yadda za su kafa kungiyoyi domin su amfana da yadda ake samun hannun jari saboda gwamnati ta tallafa musu wajen sayen hannun jari.

 

Burina yanzu a rayuwa

Burina a rayuwa shi ne in tallafa wa mata ta hanyar hada kai da kungiyoyi don bai wa mata dalibai taimako. Haka ina da burin taimakon mata marayu wadanda iyayensu suka rasu. Yanzu haka mun kafa wata kungiya a yankin Hadeja inda nan ne asalina kasancewar mahaifina dan asalin Karamar Hukumar Kaugama ne, da nufin taimaka wa mata da yara kanana. Mun fara ne daga yankinmu kuma da yardar Allah wannan kungiya za ta game Jihar Jigawa baki daya.

 

Shekarun aikina da Jigawa Inbest

Yau shekarata hudu da fara yin aiki da Jigawa Inbest a matsayin Shugabar Sashin bayar da Shawara da Tsara Dabaru (HOD Adbocacy  and Strategy), kuma yanzu ni ce Sakatariya kuma Mai ba Cibiyar Shawara a Bangaren Shari’a (Secretary Legal Adbiser).

 

Bambancin Jigawa Inbestment And Property da Jigawa Inbest

Wato Jigawa Inbest gwamnatin Jigawa ce ta kafa, kwamiti mai suna Kwamitin Bayar da Shawarwari na Jigawa (Jigawa Adbisery Council) aka yi masa ofishi a Sakatariya kuma zuwan gwamnatin Mai girma Gwamna Badaru ne aka yi wa ita Jigawa Inbest doka a watan Yunin 2016, ta zama hukuma mai zaman kanta wato agency. Shi ne aka yi mata shugabanci a karkashin ofishin Mataimakin Gwamna.

 

Aikinmu a Jigawa Inbest

Aikinmu shi ne mu wuce wa ’yan kasuwa gaba, wato masu son zuba jari mu yi musu jagora wajen kafa kamfanoni a jihar nan.  Mu muna aiki kashi uku ne, mu taimaka wa kamfanoni,  mu taimaka wa ’yan kasuwa kuma mu warware matsalolin ’yan kasuwa. Wannan shi ne bambancinmu da Jigawa Inbestment and Property, saboda su aikinsu shi ne su sama wa gwamnati jari ko su saya wa gwamnati kadarar da za ta rika karuwa da ita.

Sabanin namu aikin da muke jawo ’yan kasuwa su zuba jari a jihar domin jama’a su samu aikin yi kuma a samu yalwatar arziki a jihar. Aikinmu yana kawo ci gaba ne a jihar ta fuskar sama wa matasa aikin yi, yanzu haka akwai wasu manyan kamfanoni da ke yin aiki a jihar wadanda sun dauki matasa aiki sama da mutum 1,200 kuma ga Kamfanin Dangote ma zai dauki ma’aikata.

Kuma yanzu haka akwai kamfanoni kimanin 94 da za su kafa rassa a nan jihar. Muna da manya da kananan kamfanoni a jihar nan, yanzu haka akwai manyan kamfanoni 20 da kanana 74 da suke gudanar da ayyukansu cikinta, kuma ana sa ran za su sanya jari na Dala biliyan daya a  wannan shekara wadda hakan ya yi daidai da Naira biliyan 365.

 

 Fuskar da Jihar Jigawa take amfana da mu

Jihar Jigawa ita ce jihar da ta dogara da harkar noma ta fuskar tattalin arzikin kasa yayin da mafi yawan kamfanonin jihar an kafa su ne a kan harkar noma. Saboda haka nan gaba jihar ce za ta fi kowace jiha a Najeriya ta fuskar zuba jari da habakar tattalin arziki. Ba don komai ba sai saboda Jihar Jigawa tana daya daga cikin jihohin da suke da hasken rana. Ta hanyar amfani da hasken rana wajen samar da lantarki mafiya yawan kamkafanonin za su amfana da waccan riba ta samar da hasken lantarki ta hanyar amfani da hasken rana.

 

Akwai kamfanonin da suka nuna sha’awar kafa cibiyarsu domin samar da wutar lantarki ta hasken rana

Yanzu haka wasu kamfanoni hudu sun shigo jihar da nufin samar da wutar lantarki daga hasken rana, cikinsu akwai Kamfanin Oriantedrenuel Energy da Nobescotia da Kamfanin Fan Africa Solar da ke da cibiyoyi a Hadeja da Dutse.

Akwai kuma Kamfanin Digit Net da ke Gagarawa da Gujungu. Mu dai burinmu shi ne mu ga kamfanonin sun kafu sun kama aiki gadan-gadan sun kafa cibiyoyi a jihar sun dauki yara aiki. Akwai abin da mutane ba sa fahimta, duk abin da aka ce zuba jari, ba al’amari ne na gaggawa ba, abu ne da yake bukatar natsuwa a yi shi a hankali.

Ita harkar zuba jari ba abu ne da za a fara shi yau gobe a fara amfana ba, ba kamar bude shago ba ne, wato a zuba kaya gobe a ce an fara amfana.  Kamar kamfani irin na Dangote dole sai an yi hakuri a hankali za a fara cin moriyarsa, ba abu ne da yake bukatar gaggawa ba.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya