✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Burina ya cika ’ya’yana duk mahaddata ne’

Yaya rayuwa ta kasance a da? A lokacin da muke Marte muna garin Kirinuwa kuma muna zaune lafiya da abokan arziki, kuma muna noma, kafin…

Yaya rayuwa ta kasance a da?

A lokacin da muke Marte muna garin Kirinuwa kuma muna zaune lafiya da abokan arziki, kuma muna noma, kafin matsalar Boko Haram ta zo. To da wannan matasalar ta zo sai ya zama ba mu iya ci gaba da zama a garin Kirinuwa sai muka dawo zuwa nan garin Maiduguri don gudun hijira.

Da kuke garin Kirinuwa ’yan Boko Haram sun taba kawo muka harin da ya shafe ka?

Da suka shigo garin da farko ba sa taba kowa, domin suna zamansu ne a bayan gari, daga baya suka fara shigowa cikin garin musamman idan suka ji wani mutum yana da kudi sai su zo su karbe kudinsa, ko kuma idan suka ji wani mutum yana da kayan abinci ko na bukatun yau da kullum suna zuwa su karbe. To kawai sai suka fara yi wa mutane barna, to da mutane suka fara ganin haka sai aka fara tunanin yin gudun hijira zuwa garin Maiduguri. To ni da iyalina sai muka ankara cewa akasarin makwabtanmu duk sun gudu, kuma jami’an tsaro da suka gane cewa Boko Haram na dawowa cikin garin Kirinuwa sai suna bi suna kona wuraren da a da suke boye a kauyuka da dazuka tare da kashe akasarinsu. Sai suka shaida wa mutanen kauyuka cewa su tashi domin idan suka tafi babu shakka za su zo su kashe su. To wannan ne ya karkato da hankalinmu cewa ya kamata mu gudu sai na yanke shawarar mu yi gudun hijira zuwa nan garin Maiduguri a nan sansanin gudun hijirar da ka ganmu.

Da kuka dawo Maiduguri, yaya rayuwa ta kasance?

A gaskiya a lokacin da muka zo Maiduguri ba mu taba tunanin cewa za a tarbe mu hannu bibbiyu ba, domin mu mutanen kauye ne, kuma daji ne ba mu saba da rayuwar birni ba. Saboda haka ba mu yi zaton za a iya tarbarmu yadda ya kamata ba, amma abin sai ya saba tunaninmu domin kuwa an yi mana tarba mai kyau, kuma mun samu karamci wajen ’yan uwa da abokan arziki don sun ba mu masauki da abinci da kayayakin bukatun yau da kullum. Kuma tunda muka zo yau fiye da shekara shida ke nan muke zaune lafiya da kowa babu wani tashin hankali kuma gwamnati da hukumomi da masu hannu da shuni suna taimaka mana a kowane lokaci.

 To a yanzu kuna sha’awar komawa kauyen da zama?

To ai ko mun yi sha’awar komawa can din har yanzu babu kwanciyar hankali, gara mu ci gaba da zamanmu a nan kafin gari ya koma kamar  da. Don har yanzu muna samun labarin daidaikun Boko Haram din suna can ba su bar wurin ba, to ka ga idan mun yi gaggawar komawa ba mu yi wa kanmu adalci ba, zamanmu a nan ya fi kwanciyar hankali.’

’Ya’yanka nawa?

Su goma ne.

Ga daya ya zama gwarzon musabaka ta duniya, me za ka ce?

A gaskiya ina cikin farin ciki ganin cewa na haifi yara masu kwazo a harkar karatun Kur’ani. Domin shi wannan da ya zama zakara akwai wansa ma mahaddaci ne, kuma duk akasarin kannensu mahaddata ne kuma makaranta Alkur’ani ne. Kuma burina a ce dukkan ’ya’yana mahaddata ne kafin in rasu, kuma ga shi Allah Ya nuna mini wannan. Yanzu shekaruna sun haura 60 ba ni da wani burin da ya wuce wannan, ko yanzu na rasu burina ya cika, sa dai kawai in yi musu fatar alheri da kuma fatar su ma su samu irin haka a zuriyarsu. Ka san Allah Yana zabar daya daga cikin mutane ya daga shi ya zama zakara, to haka Allah Ya yi wa wannan yaro Idris, na kuma gode wa Allah da sauran wadanda suke taimaka mana a kan wannan al’amari na samun nasararsa. Allah Ya saka musu da alheri, Ya kuma sanya Kur’ani ya cece mu baki daya.