✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bursunoni sun yi bikin aurensu a kurkuku

Ranar 11 ga Agustan nan kurkukun Sichuan gundumar da ke Kudu maso yammacin kasar ya gudanar da ruguntsimin bikin aure ga bursunoni  uku. Wannan biki…

Ranar 11 ga Agustan nan kurkukun Sichuan gundumar da ke Kudu maso yammacin kasar ya gudanar da ruguntsimin bikin aure ga bursunoni  uku. Wannan biki ya samu halartar bursunoni 200, wadanda suka kasance cikin kwarin  gwiwa da jin cewa za su samu ’yancin kansu.

daya daga cikin bursunonin, Wang Lei yana zaman kurkuku na shekara 10 bisa laifin samar da kwayoyin magani ba bisa ka’ida ba. Ita kuwa budurwarsa Jingjing da ke tsananin sonsa, ta yi kokarin shawo kan iyayenta har suka yarda aka daura musu aure.

Doka dai ta yi wa irin wadannan ma’aurata tanadi, inda Jingjing za ta rika ziyartar angonta Wang sau biyu a wata. Kodayake tana ma da rabin sa’a na gana wa da shi a kowace rana, ta kum amince da hakan, inda ta ce jiran  da take yi masa yana da amfani.

Wannan dai shi ne karo na farko bayan shekara 60 da aka taba yi wa bursunoni bikin aure. A cewar wani jami’in kula da kurkuku, Zeng Hongbinm suna fatan auren  zai gyara tarbiyar wadan da suke tsare da su, ta yadda nan gabna za su zama mutanen kwarai.

Labarin soyayyar ’yar kurkuku mutum uku ya sosa zukatan abokan zamansu, har suke yi musu hasashen ganin sun fice daga gidan kaso, su tare da iyalansu a cikin al’umma.

Zeng ya ce kurkuku ya taka rawa a sauran fannonin rayuwa, wadanda suka hada da ilimantar da ’ya’yan ’yan kurkukun da samar musu filin  gini ko biyan diyya in an tashe su daga gidajensu.

“Wadannan matakan  na nuna yadda ake kula da mazaunan kurkukun . Muna fatan za su gyara kura-kuransu su koma cikin al’umma,” inji Zeng.