✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cabani ya koma kulob din Chelsea

Kulob din Napoli da ke Italiya ya amince da tayin Yuro miliyan 58 daga kulob din Chelsea da ke Ingila ya yi a kan dan…

Kulob din Napoli da ke Italiya ya amince da tayin Yuro miliyan 58 daga kulob din Chelsea da ke Ingila ya yi a kan dan wasan gabansa mai suna Edinson Cabani kamar yadda gidan Rediyon Marte ya ruwaito a ranar Litinin da ta wuce.
Gidan rediyon Marte wanda mallakar kulob din Napoli  ya tabbatar da labarin  sayar da dan wasan a lokacin da yake watsa labarai.
Radiyon ya ruwaito dan kwallon zai rika karbar albashin Yuro miliyan takwas da rabi a shekara, al’amarin da ya sa tuni dan wasan ya amince ya canza sheka zuwa Ingila ba tare da wani bata lokaci ba.
Edinson Cabani yana daga cikin zaratan ’yan wasan gaba da ake ji da su a Italiya.
kungiyoyin kwallon kafa da dama sun yi zawarcinsa da suka hada da na Real Madrid da ke Sifen da Manchester City da ke Ingila da sauransu don haka yanzu an kawo karshen zawarcinsa tun da ya koma Chelsea.