Da Dumi Dumi

CAF 2019: Rayuwa da gwagwarmayar Sadio Mane

Senegal Sadio Mane
Senegal Sadio Mane

Abubuwa biyar game da zakaran kwallon Afirika na bana

  1. Ya kafa tarihin cin kwallaye uku a wasa daya cikin ma fi kankantar lokaci
  2. Mahaifiyarsa ba ta kallon a Talabijin idan yana buga kwallo
  3. Zuwa filin wasa ba akan lokaci ba, shi ya yi sanadiyyar komawarsa kungiyar Liberpool
  4. Ya tashi cikin talauci
  5. Yana dan shekara 19 ya fara buga kwallo ajin kwararru na Turai

Dan wasan kwallon kafa  na kasar Senegal Sadio Mane wanda kuma yake buga wa kungiyar Liberpool ta Ingila tamaula ya lashe gasar zakaran kwallon kafa na nahiyar Afirika na 2019. A ranar Talata hukumar kwallon kafa ta Afirka Caf ta bayyana sunan Mane a matsayin wanda ya zama sabon gwarzon dan wasan nahiyar na 2019.

An haifi Sadio Mane ranar 10 ga watan Afrilun 1992 a kauyen Bambali na yankin Sedhiou a kudancin kasar Senegal. Saboda mahaifansa suna da ’ya’ya da yawa, ba su kuma da karfin tura shi zuwa makaranya, Mane ya tashi a gidan kawunsa ne inda kullum yake fita ya buga kwallon layi tare da abokaninsa.

Ganin irin basirarsa da kuma yadda ya nace shi kwallon kafa kawai yake son yi ne iyayensa da kawunsa suka sayar da amfanin gonarsu inda suka hada masa ’yan kudi don ya tafi Dakar babban birni Senegal don ya je ya jarraba neman samun wata babbar kungiya da za ya buga wa.

Mane ya je wasan karshe na gasar cin Kofin Kasashen Afirka na 2019, kuma ya ci kwallo uku tare da bayar da guda daya aka ci. Ya lashe gasar Zakarun Turai ta Champions League tare da Liberpool, inda ya ci kwallo hudu kuma ya bayar aka ci biyu. Kazalika, ya lashe gasar Kofin Zakarun Duniya na Fifa Club World Cup da aka yi a kasar Katar.

ADVERTISEMENT

A Premier bara (2018/2019) ya ci kwallo 22 kuma ya bayar an ci daya. A gasar ta bana ya ci 11 ya bayar an ci shida. Mane ya zo na biyu har sau biyu amma bai taba lashe kyautar ba.

Sadio Mane wanda a yanzu tauraruwarsa ke haskawa yana daya daga cikin manyan ’yan wasan kwallo na duniya. Ya fara sana’r kwallon kafa a wata karamar kungiya mai suna Metz a ta kasar Faransa lokacin yana dan shekara 19, kamin daga bisani ya koma kasar Austria da wasa inda ya buga wa wata kungiya mai suna Red Bull Salzburg a shekarar 2012 akan kudi fam million 4.

Bayan da ya ci gasar kasar Austria har sau biyu a kakar wasa ta 2013-2014 daga nan sai likafar Mane ta ci gaba inda ya koma yana buga wa kungiyar Southampton ta kasar Ingila wasa akan zunzurutun kudi har fam miliyan 11.8. a can ne ya kafa tarihi na cin kwallaye uku a wasa daya cikin ma fi kankantar lokaci inda ya ci su a cikin dakika 179 a wani wasa da kungiyar tasa ta lallasa kungiyar Aston Billa da ci 6-1 a shekarar 2015.

Haka kuma Mane ya taimaka wa kasarsa wajen kaiwa ga shiga gasar kwallon kafa ta duniya kuma ya taka rawar gani a wasannin da kasarsa ta buga  a gasar ta cin kofin duniya a 2018. Ya kuma buga wa kasarsa wasannin a gasar Olympic ta duniya.

A ranar 28 ga watan Yuni na 2016 Mane ya koma kungiyar kwallon kafa ta Liberpool da kwallo inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar akan kudi fam miliyan 34 har yanzu kuma yana nan tare da wannan kungiya. Mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Southampton sun bayyana dabi’arsa ta ‘African Time’ wato fitowa filin wasa a makare a matsayin daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya suka sayar da Mane a wancan lokaci. Amma daga baya bayan ya koma Liberpool ya daina wannan dabi’a ta zuwa a makare.

Mane Musulmi ne mai rko da addini, wanda samun duniya bai sanya shi fankama ba. A duk lokacin da ya samu lokaci yakan je ya wanke bayin masallacin Juma’a a birnin Liberpool. Haka kuma Mane yana taimaka wa matasa da tsofaffin garinsu duk lokacin da ya kai ziyara.

Mahaifiyarsa ta bayyana cewa bata iya kallonsa yana buga wasa a talabijin saboda tana ganin kamar wani zai ji masa ciwo tun bayan lokacin da ta taba ganin ya yi rauni an dauke shi daga filin wasa.

Mane ya kayar  sauran ’yan takara da suka hada da Mohammed Salah na kasar Masar wanda yake taka wa Liberpool kwallo da kuma Riyad Mahrez dan kasar Aljeriya wanda yake taka ledarsa a kungiyar kwallon kafa ta Man City.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya