Sabon Shugaban Kamfanin Man fetur na Kasa (NNPC), Malam Mele Kolo Kyari, ya ce kwarewa da cancanta ne abin da kamfanin zai duba wajen daukar ma’aikata ba sanayya ba.
A kwanan nan kamfanin man na ya gudanar da jarrabawar daukar ma’aikata daga duk fadin kasar nan wacce dubban mutane suka rubuta.
Malam Kolo Kyari ya kara da cewa, a karkashin jagorancinsa, za a fara aikin lalubowa da tatsar albarkatun mai da suke a jihohin Arewacin kasar nan ba da jimawa ba.
“Shugaban Kasa ya ba mu ikon cewa duk inda mai yake a kasar nan mu nemo shi kuma mu fara dibarsa don sarrafawa da wadatar da al’umma da man mai rahusa ga talakawa,” inji Kyari
A cewarsa, tun a ’yan watannin baya Shugaba Muhammadu Buhari, ya ziyarci wani gari da ake kira Kwalmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, don ganin irin arzikin mai da ake da shi a yankin.
“Nan ba jimawa ba za mu sanar wa duniya adadin yawan man da albarkantun man da ake da su a yankin,” inji shi.
A cewar Kyari, duk wanda ya taka doka, za a ladabtar da shi yadda doka ta tanada, yana mai cewa babu wanda zai dauki doka a hannunsa a karkashin shugabancinsa.